TARTSATSI 28

Advertisement

Jiki a sanyaye umma ta shige d’akinta, tana tunanin wannan rigima da takunno masu, wadda takeso ta raba mata kan ‘ya ‘ya, tayi ajiyar zuciya cikin zuciyarta ta k’udurta bazata nuna masu tasani ba, zata zura masu ido, taga iya gudun ruwansu, amma duk da haka, tana rokon Allah, akan abun yazo masu cikin sauki .

Abba ya dawo gida, bayan yayi sallah ne yaci abinci, umma ta fad’a masa sak’on sadauki ya baiwa Hafsa, Amma ta boye abinda ke tsakanin Hafsa da salma, don abin kunya ne agareta wani yaji wannan magana, don shi kanshi Abban batasan da wace fuska zai Kalli abun ba, shiyasa tayi gum da bakinta.

Abba yace “Ba damuwa, Amma bai fad’i ranar da zaizo ba? ”

Umma tace “Gaskiya yadaice yana so yazo ya gaidaka”

Abba yace “Ba laifi, duk lokacin da yazo,
ko bana nan za’a iya Kirana a waya, sai indawo mu gaisa Allah dai ya tabbatar muna da alkhairi”

Umma tace “Ameen Abban yara”

Daga nan suka canza wata hira.

Daga salma har Hafsa dukansu, haka sukayi kwana zuciya ba dad’i, kowace da abunda zuciyarta take sak’awa, umma ma kanta damuwa fal ranta.

Bayan kwana biyu da zuwan sadauki ne, yayi tunanin yakamata yaje ya ga Abban su Hafsa, domin yanaso ya bashi dama, ya dinga zuwa wurinta, duk lokacin da son ganinta yazo masa, don yanzu haka jin yake kamar yayi shekara biyu,ba tareda ya gantaba, saboda Hafsa ta zamo jinin jikinsa, duk wani motsi nashi Hafsa ce, musamman in ya tuno murmushinta Mai sanya shi kasala.

Atake ya jawo wayar shi, ya kira Aliyu bugu biyu Aliyu ya d’auka, bayan sun gaisa ne yake ce masa, yana so yaje ya gaisa da Abba, Aliyu yace bari yaje university in da yake aiki ya fad’awa Abba don yasan yanzu ko yaje gida bazai iskeshi ba, sadauki yana ta godiya don yaji dad’in taimakon na Aliyu ba Kad’an ba.

Advertisements

Aikuwa haka akayi Aliyu har cen yaje, yasanar da Abban zuwan sadauki, Abba da sauri ya kira umma yace da ita bak’o zaizo, a tanadar masa wani Abu, ai kuwa umma ta kira Hafsa ta sanar da ita, Hafsa nan take gabanta ya ya fad’i, jikinta yayi sanyi sosai, daman acikin kwana biyun nan ba wani kuzari ne da ita ba, saboda takasa hango hanya mafi sauki, da ya dace ta cikawa salma Alk’awalinta.

Umma ta kalleta dakyau tace

“me kika ya dace muyi masa?”

Hafsa jiki ba k’wari tace da umma

“Muyi masa dambu tunda muna da komi a k’asa”

Umma tayi murmushi tace “Yawwa ‘yata, kin kawo shawara, amma aganinki zai iya cin dambun?”

Hafsa tayi murmumushi tace “zaici umma, ai kinsan dambu mutane da yawa suna sonshi”

Umma tace “to bari muje mu fara”

Ai kuwa nan take suka tsunduma kitchen, umma da Hafsa sai faman aiki suke, cikin natsuwa, don so suke su had’a shi yafi na kullum dad’i, don wannan dambun na musamman ne, aiko nan take sai gida ya gauraye da kamshi, salma dake d’aki tana chatting da Dr sadik, akan cewa ta shirya zaizo yau, tana jin kamshi ya buge hancinta, ba shiri ta kashe Data ta ajiye wayar ta fito.

Tace da umma “wannan k’amshi fa?”

Umma tace “bak’o zamuyi”

Salma tace wane bak’o umma?

Advertisements

Kafin umma ta bata amsa salma tadafe baki race

“Au wai duk don Dr yace zai zo ne, kukewannan hakilon?cab lalle kam”

Ta juya ta fara tafiya da niyyar ta komawar ta d’aki umma ta kalleta tace

“Bak’on Hafsa ne zaizo, yanzu Abban ku ya kira yace atanadar masa wani Abu”

Salma tayi wani juyi da k’arfi tace

“Ba dai Wanda yazo ranar nan ba?”

Umma ta kalleta Shek’ek’e tace
“Shifa miye matsalar ki akan hakan?”

Salma nan take yanayinta ya canza jiki ba k’wari tace

“Babu”

Tana k’are maganar ta shigewarta d’aki, umma ta bita da kallo har ta shige ta girgiza kanta taci gaba da aikinta, ita dai Hafsa aikinta kawai take ba tareda ta nuna wata damuwa akan lamarin ba, har suka k’are aikin su salma bata fito ba, don harda kunun aya umma tace sai anyi.

Bayan sun k’are ne umma tace da Hafsa taje ta yo wanka,kar yazo bata shirya ba, har Hafsa ta fara tafiya, umma tace da ita

“ki tabbatar kinyi kwalliyar k’warai, don kar ki biye waccen ‘yar son zuciya”

Hafsa tayi marau marau da ido alamun kuka takeso tayi umma tace

“kul kar inga k’walla a idonki, kije ki natsu kiyi kwalliyar ki mai kyau”

Hafsa tayi saurin juyawa, tareda share k’wallar da umma ta gargad’eta akanta, don ta riga ta fito batada yanda zatayi,a haka ta shiga d’akinsu ko kallo salma bata isheta ba ta cire kayanta ta shige toilet.

Bayan ta fito ne taji dawowar Abba ta saka hijabinta taje tayi masa sannu da zuwa sannan ta dawo ta Fara rangad’a kwalliya, salma dake kallonta ta tashi fuu ta fita da alama itama gaida Abba taje yi, minti biyu sai gata ta dawo, tana kallon yanda Hafsa take tsara kwalliya, itama ba shiri ta shiga wanka, ta fito ta fara murza tata kwalliyar.

Suna cikin kwalliyar ne usman ya shigo da gudu, yau saboda zumud’i, ko sallama bai samu yayi ba, yace da Hafsa

“Aunty Hafsa mutumenki na ranar ya k’ara dawowa”

Daga salma Har Hafsa gabansu ne yace dam! dam! Saboda dukansu su biyun kowa da dalilin da ya sakashi fad’uwar gaban.

Kafin Hafsa tayi magana salma ta katsa masa tsawa akan yaje ya bata wuri, ta fake da yimasa fad’a akan rashin sallamar da baiyi ba, itadai Hafsa tsam ta tashi, ta Fara saka kayanta bayan ta k’are ta murza d’aurin d’ankwalinta ya zauna cif ta k’ara duba kanta amadubi tana yiwa Allah godiya akan baiwar da yayi Mata.

Sadauki kuwa tareda Abokinsa yazo wanda yasa yayiwa Hafsa lik’i wato kabiru wanda ake kira said k. Bayan anyi masu iso cikin gidan , bakunansu d’auke da sallama suka shiga cikin d’akin Abba har zasu zauna k’asa Abba yace su hau kan kujera amma suka k’i hawa suka darshe a k’asa, bayan Sun k’are gaisawa ne, kb ya Fara magana da Abba yace

“Abba munzone Akan Abokina yaga Hafsa, yace yana so, to shine mukazo muna so abashi dama, ya shiga cikin Mane Man aurenta”

Abba ya Kalli sadauki dakyau tashi guda yaji hankalinshi ya kwanta dashi cikin dattijantaka Abba yace

“Na bashi dama yazo su daidaita kansu in matar shi ce zamu bisu da addu’a, fatanmu kawai Allah ya sanya alkhairi, acikin lamarin”

Dukansu suka had’a baki sukace “Ameen Abba”

Abba ya k’ara kallon sadauki yace

“Ni kamar ma naso na sheda fuskar?”

Sadauki yayi murmushi yace

” Eh Abba bazaka rasa ganeni ba, don kuwa ni d’an gidan bashir Dala ne”

Abba da hanzari ya k’ara kallon sadauki yace

“Masha Allah kace Abun na gida ne Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi”

Sukace “Ameen”

Nima dai kam nace Ameen🤪

Akafta🤸🏻♀

*Daga Alkalamin*
*D/Auta✍🏻*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 38

Advertisement 38 Valhalla VintageVerb VST Crack Ya Rasa yarda zaiyi? Yasan Yana San Binaif,Baya so yake nuna son…
KALLABI
Read More

KALLABI 66

Advertisement BABI NA SITTIN DA SHIDA Mikewa Gidado yayi shima ya fita, baki daya ya bar masarautan, inda…
Read More

Lu’u Lu’u 47

Advertisement _Bismillahir rahamanir rahim_ *47*     Mi’kewa tayi da azama ta fita a d’akin, bafaden dake k’ofar…
KALLABI
Read More

KALLABI 29

Advertisement BABI NA ASHIRIN DA TARA. “Ta zame min mara amfani, wanda ba zan kuma amfanar rayuwa ta…