TARTSATSI 32

Advertisement

*page 32*

*********************

Hafsa suna tafe a cikin mota, Abba yana ta bata hakuri akan ta kwantarda hankalinta, insha Allah gobe lafiya lau salma zata tashi, Hafsa sai faman share k’walla takeyi, cikin zuciyarta sai sak’a da warwara take, na abunda taga zai fiddo da su cikin wannan tartsatsi, ita da ‘yar uwarta, amma duk hanyar da ta kamo, sai taga ashe ba Mai b’ullewa bace, har suka je gida Hafsa batamasan sunje ba, saboda tunanin Mafita.

Koda Abba ya kawo Hafsa gida, da sauri ta harhad’a abunda tasan za’a buk’ata taje tasaka cikin motar, Abba ya ja ya koma asibiti, ita kuma tashige gida.

Usman da umar da autar umma habiba, suna tsakar gida suna cin abinci, Hafsa ta shigo haka kawai sai taji yaran sun bata tausayi, saboda suma kansu tartsatsin ya fara shafuwarsu, basuji basu gani ba ta share k’wallar dake k’ok’arin sauka a saman kyakkyawar fuskarta, taje kusa da habiba dake ta cin abincinta amma da Kalli fuskarta tasha kuka, idonta sunyi jawur, Hafsa ta dafa kanta tace

“Autar umma abinci kike ci?”

yarinyar ‘yar shekara hud’u ta d’ago fuskarta tana so tayi kuka tace

“Aunty kinga yaya usman ya buge ni”

Hafsa ta kalli usman tace

“Haba yaya usman me autar umma tayimaka da zaka bugeta?”

Advertisements

Usman yayi dariya yace

“Keko aunty wai dole sai na kaita wurin umma, da ta damemu da kuka ne, niko na bugeta”

Hafsa tace “Haba usman baka ganin kai yaya ne, ko kanaso ta renaka”

Usman ya girgiza Kai Hafsa yace “To kadaina kaji ko”

yace “to”

Tace “kunyi sallah?”

Sukace “Eh”

Umar yace

“Amma aunty yaya usman yace wai kar muje masallaci”

Kafin hafsa tayi magana usman ya harari umar yace

“Halan bakaga, yanda
autar umma take ta kuka ba? da ita kakeso muje masallacin, Tayi kuka kasa akoro mu ko? To ba’a je ba d’in”

Hafsa tayi murmushi tace

Advertisements

“To yanzu dai kowa yayi hak’uri, inkun k’are cin abincin kuje kuyi sallar Isha’i, kuyi wa aunty salma addu’a, Allah ya bata lafiya”

Duk suka ce “Ameen”

Ta dawo wurin autar umma ta k’are cin abinci, wanke mata hannu, ta Yi mata wanka ta kaita d’akinsu ta shinfid’eta kan katifarsu, ai kuwa kamar jira take nan take, baiwar Allah tayi bacci.

Hafsa kuma bayan ta k’are komi daya dace tayi, sannan tazo ta kwanta a gefen katifarsu, ta tsunduma tunani, nan take wani marayan kuka yazo mata, saboda tausayin kanta da takeyi, bata tab’a jin damuwar rashin uwa ba irin wannan rana, ashe dai ita uwa wani ginshik’i ne ga arayuwar ‘ya’yaye, duk wani gata da zaka samu, sai anyi ranar da zakayi kukan rashin su acikin duniya, don yanzu haka tanaso, ace ta fad’a wa wani wannan damuwar da take ciki,kodon ta rage girman abunda ke nuk’urk’usarta cikin zuciya,amma to wa gareta bayan umma, kuma bazata so ta sanadin hakan rashin jituwa ta shiga tsakaninta da salma ba,tayi zurfi da tunanin ta ne, gwaggo haja ta fad’o mata arai, kasancewar ta uwa d’aya uba d’aya da mahaifiyarta, to amma inda matsalar take muddin ta d’auki matsalar ta kaiwa gwaggo, to tabbas tamkar taci amanar umma ne, take gani saboda irin k’aunar da umma take yimata, bai kamata ta fallasa wannan sirrin ba, ga kowa, don tana gudun abunda zaije ya dawo, Aikuwa nan take ta k’ara fashewa da wani azababben kuka, wanda duk wanda yajishi sai ya tausaya mata.

Ta d’auki tsawon lokaci tana ta risgar kuka, aikuwa ba shiri wani sautin kid’a mai dad’in sauraro ya fara tashi, da sauri Hafsa ta tashi zaune gaban ta sai fad’uwa yakeyi, sai waige waige take tana neman ta ina kid’an ke tashi, ai kuwa caraf idonta suka sauKa kan wayar da sadauki ya bata, dake ajiye a kan madubinsu na kwalliya, da umma ta ciro a d’akinta, ta kawo masu, wanda a acewar ta sunfita buk’atarshi.

Cikin zafin nama ta tashi taje ta dauko wayar, ta zauna don ita shaf ma, ta mance da ita, cikin kasalar jiki tareda k’aruwar bugun zuciyarta, tasa hannu ta danna tsanwa, aikuwa saiga muryar sadauki rangad’ad’au yana cewa

“Assalamu Alaikum”

Hafsa tayi k’ok’arin saita kanta, tareda jarumtar fito da muryarta da ta shak’e, saboda tsananin kukan da ta gurza, tace

“Wa’alaikumussalam ina wuni”

Ta k’are maganar bakinta yana rawa, sadauke dake kwance, ba shiri ya tashi zaune yace

“Wa ya saki kuka? me akayi maki,?wa ya b’ata maki rai? har yasa kikayi irin wannan kukan? da muryarki ta shak’e ko magana ma baki iya yi? ”

Nan take Hafsa ta k’ara kid’imewa jikinta ya d’auki rawa tayi jarumtar cewa

“Ni banyi kuka ba, kaina ne yake ciyo”

Sadauki bakinshi har rawa yake yace

“Ganinan zuwa yanzu muje inkaiki asibiti”

Wani fad’uwar gaba ya ziyarce ta, jikinta yana kyarma tace

“Don Allah kayi hak’uri kar kazo, wallahi lafiya ta lau, aunty salma ce batada lafiya, tana asibiti”

Baisan lokacin da ya sauke, wata nannauyar ajiyar zuciya ba yace

“To shine zaki zauna kina ta kuka, don salon ki cutar dani ko?”

Hafsa jiki ba k’wari tace

“Kayi hakuri, amma kasan dole inshiga damuwa ko?”

“Miye amfanin damuwa, da wadda bata damu da taki damuwar ba, haka kawai, kiyi ta wahalda kanki abanza”

Hafsa ta zaro ido waje tace

“‘yar uwata ce fa ko ka manta?”

Kafin ya bata amsa tace

“Dazu bayan kun wuce muka ganta a k’ofar gida, ta fad’i sumammiya, dukanmu bamusan me yasameta ba, yanzu haka tana asibiti kwance”

Sadauki yayi murmushi yace

“Allah sarki Ashe abun yayi girma da yawa,to Allah ya bata lafiya”

Hafsa tace “Ameen amma ai zakazo, dubata kafin ka wuce ko?”

Sadauki yayi wani kallo, kamar yana ganinta yace

“Miye Alak’a ta da ita da zanzo ganinta nikam, amma dai inada shawarar da nikeso inbata ki fad’a mata?”

Hafsa jikinta yayi sanyi tace

“Allah yasa ba kaine silar suman ta ba dai”

Sadauki yace “ohon mata, nidai na fad’a mata gaskiya ne, iya wuya ina tare da Hafsa matar sadauki, nan da wata biyu masu zuwa, insha Allah,saboda haka ki fad’a mata cewa, zafin nema fa baya kawo samu, ni na Mace d’aya ne, d’ayar ma wadda ta cancanta, ba gudu ba ja da baya”

Dan take wani gumi ya karye wa Hafsa duka ilahirin jikinta gaba d’aya saboda yanzu ne tagano abinda ya jefa salma cikin mawuyacin hali bakinta yana rawa tace

“Don Allah don girman Allah, ka ceci rayuwar ‘yar uwata, saboda rayuwarta tana cikin had’ari, muddin bata sameka ba”

Sadauki yayi wata dariya yace

“Don Allah, Don girman Allah, kibar sadauki da masoyiyarshi, farin cikinshi, annurin zuciyarshi, hasken idonshi Hafsatttt!!!”

Hafsa da shiri ta kashe wayar ta jefar da wayar ta girka sabon kuka, sadauki ko sai faman kira yake Yi, da ta tsinke ya k’ara wani, sai da yaga da gaske bazata d’auka ba, sannan ya daina kiran, minti biyu tsakani saiga k’arar shigowar text

Da sauri takai hannunta ta bud’a text d’in, don a tsammaninta cewa zaiyi ya amince, sai taga sabanin haka .

Ga abunda ya rubuta

Sak’o yana nan na baiwa k’anenki, kiyi k’ok’ari ki kaisu ad’inke maki, kafin in dawo, don ni atsarina ina son kullum inga matata, a cikin kwalliya da sabon kaya.
Bye
Mijin Hafsat

Hafsa jiki a sanyaye ta ajiye wayar, ta shiga tunanin wad’anni kaya ne yabada, tsam ta tashi ta shiga d’akin umma, don tasan yanzu dai kam su usman sunyi bacci, don haka bazata tashe su ba, tana shiga uwar d’akin umma, ta dafe kirji ganin tulin ledodi kamar hauka, jiki ba k’wari ta isa wurin kayan, ta Fara bud’awa, ledar farko shaddodi ne, daga gani kasan ankashe nera wurin sayensu, yadi goma goma har guda biyar, tareda wasu kwalayen turare designers wad’anda randa take bata tab’a ganin irinsu ba, da wasu kudi d’aure dami guda, a jikinsu an rubuta 50k, Da alama dai na Abba ne ake nufi.

Tayi ajiyar zuciya ta bud’a wata ledar saiga Atamfofi guda biyar Suma, tareda kudi aciki ansa 20k,nan take hafsa a ranta ta furta na umma ne.

Ta matsa a kusa da wata k’atuwar leda, wadda tafi kowace girma, acikin su, ta bud’a wasu rantsama rantsaman lesussuka ne guda uku, Kai daga gani ba irin na k’ananan mutane bane(wato irinmu kenan) sai atamfofi guda biyar da shadda biyu,da d’aurin kud’i 100k ajiki, da sauri Hafsa ta saki ledar, taja da baya, arikice ta fito a d’akin, tasa makulli ta rufe, jiki yana rawa ta shige d’akinsu, ta dantse da makulli, ta haye katifarsu sai rawar sanyi take.

 

Tofa nima kam nayi nanπŸƒπŸ»β™€πŸƒπŸ»β™€πŸƒπŸ»β™€πŸƒπŸ»β™€πŸƒπŸ»β™€

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 25

Advertisement *Page 25* ********************* Aliyu yayi murmushi yace “‘yan biyun umma, k’anne na ne, kuma k’annen Auwal ne…
KALLABI
Read More

KALLABI 5

Advertisement *<Babi Na Biyar>* EWF “`Wannan shafin gaisuwarki ce Mammyn Afreen ki more pagen da gasken gaske… Ina…
Read More

TARTSATSI 79

Advertisement *Page 79* ******************** Yanda hajiya Zulai ta kwana da alwashin zuwa wurin boka, domin afarrak’a auren Aliyu…
KALLABI
Read More

KALLABI 17

Advertisement BABI NA SHA BAKWAI *GAISUWARKU CE A WANNAN SHAFIN MASOYAN KALLABI NAGODE SOSAI* “Fita aka ce maka,…