TARTSATSI 30

Advertisement

*Page 30*

*******************

Sadauki ya kalleta dakyau yace

“Ina saurarenki dafatar dai duk abunda zai fito bakinki ki tabbatar alkhairi ne”

Hafsa tayi hanzarin fad’in “Alkhairi ne idan har zaka dubeshi da fuskar hakan”

Sadauki yace “OK ke nike saurare”

Hafsa ta k’ara sauke ajiyar zuciya tace

“Don Allah wata alfarma ce Nike so kayiman, dafatar bazaka watsa man k’asa a ido ba”

Sadauki yace “Fad’i Kai tsaye, alfarmarki ko wace iri ce, indai bata kasance Abu biyu ba, to nayi maki alk’awali zan karb’e ta hannu bibbiyu”

Salma tayi saurin fad’in
“kamar me da me kenan?”

Advertisements

Ya yi ajiyar zuciya yace

“Ta farko idan bata taka dokar musulunci ba”

Yayi shiru Hafsa tace “Dayar fa”

Ya furzar da iska abakinshi yace

“Na biyu idan har abunda zaki fad’a bazai kawo tangard’a a zamanmu ba”

Hafsa da kanta yake a duk’e, da hanzarinta ta d’ago kanta, ido cikin ido ta kalleshi tace

“yanzu idan nace inaso, ka sadaukar da soyayyarka wurin auntyna, bazaka iya yiman wannan alfarma ba?”

Sadauki yace “Tabbas ko acikin mafalki naga nayi irin mafalki zan tashi in nemi tsari da wannan mafalki,zuciyata kekad’ai take rayuwa da tsantsar sonki da k’aunarki, bantab’a son wata d’iya Mace ba a duniya,sai akanki to akanmi zanbi wannan bahaguwar alfarmar taki, saboda haka ki yi gaggawar ajiye wannan zance naki Marar tushe balle makama”

Nan take Hafsa jikinta ya fara kyarma, nan take hawaye suka faro gangarowa akan kyakkyawar fuskarta, Dan hanzari sadauki ya ciro wani handKchief fari Sol sai k’amshi yake Yi, ya ajiye mata akan cinyarta yace

“Duk wata k’walla taki da kika bari ta sauka a k’asa, tofa kisani tamkar ana d’igawa sadauki dalma ne ajikinshi, saboda haka ruwanki ne ki tausaya man, ko kuma kici gaba da gana man azaba”

Hafsa ba shiri ta kalleshi, Da kwayar idanunshi, yayimata alama da tabbas haka d’inne,aikuwa nan take ta had’iye kukanta ya saka hannu aljuhunshi saiga wata dalleliyar waya daga gani Kai kanka kasan ba k’ananan kud’i aka zuba a wajen sayenta ba, ya kunna wayar saida ta gama searching ta tsaya daidai aikuwa saiga pic d’in sadauki ya bayyana ajikin tsadaddar wayar, ya mik’a mata, baki a sake Hafsa ta sa hannu ta karb’a yanayinta ya nuna alamar tambaya sadauki yayi murmushi yace

“Taki ce ki duba, idan batayi maki ba, sai aje a canzo wata”

Advertisements

Hafsa ta zaro ido waje tace

“Rufaman asiri”

Yayi k’ara yin murmushi yace “ai kam asirinki arufe yake ruf nurul hayaty”

Hafsa nan take kunyar zancenshi ya kamata ta Rufe fuska, sadauki yace

“Wai ke kunya meyasa baki tausayin sadauki ne, sai ina cikin jin dad’ina kizo ki takuraman mata”

Hafsa ta wayance tace

“Nagode sosai, Allah ya biyaka ya saka maka da gidan aljannah”

Ya kashe idonsa yace saura d’aya addu’ar

Tace “wace Keenan? ”

Yace “kice Allah yasa, Hafsa ta zamo matar sadauki, nan da kwana biyu”

Hafsa ta zaro ido ta harareshi tace

“Sai kace d’iyar roba”

Ba shiri sadauki yayi dariya daganan suka bige da hira mai tattareda tsantsar so da kulawa, sadauki ya Karb’i wayar Hafsa yayi ta yimasu selfie haka ma ya d’auko tashi wayar yana ta yimasu, haka ma zoben ya k’ara bud’e shi yace ta bada hannunta ya saka mata ta rasa ta yanda zata mik’a hannunta saboda masifaffar kunyarsa da take ta cizon ta, shikam ko ajikinshi bata tantance ba kawai taji ya riko hannunta yana k’ok’arin saka mata zoben, ita ko sai faman mutsu mutsu take da hannun, Da yaga da gaske take dole ya mik’a mata zoben ya had’e fuska azuwan ba wasa dole sai da tasaka tana ta b’oyon hannun wai kar ya gani yana murmushi yayi ajiyar zuciya yace

“Hafsa ki rik’e sadauki amana, kar ki bari acuci marayan Allah”

Da sauri ta sunne Kai ita kunya yace

“To ni zan wuce, amma kafin in tafi inaso ki turo man kyautar da kikayiman”

Tace “ta mefa?”

Yace “Au har kin manta, auntynki da kika bani kyauta kodai daman kyautar iyakacinta baki ne batakai zuci ba”

Hafsa Hafsa tayi marau marau alamar kuka tace

“Takai ko kana nufin ka amince?”

Ba tareda yayi magana, ba ta k’ara da cewa

“jirani inkirata”

Har ta Fara tafiya, sadauki yayi murmushi, ya kira ta ta juyo, yace da ita

“kice tasameni a waje”

Aikuwa Hafsa ta fita tana ta k’ok’arin share k’waalla, sadauki yayi murmushi cikin zuciyarshi yace

“Ana so ana Kai kasuwa”

Yasa kanshi ya fita waje, yana jiran zuwan salmar.

Acen cikin gida ma ba tsumaniyar da salma batayi ba, akan tana so ta fito su gaisa da sadauki, umma ta hana, saboda ayukan da tayi ta saka salmar, tareda kasawa ta tsare, don kar ta samu hanyar fita, batareda ta sani ba.

Shigowar Hafsa yayi dai dai da bugun k’irjin salma Hafsa ta k’araso a kusa da ita tace

“Yace kije ku gaisa”

Hafsa jiki yana kyarma taja hijabi tayi waje cikin sauri, don karma umma ta dakatar da ita, Tana fita tayi tozali da kyakkyawar fuskar sadauki, nan take wani farinciki ya ziyarci zuciyarta tareda bayyanarshi akan fuskarta, ta k’araso da sallama, sadauki dake jikin mota a tsaye, da kb dake zaune sit d’in direba, duk suka amsa mata sallama.

Sadauki ya kalleta fuska ba walwala yace

“Salma ko? ”

Tace “Eh”

Yace “naji sak’onki a wurin Hafsa”

Salma ta Fara washe baki tana sunne Kai.

Sadauki yakai second goma zuwa sha daya kansa yana du’ke sannan ya d’ago fuskarshi ya dubeta dubi irinna renin hankali d’innan, aikuwa salma nan take hantar ta Kad’a, sai jikinta ya Fara kyarma, domin jikinta ya bata duk abunda zai fito a bakinshi, cikin wannan lokacin to tabbas ba alkhairi bane.

“Me yasa ke baki son Hafsa irin son da take maki?”

Kafin ta bashi amsa ya k’ara da cewa

“Allah ya albarkaci Hafsa da kyakkyawar zuciya, wanda wannan halin da ta nuna ya k’ara rub’anya son da nike yimata, sau million acikin zuciyata, ina son Hafsa son da ni kaina bansan adadin shi ba, raba ni da ita tamkar rabani da rayuwata ne, matuk’ar Hafsa Tana numfashi to tabbas ina gaya maki, ba wata d’iya da zata samu damar da zan d’aga ido, in kalleta da sunan so, saboda haka ki rubuta ki ajiye, koda ace yau Hafsa Allah yayi Wa’adinta ya cika, to tabbas sai an d’aura mani aure da gawarta, inmata wanka in binne ta da hannuna acikin k’abarinta, kisani nida Hafsa munzamo hanta da jini, rabamu nida ita abune mai matuk’ar wahala”

Ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya yace

“Ni Umar farouk sadauki Bashir dala na mallakawa Hafsa zuciyata”

“Kiyi hak’uri auntynmu, Allah ya baki dai dai ke don nikam an riga anbada sadaka ta na barki lafiya”

Ya shigewarshi mota kb ya tada suka fisgeta da k’arfi tareda bad’a mata k’ura suka wucewarsu.

Salma kam nan take hasken dake idonta yayi low, ta fara tafiya kafafu suka sark’e, dif nefar idanunta suka d’auke, sai ji kake tiiiimm! Ta fad’i a k’asa sumammiya .

Yau ana tartsatsi😱

Akafta🤸🏻♀

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 8

Advertisement €pisode 8……………………. Cikin daƙiƙa uku Tsuntsu Bilbil ya sauka gabansu na Naheela. Cikin kakarin jini ta shiga…
Read More

TARTSATSI 3

Advertisement   ☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️ Home of qualities and trusted writers of the nation https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp…
KALLABI
Read More

KALLABI 32

Advertisement BABI NA TALATIN DA BIYU Duk yadda Aminatu taso kin shiga cikin gidan haka Innayoh ta tisa…
KALLABI
Read More

KALLABI 30

Advertisement BABI NA TALATIN CIF Cikin rawan jiki da tarin zazzaɓin da ya rufe su dukkan su, suke…
KALLABI
Read More

KALLABI 29

Advertisement BABI NA ASHIRIN DA TARA. “Ta zame min mara amfani, wanda ba zan kuma amfanar rayuwa ta…