TARTSATSI 31

Advertisement

*Page 31*

**********************

Fad’uwar salma, yayi daidai da fitowar Hafsa daga gida, da gudu ta k’araso wurinta, tareda k’walla wata masifaffiyar k’ara tace

“Salma!!!!!!!!!”

Saiga motar Dr sadik ya danno kai, yana k’ok’arin gyara parking ne, ya hango salma kwance a k’asa ba alamun numfashi atare da ita, ga Hafsa durk’ushe a kanta ta rungumota ajikinta tana ta gurzar kuka tareda kiran.

“Wayyo salma kar ki mutu kibarni, aunty salma ki tashi”

Sai faman girgizata takeyi amma ina ko gezau ba alamun numfashi atattare da ita.

Atsiyace Dr ya fito ya isa wurinsu, da hanzarinsa, ya sa kara kanshi saiti da zuciyar ta, nan take gumin tashin hankali ya karyo mashi, ya d’ago kansa ya rik’a tsintsiyar Hannunta, ya danna ‘yan yatsun shi biyu saiti da jijiyar ta, yaji Tana halbawa alamun akwai kingin numfashi atare da ita, da saurinshi ya d’auketa cancakar ya sakata mota, ya zagayo ya shiga ya tada ita da saurinshi, Hafsa atsiyace ta nufi hanyar shiga cikin gidan nasu.

Dr yayi saurin kallonta yace

“Asibiti zamu fa ina zakije kuma?”

Advertisements

Hafsa tace “umma zanje in fadama wa, kar tayita neman mu, ba’asan inda muka je ba”

Dr yace “zo zo Muje bamu da isashen lokaci rayuwar ta tana cikin k’ila wa k’ala”

Da gudu hafsa ta dawo ta fad’a motar, tareda rungumo salmar ajikinta tana gunshek’an kuka, ad’ari Dr yaja motar akayi dai dai da fitowar usman daga gida, ya hango salma tana ta Kuka cikin motar, kafin ya tantance Dr yaci ribas da k’arfi har sun bar k’ofar gidan.

Da sauri usman ya koma gida yana fad’awa umma, umma hankali tashe taje wurin Abba ta sanar dashi, Abba da yake yana da number’r Dr don yana kiranshi shi wani lokaci suna gaisawa, ai kuwa ya danna masa kira har ta tsinke Dr baid’auka ba Abba ya k’ara kira Dr dake k’ok’arin yin parking a cikin harabar asibitin nasu sai lokacin ya ga kiran na Abba saida yama gyara zaman motar yana bada umurnin a d’auko gadon d’aukar maralafiya lokacin har kiran na Abba ya k’ara tsinkewa sannan cikin sauri ya bi Abban da kira, bugu d’aya Abba ya d’auka kafin Abba yayi magana Dr ya gaidashi yace

“Muna tare da Hafsa a asibitin mu salma batada lafiya”

Abba cikin hali nasu irin na manya, ba tareda ya tsaya tambayar komi ba, yace

“Allah ya bata lafiya gamunan zuwa yanzu”

Dr yace “Ameen” tareda kashe wayar, akayi dai dai da masu d’aukar mara lafiya sun k’araso, shida hafsa suka fiddota aka d’ora ta a kan gadon, Dr ya bada umurnin ayi sauri akaita emergency room, aikuwa haka akayi hafsa tana biye dasu tana kuka, ba k’aramin tausayi zata baka ba in ka kalleta, irin yanda nan take idonta sukayi ja suka kunbure fuska tayi jawur.

Bayan anshige da salmar ne, Dr da sauran likitocin da ya gayyato tareda nurses suka wuce da sauri,suka shiga suma, saboda yana cikin rud’u sosai, shiyasa ya Nemo taimakon wasu likitocin ‘yan uwansa, don su taimakamasa.

Hafsa dai tana kan wata kujera a zaune, ta dafe Kai sosai saboda wani masifaffen ciyo da yake yimata, sai faman tunani takeyi, me yasa salma suma, meya faru tsakaninta da sadauki, wanda har ya sanya ta shiga, acikin wannan mayuwacin halin.
Tana cikin wannan tunanin ne, taji muryar umma da Abba sun zo, da sauri ta d’ago kanta tayi wurin umma, ta rungumeta ta sake aza wani sabon kuka, da sauri umma ta d’agota tace

“Ya isa kukan haka”

Umma tajawo hannun hafsar, suka zauna kan kujerun dake jere a wurin, tana tambayar ta

Advertisements

“Me yasami salmar ne? don itadai tasan lafiya lau ta fito daga gida, kodai kid’e ta akayi ne?

Hafsa tace

“wallahi umma nima bansani ba don fitowa ta Kenan naga faduwar ta”

Umma tace “to ina bak’on naki?”

Hafsa tana share hawayenta tace

“Koda na fito ya tafi”

Aikuwa nan take umma ta hasko abun,da ya faru tamkar tana wurin akayi, wato dai watak’il ya nuna mata Hafsa yake so, ba ita ba, shine mafarin suman Nata, nan take jikinta yayi sanyi, ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, tace

“Allah ya bata Lfy”

Hafsa da Abba da sauran mutanen dake wurin, gabaki d’aya sukace “ameen”

Sun kwashe wajen awa biyu kafin a fito da ita Abba tun yana tsaye har yakai zaune zuciyarshi d’auke da addu’ar samun sauki agareta.

Ba k’aramin namijin k’ok’ari doctors sukayi Akanta ba, don kuwa tayi nisa sosai, dak’yar suka shawo kan matsalar, tareda yimata allurar bacci, don zuciyarta dake barazanar kamuwa da heart attack.

Bayan an samu nasarar ceto ranta ne aka gungurota aka fito da ita,hafsa dasu umma duk suka mike tsaye suka isa wurin ta, gata kwance samb’al tamkar matatta, banbancin kawai numfashinta da ke sauka a hankali, wanda saika kula ma ne zaka lura da Hakan.

Abba da Dr suka tsaya suna gaisawa, yayinda umma da Hafsa suka bi masu tura gadon, tareda nurses d’in da ke biye a bayansu, har aka kaita wani d’aki na musamman wanda ita kad’aice zata zauna acikinshi bayan an azata kan gadon ne aka mak’ala mata k’arin ruwa sauran nurses d’in suka k’are aikinsu suka fita, sai ga Dr ya shigo tareda Abba, ya gaisa da umma umma tayita yimasa godiya don ba k’aramin jin dad’i sukayi ba da irin wannan d’awainiya da yayi da ba, yana jin kunya yace bakomi ai yiwa kaine, daman cen Abba kafin su shigo ya yi masa godiya.

Bayan sun k’are godiyar ne, Dr ya gyara tsayuwa yace dasu,

“Kasancewar duk abun na gida ne, zan fad’a maku abinda bincikenmu ya bamu, dangane da abunda ya haifar da wannan doguwar suma da salma Tayi, hakika nin gaskiya akwai abunda taji Wanda ya razanar da ita, ya firgitata wanda shine yayi sanadiyyar tab’a mata zuciya, jikinta ya kasa jurar wannan abun shine yayi sadadiyyar sumewar ta, amma yanzu insha Allahu nan da awa biyar zata farfado saboda anyimata allurar bacci don zuciyarta ta samu relief”

Ya k’ara da cewa “sannan mungano tun kafin yanzu, akwai damuwa sosai a tattare da ita, wadda itama ce ta k’ara haifar da matsalar da ta faru yanzu”

Abba da umma suka Kalli juna, Abba fuskarshi d’auke da alamar tambaya, yace da umma,

“Me ya fitar da salmar waje?”

Umma jiki ba kuzari tace

“Wanda yazo wurin Hafsa ne yace tazo su gaisa”

Abba ya dawo da tambayarshi gun Hafsa yace

“Koda kika fita waje ita da wa kika ganta?”

Hafsa ta share k’wallar ta tace

“Ita kad’ai naganta kasa ta fadi”

Abba ya sauke ajiyar zuciya, yace
“Allah ya bata lafiya, domin ita kad’aice, zata bamu wannan amsar”

Dukansu suka ce “Ameen” suka maida hankalin su kanta suna kallon yanda numfashinta yake sauka a hankali tana ta bacci.

Dr yayi mata Allah ya sawak’e ya fita tareda Abba, umma da Hafsa kam suna nan zaune, sun sakata agaba suna ta kallonta, amma fa kowanensu akwai abinda zuciyar shi take ta karanta mashi, har akayi mag’riba Dr yayo sayayya nik’i nik’i ya kawo ya ajiye, umma kunya kamar me sukayi mashi godiya ya fita, umma ta shiga toilet d’in dake cikin d’akin domin d’oro arwallah, saigashi ya dawo da katotuwar carpet ya baiwa Hafsa ya fita, ta karb’a ta shinfid’a masu, umma ta fito itama ta shiga ta yo arwallar.

Bayan sunk’are sallahr ne tareda yiwa salma addu’ar samun sauki, saiga Abba ya shigo yace zaije gida ya d’auko masu kayan but’atar asibiti.

Hafsa tayi saurin cewa

“umma kuje gida ni zan kwana da ita”

Umma Tayi murmushi ta dafa kanta tace

“Kije kibi Abbanku ki had’o muna
kayan, a kawo muna, gobe sai ki yomuna abin Kari ki zo muna dashi”

Hafsa ta marairece fuska tace

“Ko naje gida hankalina bazai kwantaba umma, nafiso inga farkawarta a gaban idona”

Ta fashe da kuka Umma tayita, lallashinta sannan ta Yi shiru taje kusa da gadon da salma ke kwance ta rik’o hannunta, Tana ta kallon fuskarta wani kuka ya tuk’ak’ota ta fita d’akin cikin sauri tana gunjin kuka, Abba da umma suka biyota suna ta faman lallashinta, cikin kuka Hafsa tace,

Umma bamu tab’a raba wurin kwana ba nida aunty salma, amma yau gani kwana Nikad’ai akan katifarmu ita kuma akan gadon asibiti ta k’ara sautin kukanta, ita kanta umma saida wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, Abba da yaga abun nasu zaiyi girma, ya rik’a hannun Hafsa da alamar ta taso suje, ba musu ta bishi Tana sharar hawaye.

********

Abangaren sadauki kuwa sun fara tafiya ne kb ya dubeshi yace

“Amma dai gaskiya baka kyautawa wannan bab d’in ba, wai meye sirrin wai nifa duk kasani a duhu”

Sadauki nan take ta k’ara had’e fuskarshi yace

“In har zakayi ta biyu da ita ne, kawai ka fad’i malam, ashiga nema, nan da wata biyu sai kazamo mijin Mace biyu”

Kb ya Sosa kanshi yace da sadauki

“Dadai ace ko shekara nayi da aure, to da tabbas zan shiga neman aurenta, don nidai tayiman gaskiya, amma yanzu kam bazan jaza wa kaina aiki ba, aure wata uku kacal in kinkimo wani sabo don nazama akuri sarkin aure”

Ya k’are maganar yana dariya, sadauki shima ya dara batareda ya kalleshi yace

“Ai da biyu akace mu fara ko? In har zamuyi adalci, ko Kai baka cikin masu adalcin ne? ”

Kb ya tuntsure da dariya yace

“Baka ciki dai kai amma nikam ina ciki”

Sadauki ya kalleshi yace “saboda mi ni ka cireni a lissafi”

Kb yace “a yanda ka riga ka mato da soyayyar Hafsa, gaskiya da wuya inzaka iya yin adalci tsakaninta da wata”

Sadauki yayi murmushi yace

“Ya akayi ka gano?”

Kb ya fara dariya yace

“Ai ni naga abunda na gani shiyasa, waima don kuturun wulak’anci, shine ka shanyani a waje, kana cen kana ta soyewarka, ko abincin ka bari inji ya yake amma zalamar ka ta hana”

Sadauki yayi dariya yace,

“So kake yau nuratu tasa maka bak’in Glass ko? Kama gode ma Allah da bakaci ba, don in har kacika cikinka, to ita nata zubarwa zakayi kenan?”

Kb yace “ba wani wayo da zakayiman, kawai dai kace, ba rabona aciki, shiyasa banci ba”

Kafin kb ya ya Kai karshen maganarshi, sadauki ya dafe goshi yace

“kash!!!!! ”

Kb ya Yi saurin kallonshi yace “yade”

“Na mance ban bada kayan da nazowa su Abba dasu ba, waccen yarinyar duk tasa na rud’e gabaki d’aya juya mu koma kawai”

Da sauri kb yayi Rivas ya juya suka koma, suna zuwa akayi dai dai usman yana ta kwallo da abokanshi biyu a k’ofar gida, kasancewar shi yaro bai kawo wutar abinda ya dace ba, shiyasa bai wani damu ba da ciyon na salma.

Sadauki ya fita ya bud’a but ya kira usman da baima lura said zuwan nasu ba saboda k’wallon da ta d’auke mashi hankali, da gudunshi yazo ya fara gaidashi sadauki ya amsa fuska sake yace

“Usman ko? kira abokanka ashiga da wad’annan kayan”

Usman ya d’aga murya ya kirasu suka zo da gudunsu, suka fara jidar ledodin, suna kaiwa cikin gida suna dawowa, sunyi wajen maya biyu sannan sadauki ya rufe but din, ya ciro kud’i ya rarraba masu sunata murnar ganin sababbin kud’i, sannan kb ya tada motar suka wuce.

 

Masu zuwa ganin salma asibiti suzo muje๐Ÿƒ๐Ÿปโ™€๐Ÿƒ๐Ÿปโ™€๐Ÿƒ๐Ÿปโ™€๐Ÿƒ๐Ÿปโ™€๐Ÿƒ๐Ÿปโ™€

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 12

Advertisement ยฃpisode ~12 GANYE……. Iskan da ke kaษ—awa ko ina zai tabbatar maka da ruwan sama ke shirin…
Read More

TARTSATSI 52

Advertisement *Page 52* ********************** Da gudu usman yazo kan Umma, yana girgizata tareda kiran sunanta, amma ina Umma…
KALLABI
Read More

KALLABI 5

Advertisement *<Babi Na Biyar>* EWF “`Wannan shafin gaisuwarki ce Mammyn Afreen ki more pagen da gasken gaske… Ina…