TARTSATSI 33

Advertisement

page 33*

*********************

Nan take wani zazzabi ya rufeta, saboda lamarin na sadauki, ba k’aramin tsorata ta yayi ba, cikin zuciyarta tace

“wannan ai almubazzaranci ne, taya zai zube tsibin dukiya irin haka, duk saboda mace, macen ma irina marainiya, sai kace wanda baisan zafin nema ba”

Ta ta shi ta d’auko paracetamol ta sha, ta janyo bargo ta lullub’e,sai rawar sanyi takeyi, Tana ta faman nazarin, ina mafita cikin wannan lamari nata, don fa ita gaskiya tana son sadauki, amma in ta tuno da yanda salma take son sa, sai taji wani katoton abu, ya tsaya mata a zuciya, wannan ai shine ga k’oshi ga kwana da yunwa, haka dai ta kwana Tana ta tunanin zuci, sai ta Fara kuka, in ta tuno da sadauki da barkwancinshi, sai ta koma yin murmushi.

Abangaren umma kuwa,A zaune take sai faman kallon salma takeyi, tana share hawaye, tana tsananin jin haushin d’aukarwa kanta kayan da bata iyawa, da tabi shawarar da take bata to da tabbas duk abun bai yi tsanani har haka ba, yanzu gashi wanda takeson yazo amma ita ba itace a gabanshi ba, ta k’udurta a ranta, muddin Allah ya sa ta farka lafiya, zata bata shawarar abunda zai fisheta, daga cikin wanga bak’in TARTSATSIN wahala, hankalin kowa ya kwanta don yanzu ne take da damar hakan batare da kowa ya sani ba.

Aikuwa haka akayi bayan awa biyar d’in da akace zata farka umma cikin gyangyadin da ya fara d’aukarta ne taji salma ta Fara tari, umma afirgice ta farka, Tana ganin salma ta farka, sai murna ta maye gurbin firgicin, fuska d’auke da farinciki ta matso kusa da ita.

Salma cikin dusashiyar muryar mara lafiyan da yasha jiki tace,

“Umma ruwa”

Umma tace “bari a kira Dr don yace da anga kin falka akira shi”

Advertisements

Aikuwa haka akayi umma ta fita da sauri, taje fad’awa nurse d’in dake kusa farkawar salma, kafin ma nurse taje kiranshi ma sai gashi ya zo, daman cen yasan ko yaushe cikin lokacin zata iya farfad’owa, shiyasa ya zo Kai tsaye, yana zuwa yace da umma,

“Ta falka ko?”

Umma tace “Eh”

A tare suka shiga cikin d’akin, koda sukaje sun isketa, tana k’ok’arin tashi zaune, amma takasa saboda rashin k’arfin jiki da batada, da sauri umma ta isa wurinta ta taimaka mata, ta tashi zaune, aka saka mata filo abayanta ta jingina, Dr ya cire mata k’arin ruwan da ke mak’ale a hannunta, umma ta kalleshi tace,

“Tace abata ruwa tasha za’a iya bata?” .

Dr yace “Eh zata iya cin komi, amma kafin nan afara bata tea”

Umma tace “to”

Tareda yunk’urawa domin had’a mata, cikin sauri Dr yace

“umma bari jeki ki zauna, bari kawai in iyar da ladata”

Ya k’are maganar yana murmushi, itama kanta umma taji dad’in yanda Dr yake baiwa salma cikakkkiyar kulawa, yanzu ta k’ara tabbatar da cewa Dr yana tsananin son salma, kuma so na tsakani da Allah, da ace zata yiwa kanta karatun ta nutsu, da ta gano abunda yafi dacewa da ita, ba hasashen banzan ta ba.

cikin kayan siyayyar da Dr yayo masu, daman akwai kayan tea aciki, bayan ya k’are had’a mata tean ne ya tashi tsaye ya mik’a mata, jiki a sanyaye salma ta karb’a, saboda haka kawai yau Dr ya bata tausayi, a cikin ranta tace

“Ashe haka kakeji kaima?”

Advertisements

Dr ya kalleta yayi murmushi yace

“ya kike jin jikin naki a yanzu?”

Tace “da sauk’i sai kawai rashin k’arfi da nikeji a jikina”

Dr yayi murmushi yace

“OK kiyi k’ok’ari kisha tea d’in, sai kid’an ci wani abu, koda kad’an ne, bari inje indawo, Allah ya bidi lafiya”

Umma dake kallonsu suke bata sha’awa tace

“Ameen”

Itama salma ta amsa akan lab’b’anta, tareda yimashi wani duba na tausayawa, yafita yana murmushi farin ciki fal ranshi, saboda ya hango matakin nasara a cikin k’wayar idonta.

Bayan ya fita ne umma ta matso tace

“kisha shayin fa kada ya huce”

Salma ta d’aga Kai ta Fara sha, tana ta kurb’a a hankali har ta shanye, umma ta karb’i kofin ta ajiye ta jawo ledar da Dr ya kawo masu da dare, ta bud’a wata dank’waleliyar kaza ce taji gashi har wani nason dad’i takeyi tareda Irish da yaji suya mai kyau had’e da kwai umma ta zuba mata a plate ta mik’a mata itama ta d’an zuba tanaci, salma saida taji cikinta yayi nauyi sannan ta hak’ura da lodawa, saboda ba k’aramar yunwa tajiya ba, bayan ta k’are ne umma ta kawo mata ruwa tasha.

Umma ta dubeta tace

“zaki iya yin sallah a yanzu? domin ki rama sallolin da ake biyarki?”

Salma tace ummar ta kama ta, sai ta tashi, umma ta rik’a ta, ta kaita toilet, bayan ta k’are abunda zatayi ta d’an lallab’o ta fito, umm tana ganinta Tayi Sauri ta rik’o ta, daman cen ta shinfid’a mata carpet, ta bata hijab ta saka, ta samu daga zaune ta ranka sallolin da ake biyarta, bayan ta k’are ne umma itama tazo saman carpet d’in ta zauna, ta dubeta dakyau tace

“Ya jikin?”

salma tace “jikina yad’an fara warwarewa”

Umma tace “Alhmdllh”

Salma tace “ina Hafsa?”

umma tace “tana gida tun da sassafe nasan zata shigo, don bata ma so tafiya ba, sai kuka take tayi, sai anbarta ta kwana wurinki”

Salma nan take ta tuno da tozarcin, da sadauki yayi mata,akan Hafsa ai kuwa sai hawaye shar shar, umma tace

“Lafiya kuma daga magana, sai kuka?”

Salma tace “wani Abu na tuno umma”

Umma ta gyara zama tace

“yawwa dama ina son intambayeki, wai miye dalilin suman ki?, me kika gani wanda ya firgita ki har kika sumea k’ofar gida?, nidai nasan kinzo ne wajen bak’on Hafsa domin ku gaisa, sai gashi kawai akace, anganki a k’ofar gida kin suma”.

Salma wasu hawaye ne masu zafi, suka zubo mata a kyakkyawar fuskarta, da ta d’an nuna rama, cikin kwana d’aya rak da kwantawarta jinya, sai share hawaye take faman yi, amma ta kasa yin magana.

Umma ta kira sunanta, da murya mai nuna alamar, duk maganar da zata fito a bakinta, to tabbas mai muhimmanci ce,tace

“Ummusalma, kiyiwa kanki k’iyamullaili, ki raba kanki da son maso wani da kikeyi, wanda masu iya magana suka kirashi da koshin wahala, nasan komi dake faruwa a tsakaninku, keda Hafsa, dangane da d’an gidan Alhaji Bashir dala dake sonta”

Cikin sauri, tareda nuna firgici da jin lafazin na umma, salma ta yi saurin d’ago kanta ta kalleta fuskar ta d’auke da mamaki.

Umma ta jinjina mata Kai, alamar da gaske takeyi, tareda k’ara had’e fuskarta, alamar ba wasa cikin maganar da sukeyi.

Umma ta sauke ajiyar zuciya tace

Salma daga yau inaso ki ajiye komi, ki fuskanci abinda zai haifa maki, d’a mai ido, kiyi nazari dakyau, Yaronga Hafsa yakeso ba ke ba, sannan abunda na fahimta itama fa tana sonshi, kawaici ne kawai take yimaki, saboda hankali da ta fiki, shin akanmi ke bazaki yimata halacci ba, ki tayata son abinda takeso, ba wai ke kiyi k’ok’arin cusa kanki, inda ke da kanki kika san cewa, bakida kwarjini a wurin, wallahi ki tsaya ki fuskanci rayuwa, ki banbance fari da baki, domin kisamowa kanki salama a zuciya”

Salma sai wani k’aton kuka da ya zomata ba tareda ta shirya mashi ba cikin kukan tace

“Umma nariga Hafsa sonshi fa, na dad’e ina yiwa kaina tanadin wannan mutumen, amma sai gashi kwatsam don mugunta, yak’i zuwa wurina yaje wurin ‘yar uwata, da mukafi shak’uwa da ita, da kowa a duniya, wallahi nidai ba’a yiman adalci ba”

Umma ta zura mata ido sosai tace

“Kinji rashin hankalin naki ko, to bari kiji saboda wad’anga wawanyun halayen naki ne, Allah yayi maki irin wannan jarabawar, in zaki tuba ki koma ga Allah, da sannu zai musanya maki da alkhairin da bakiyi tsammani ba, inkuma kika bijire wallahi iyakata dake addu’a, amma nikam ban isa in hana ubangiji yayi ikonsa akanki ba”

Salma ta k’ara sautin kukanta tace

“To ni yanzu umma, ya zanyi in daina son shi nikam?”

Umma tayi murmushi tace

“Salmata! Ki Yi imani da kaddara mai kyau, ko akasinta, insha Allahu da sannu zakiji kin daina sonshi, sai ki maye gurbinshi da Dr sadik, mai sonki a tsakani da Allah”

Salma tace “wallahi ni umma bantab’a sonshi ba fa”

Umma Tayi jimm na minti biyu sannan tace

“ki koyawa kanki son nashi, don kuwa kika yarda ya sub’uce maki, ko to wallahi kinyiwa kanki, don kuwa Dr yana sonki sosai, arayuwa ko da ki auri wanda kike so bayasonki, gwara ki auri wanda yakesonki baki sonshi, Allah dai yayi maku zab’i na alkhairi”

Salma tashare hawayenta tace “Ameen”

Dr sadik dake tsaye jikin a jikin k’ofa, yana saurarensu wannan doguwar muhawarar tasu, ya dafe kirji tareda zaro ido a waje tamkar idon mota, jiki asanyaye ya juya ya koma office d’inshi, wanda dama ya dawo ne don in ta k’are, ya k’ara saka mata kingin ruwan da suka rage, asamu su k’are kafin safiya, don son yayi a sallameta da safe, sai ya rik’a zuwa gida yana dubata, Ashe rabon yaji wannan bak’ar firar ne, duk da yake ba k’aramin burgeshi Umma tayi ba, don ya gano kwata kwata salma batayo halin ta ba, don Hafsa da ba itace ta haifo ta ba, har tafi salma biyo halin kirkin umma.

Yana tafe yana zancen zuci har ya had’u da wata nurse yace taje ta saka ma salma ruwa yana gama bata umurnin ya wuce, ita kanta nurse d’in tayi mamakin ganin Dr a cikin wannan yanayi, kasancewarshi mutum mai mutunci da sanyin hali,a cikin asibitin kowa ganin girmanshi sukeyi, saboda kirkinshi da tausayin da yake nunawa ga majinyata, da masu k’aramin k’arfi, mata da yawa yana burgesu, akwai da yawa masu sonshi, amma iya kacinshi da kowa mutunci.

Koda ya shiga office d’inshi ya zauna sai faman nazari yake akan yayi abunda ya dace ya k’udurta aranshi zai d’aukarwa kanshi matakin da ya dace, tunda dama salma tun farko ta fad’a mashi bata sonshi, shi dai ne ya nace, amma yanzu kam da ya iyarda aikinshi, da yayi niyyar Yi saboda Allah, to insha Allah zai shafawa kanshi lafiya, yayi nisa da salma, tunda dai har yanzu ba shi acikin zuciyarta, wani takeso, a cikin ranshi yace

“Dole ne kiso d’an gidan Bashir dala salma, don kuwa tabbas ya cancanci, mata suyi ta ribibi akanshi ,ga kyau, ga dukiya, kuma ga mutunci, yayi addu’a akan shima Allah ya bashi wadda yakeso take Sonshi.

 

 

Kazo zanbaka kanwata kaji Dr😒

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 18

Advertisement Page 18*   ********************** Salma tana fitowa, sukayi kicibis da umma,umma ta dubeta dakyau,taga duk ta hade…
Read More

TARTSATSI 23

Advertisement *Page 23*   ********************** Koda salma ta bud’a idon ta sai taga wayam ba Hafsa,ta tafiyarta bata…
Read More

TARTSATSI 86

Advertisement *Page 86*   **********************   Umma da Su Umaima, suna sashen Aunty amarya tareda su Gwaggo, da…