TARTSATSI 29

Advertisement

*page 29*

Bayan sun k’are tattaunawar ne Abba, ya kira umma suka gaisa mutunce, umma sai faman sunne Kai takeyi kunyar sarakuta take kwasar ta, bayan sun k’are gaisawar akayi masu jagora har tsohon d’akin auwal, inda d’azu su Hafsa da umma suka gyarashi tass, yayinda aka dauke d’an k’aramin gadon auwal dake da’kin aka Kai shi a d’akin su Hafsa, aka ajiye da niyyar su hak’a shi sudinga kwana akai sai aka bar kujerun kawai.

D’akin sai wani tsadadden kamshi ne ke tashi, dukansu suka samu wurin zama suka zauna, sun fara tab’a ‘yar hira ne, sukaji sallamar usman d’auke da kayan abinci ,a hannunsa, Hafsa biye dashi d’auke da sauran kayan, tare suka ajiye usman ya gaishesu, yazo zai fita sadauki ya kirashi ya bashi bandur d’in ‘yan nera ishirin, usman yak’i karb’a, kb ya Karb’a ya saka masa a aljihu, usman yayi godiya ya fita yana ta faman murna.

Hafsa kuwa wuri ta samu ta zauna ta d’ago Kai da niyyar ta gaishesu caraf idon ta suka had’u da na sadauki,ba shiri ta janye nata idanun, saboda wani yam da taji ajikinta, batasan me yasa ba duk suka had’a ido sai tajita a wani iri, wanda bata taba jin hakan ga kowa ba, sai akan wannan -shine gay- d’in.

Sadauki kuwa da tunda ta shigo, tsarin kwalliyarta, ya tafi da Rabin tunaninshi, ya k’ura mata ido sosai,ko kiftawa baiso yayi,saboda shidai komi na Hafsa burgeshi yake, sai da kb yayi gyaran murya, sannan dukansu su biyu suka tuna wai ashe ba sukad’ai bane a wurin.

Hafsa ta d’ago fuskarta ta Kalli kb ta gaidasa, cikin siririyar muryarta mai dad’in sauraro, kb ya amsa yana satar kallon sadauki,dake ta kallon Hafsa, itama akayi dai dai ta Kai kallonta wurinsa da niyyar ta gaidashi clashing idanunsu suka k’ara yi a haka dai ta daure ta gaidashi ya amsa cikin tsantsar farinciki, kb kam yaga abunda yafi kawai ya basu wuri kar su d’an zanta ya Kalli Hafsa ya Kalli sadauki yace

“Love birds ni zan fita in d’an sha iska”

Dukansu suka kalleshi sukayi murmushi Hafsa tace
“Haba dai kajira kuci abinci”

Kb yace “Kedai bari in d’an zagaya, inga unguwar taku ya take kafin ku k’are Gaisawa”

k’are maganar sa keda wuya ya tashi ya fita abunshi.
kb yana fita sadauki ya kalli Hafsa yace

Advertisements

“Madubala wutar kyau, nidai nayi sa’ar mata, duk fad’in duniya ba Wanda ya isa ya kamo k’afa ta Nifa mai sa’a ne gaskiya”

Ya k’are maganar fuskarshi d’auke da wani murmushi, mai k’ayatarwa, Hafsa ta k’ara sunne Kai, sadauki yace

“A’a yanzu ke kunya me ya kawoki tsakanin masoya”

Hafsa ta dafe bakinta tana shirin dariya tace

“Ga irin kalar abincinmu nan, in zaka iya ci?”

Sadauki ya Kalli kulolin yace da ita

“Me kike nufi ni zanyi saving d’in kaina ne ko kuwa? tab to kima shirya don sadauki jarumine a waje, shagwab’ab’b’e ne a gida, balle yanzu da nike agabanki, ai manta ko ni wanene nikeyi, ke in tak’aice mk sunana ma idan kikace in fad’a mantawa zanyi”

Hafsa tayi guntuwar dariya ta tashi daga mazauninta ta jawo katuwar carpet ta shimfid’a ta dawo da kulolin a tsakiya ta zauna ta bud’a kular dambun, wani k’amshi ya ziyarci hancinshi da sauri ya sauko saman carpet d’in ya zauna ya dafe cikin shi yace

“Wai Allah, har naji na k’oshi, wannan k’amshi haka”

Hafsa bata kalleshi ba tayi dariya dai ta fara zuba abincin ta cika plate fam ya bud’a ido da karfi yace

“Wannan Abincinfa, dawa dawa zai cishi?”

Tayi siririyar dariya tace “Bak’on Hafsa da aunty salma”

Advertisements

Sadauki yayi saurin kallonta batareda yace komi ba ya spoon biyu ya saka yace

“Oya ci muci malama”

Hafsa tayi saurin kallonshi tace

Tace “Ni?”

Yace “Eh ke fa, inkuwa ba zaki ci ba, to had’a kayanki ni ma nagode”

Hafsa ta marairaice fuska alamar tausayi, haka kawai taji Idan bai ci ba zata iya yin kuka, cikin sarkewar muryar kuka tace dashi

“Kayi hak’uri zanci”

Yace “to Fara ci ingani”

Ta d’auki spoon ta d’ebo kad’an ta ci, ya kalleta dakyau yayi murmushi ya canza murya kalar mata yace

“Sadauki na tausaya maka”

Hafsa ta tuntsure da dariya, haka suka ci abincin Hafsa sai faman wayo take masa, kamar ci take sadauki ko sai santin dambu yake zubawa, hadda cewa idan sukayi aure, kullum shine zata dinga girka masa safe da dare, ba shiri hafsa tasa wani plate tayi masa waigi, yasha kunun aya shima sai santi yake ta bugawa, haka suka k’are cin abincin yana ta sanya Hafsa dariya.

Ya fiddo da wani d’an k’aramin Abu sai d’aukar ido yake, yana bud’awa sai ga wani zobe mai shegen kyau sai kyalli yakeyi, ya ciroshi daga cikin gidanshi, yace ta kawo hannunta ya saka mata, tak’i badawa, yayi yayi tak’i, ya b’ata fuska yace

“Shikenan gashinan ki saka da kanki, amma naso ni nasaka maki da hannuna, yanda duk lokacin da kika kalleshi, zaki tuno da fuskata saboda tafiya zanyi gobe insha Allah sai nayi sati biyu acen”

Hafsa tayi ajiyar zuciya tayi zuciyarta tana rawa amma ahaka tayi jarumtar magana tace

“Akwai maganar da nike so muyi dakai”

Tofa😱

Akafta🤸🏻♀

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 22

Advertisement Page 22* ********************** Ashe ba salma kad’ai ba mata da mazan dake wurin, ya tafi da tunaninsu,…
KALLABI
Read More

KALLABI 48

Advertisement BABI NA ARBA’IN DA TAKWAS Tun bayan dawowar shi, baki daya ya kasa sukuni, asalima ko wurin…
Read More

TARTSATSI 75

Advertisement *Page 75*   *********************   Alhaji acikin b’acin ran da ya bayyana, akan fuskarshi k’arara yace:  …
KALLABI
Read More

KALLABI 26

Advertisement BABI NA ASHIRIN DA SHIDA Muryan shi na rawa ya rike hannun ta. “Zai fi kyau ki…