TARTSATSI 3

Advertisement

 

☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️

Home of qualities and trusted writers of the nation

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

 

*Nagode da addu’o’inku masoyana aci gaba da ruwan comment.*

*Shafa Abu gaisuwarki daban take jinjinar ban girma kawalliyata*

*Amina Haladu ga taki kema*

Fati Ghana
Omee
Nasmi Diyata
Hummy
Kuma ga taku gaisuwa

*************

Advertisements

Bayan Abba ya dawo masallaci, shida su usman, umma tagabatar mashi da abincinshi, yana ci suna Hira nan take bashi labarin diramar da sukayi da salma yana murmushinsu na Manya yace

“yummu Salma taci arxikin banda ra’ayin yiwa d’iyana auren dole, da ina kyautata zaton ta kanta zanfara.”

Umma tayi murmushi tace

“lalle kam don abun nata ya shalle tunaninmu.”

Abba ya nisa yace

“muci gaba da yimasu addu’a, Allah ya basu mazajen aure nagari, mu auraddasu, mu huta”

Umma Tayi ajiyar zuciya tace

“Ameen Abban yara, ai kullum munayi, fatanmu kawai Allah yasa adace.”

Abba yace

“Ameen y Allah”

Abangaren su salma ko sunacen daki suna hira inda hafsa take cewa

“Aunty salma yana da kyau. gobe Muje mu gano aunty umaima, mun kwana biyu bamu je ba.”

Advertisements

Salma ta yatsine fuska tace

“ke nifa tsinannen yawon nanne baniso, kana fita abika da na mujiya, har Asamu wani kulafutacce, mai cewa ya gani yana so”

Ta wani tabe baki tace

“Tarkacen banza, su wani kwaso kafafu suna rawar jiki, batareda sun tsaya sun kara kallon kansu, a jikin madubi ba.”

Hafsa ta kalleta dakyau tace

“To ke aunty salma so kike muyi ta zama gida, batareda mun samu masu cewa suna sonmu ba?”

Ta kara cewa

“Nifa aganina, indai zaka sami, Wanda zai soka tsakani da Allah, kuma kaima yayi maka zaka iya aurar abinka batare da duban wata nakasu ta halittarsa ba don dole ne asamu abinda zai rasa, a cikin halittarshi”

Tayi ajiyar zuciya takara cewa

“Zaki sami wani baki, wani fari, wani guntu, wani dogo, wani siriri, wani mai jiki, to kinga in akace sai wanda yahada komi tsaf, to gaskiya mata da yawa bazasu yi aure ba”

Salma ta harare ta tace

“Shikenan sai in kwasowa kaina jangwam lalle ma yarinya”

Hafsa tayi tagumi tace

“Jangwam din mi? Kedai kawai ki samu wanda zai rike maki zuciya wannan ra’ayin naki duk zaki ajeshi ne”

Salma ta tashi tsaye, tazo gabanta, ta jujjuya, Tayi tafiya, taku biyu zuwa uku ta dawo, ta kwance dunbujen gashin da Allah ya arzuta ta dashi ya sauko gadon bayanta tace

“ko indiya yarensu na inyanci kawai zata nuna Man”

 

Hafsa bita da kallo, ko kyaftawa batayi, saboda gabadai notukan kanta sun kwance, bakinta ya kasa fidda ko Kalma daya kafin ta kamo abinda zata fada salma ta kara cewa

“Dubanni dakyau, me Allah ya rageni dashi, yanda kika gannin nan, haka zan samu dai dai ni, don bazan je in kwasowa kaina wanda ko d’iya ka haifa arasa tantance nawaye ba, aganka da goyo, ace dan waye ka dauko haka kawai arena maka wayo.”

Hafsa Tayi jarumta tace ta kwantar da murya tace

“Aunty salma ko kinsan majority wadanda kike ganinsu komi yaji dinnan halinsu abin kyama ne”

Nan take fuskar salma ta canza tayi gaggawar fadin

“Indai su kike Man fatar insamu to ai Shikenan.”

Hafsa bakin ta yana rawa tace

“wallahi aunty salma ni ba nufina kenan ba, ke kanki kinsan bazanso hakan ba.”

Ta kara cewa

“Allah dai ya kiyaye”

Salma tace

“To kidaina yiman irin wannan magana banso.”

Hafsa ta bata rai tace

“Allah ya baki hakuru”

Ta yi ajiyar zuciya ta kara cewa

“Bazan taba zura maki Ido ina kallo ki fada halaka ba saidai muyi abunda zamuyi saina fada maki gsky.”

Tayi fuu taje tayi kwanciyarta tabar salma tsaye tana kallonta jikinta yayi sanyi sosai ganin yanda hafsa tayi fushi da ita.

Cikin Sanyin jiki taxo kusa da ita takwanta ta kira sunanta tace

“Haba manga tah! me yasa ra’ayin yazo banban da naki? Ko bakibin ra’ayina Don Allah ki fahimceni amma tunda na bata maki Don Allah kiyi hakuri.”

Hafsa tayi mata shiru kamar tayi bacci,itama tayi shiru tana karanta wasikar jaki har bacci yayi awon gaba da ita

Hafsa tana ganin baccinta yayi nauyi tayi tsam ta tashi ta shiga toilet dinsu dake hade da dakinsu, ta doro arwallah, ta shinfida sallaya, tayi nafilolinta da ta saba tadaga hannu tana rokon Allah, ya ganar da salma gsky in aljannu ne ke damunta Allah ya shiga tsakaninta dasu tashafa itama taje takwanta bacci barawo yayi awon gaba da ita.

********
Asubar fari suka tashi sukayi sallah ka’ida ne kullum sai kowa yaje yayiwa Abba da umma ina kwana, daga nan su je kitchen su hada abun Karin safiya, bayan sunkare suje su dan kara kwantawa, idan sun tashi suje suyi wanka.

To ko yau ma haka dince, bayan sungayawa umma, suna so suje gidan bbVuaunty umaima, ta fadawa abba yace

“Allah ya dawo dasu lafiya”

Akafta🤸🏻♀

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 46

Advertisement page 46* ******************* Hafsa hankalinta ya dawo ajikinta, koda ta waiga bataga Salma da khadija ba, nan…
Read More

TARTSATSI 89

Advertisement *Page 89*   *******************   Amarya sadiya ma sanyin asuba ne yasakata dunk’ulewa wuri d’aya, tana rawar…
Read More

TARTSATSI 16

Advertisement Page 16* ******************** Dr sadik ya Kalle ta dakyau yace “Tunda har nazo, dole in saukar da…
Read More

Lu’u Lu’u 41

Advertisement Bismillahir rahamanir rahim_ *41*   Babban teburin falon b’angaren sarauniya Juman aka zauna cin abinci, wanda sarauniyar…
Read More

Lu’u Lu’u 43

Advertisement Bismillahir rahamanir rahim_ *43*   Cikin taushin murya numfashinsu na gauraya yace “Za ki hak’ura ne ko…
INAYAH
Read More

INAYAH 54

Advertisement 54_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Rigar jikinta mara nauyice ta yaye ahankali tareda bayyanarda dogayen Lafiyayyun cinyayoyinta marasa tabo ko…