TARTSATSI 34

Advertisement

*Page 34*

 

********************

Abangaren Hafsa kuwa koda Asuba tayi taji sauk’in zazab’in da ya kafceta, a cikin dare, jiki ba wani kuzari ta tashi, bayan tayi sallah ta fad’a gyaran gidan, tareda d’ora masu abun karin da zasu ci har akai ma su umma dake asibiti, aikuwa usman da umar suka fito suma suna taimakata, koda karfe bakwai na safe tayi, sun kammala komi, tayiwa umar da autar umma wanka, usman da umar sukayi shirin makaranta, bayan duk sun karya,itama taje ta watsa ruwa tana sauri don kar Abba ya jirata, bayan kowa ya gyara ne, Abba ya fito suka gaidashi, suka d’auki kayan abincin da za’aje dashi asibitin suka Kai mota, duk suka shishiga suna jiran fitowar Abban, bayan Abba ya fito ne ya rufe gidan ya mik’awa Hafsa makullin, ya tada motar suka fara tafiya, makarantar su umar aka saukesu a bakin get Abba, ya basu kud’in taransu suka shige, Abba ya juya akalar motarshi zuwa asibiti, autar umma dake gefen Hafsa, azaune tace,

“Abba Nima baka bani, kud’in tara na ba”

Ta k’are maganar tareda son tayi kuka, daga Abba har Hafsa sukayi dariya, Abba ya ciro nera ashirin ya mika mata, tasa hannu tana karb’a, tana ta murna tace,

“Abba nagode, Allah ya kiyaye, ya kaika lafiya”

Dama ta saba kullum yabata kud’in tarar haka takeyimasa, duk da ba makarantar take zuwa ba, amma k’aida ne sai anbata Nata kud’in tarar, har su umar ma al’adarsu kenan,yana basu kud’in suke yimasa wannan addu’ar, Abba yaji dad’in addu’ar tata yana murmushi yace

“Ameen”

Hafsa itama tana dariya ta jawota a jikinta tace

Advertisements

“Toni nawa zaki bani a cikin kud’in”

Autar umma tayi dariya ta k’ara lafewa a jikin Hafsa, koda suka Kai asibiti har ta Fara kwana, ta yarda ashirin d’in da takewa rikicin sai anbata.

Hafsa ta d’auko ta fito da ita Abba yace tazo su tafi ya rik’a hannunta suka shiga cikin asibitin, ita kuwa Hafsa ta d’auko kayan abincin ta biyosu abaya, suna tafe har sukaje d’akin da aka kwantar da salmar, koda suka shiga, autar umma tana ganin umma, taje da gudu ta k’amk’ameta tana ta murnar ganinta,(Allah sarki uwa Mai dad’i, Allah ya k’ara muna tsawon rai mai albarka, mu rayu tareda ‘ya’yanmu Ameen).

Bayan duk an gaggaisa ne Abba yake tambayar jikin salma umma tace

“Ai inhar abun yabi haka to gsky Alhmdllh”

Ya dubi salmar yace “yajikin?”

Tace “Da sauk’i Abba”

Abba yace “To Allah ya bida lafiya”

Dukansu suka had’a baki sukace “ameen”

Abba ya Kalli umma yace

“Akwai abunda ake buk’ata? Don inason in wuce wurin aiki”

umma tace “bakomi gaskiya don nama ji ance, da ank’are saka mata ruwan za’a bamu sallama”

Advertisements

Abba yace “Masha Allah, to Allah ya bida lafiya duk yadda akayi zamuyi waya”

Ya ciro kud’i ya mik’awa umma, yayi masu sallama ya wuce, umma ta bishi domin ta rakashi,tana rik’e da hannun autar ta ,suka fita.

Hafsa kuwa dake gefen gadon salma, a zaune ta Kalli salmar tace

“Sannu aunty salma”

Salma ta Kai dubanta gareta tace

” yawwa” atak’aice

Hafsa bataji dad’in amsawar da tayimata ba, amma ta share kamar ba wata damu atareda ita Tana murmushi tace,

“Na d’auko maki wayarki, don kada mutane suyita nemanki ba’a jiki ba, Don dana koma naga tarin Miss call sai na kashe ta”

Hafsa ta k’are maganar, tareda saka hannu a cikin jakar ratayar da ta zo da ita, ta d’auko wayar ta mik’a mata jiki ba kwari salma tasa hannu ta karb’a, tana k’ok’arin kunnawa ne Hafsa ta fito da tata wayar, da sadauki ya bata, cikin dakewa tace,

“Nima ga tawa ki gani”

Jikin salma har rawa yake ta karb’i, wayar tana jujjuyata, don duk da ba wani sanin wayoyi tayi ba, daga ganin wagga kam tasan ta ninka tata sau goma, ta k’ara duban wayar tace

“Wow Hafsa wagga wayafa, tayi kyau sosai gaskiya ,waya saya maki ita?”

Ta k’are maganar tana k’ok’arin kunna power din wayar, aikuwa saiga photon sadauki ajikin screen d’in wayar, yayi masifar kyau, murmushi mai tsada shinfide akan kyakkyawar fuskarshi, ba k’arya fa sadauki ya had’u har ya gaji da had’uwa, salma ta k’ura mashi ido, nan take ta k’ara dulmiya a cikin kogin k’aunarshi, sai wani murmushi takeyi, tana shafar jikin wayar a hankali,
tamkar wata zautacciya,sai ga hawaye shar shar afuskarta, Hafsa tana ganin abun da ke faruwa, tayi saurin fisge wayarta, cikin fushi tace

“Miye haka aunty salma?”

Saboda azahirin gaskiya, taji mugun zafin abunda taga salma tayi,don dai haka kawai takejin wani masifaffen kishin sadauki yana fisgarta, Amman tayi sauri tayi control d’in kanta, tareda furta Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, a cikin zuciyarta, aikuwa nan take hankalinta ya dawo a jikinta, tace da salma

“Kukan fa na miye”

Salma ta share hawayenta tace “bakomi, don Allah d’an bani inga, pictures d’in dake wayar”

Hafsa tayi sororo tana yimata wani kallo, cen kuma ko me ta tuna, fuskarta d’auke da murmushi ta mik’a mata wayar, ai kuwa salma ta karb’a ta shiga gallery daman cen ba wasu photuna ne acikin wayar ba, kasancewarta sabuwa, sai photunan da sukayi ranar da ya bata wayar, aiko gasunan birjik salma ta fara kallo zuciyarta sai suya takeyi, tak’i kuma daina kallon har takai wurin wani wanda, sadauki ya dawo a bayan Hafsa ya tsaya, yayimasu selfie inba’a gabanka akayi pic d’inba, tabbas ba makawa zaka rantse, Da cewa rungumeta yayi sukayi photon, Ba shiri salma ta bud’a baki ta d’ad’a arnen kuka, ga kuma wayar a hannunta, ta kasa daina kallon photon, da sauri Hafsa ta karb’e wayarta, ta maidata a cikin jaka, ta wayance tace,

“Haba aunty salma, me kuma yayi zafi don Allah”

Salma ta bita da wani Mugun kallo tace

“Yanzu Hafsa ashe zaki iya cin amanata, ni zaki yaudara ko?”

Hafsa ta zaro ido waje tace “Amanar me naci taki?”

Salma ta d’an sassafta kukanta tace

“Ashe zaki iya karya alk’awalinda kikayimani, har ki zak’e kina cin dunduniya ta, abayan idona”

Hafsa tayi murmushi tace

“Alk’awalinki na cika,Allah shine she data, sai dai akasin da akasamu, ta b’angaren shi, saboda haka in baki mance ba, dama cen na gayamaki, in har bai amince ba, to zan zare wuyan hannuna, don haka ga wata dama, ta k’ara samuwa a gareki, yanzu kije na baki damarki a hannunki, ki shawo kanshi da kanki, in har ya amince dake, to wallahi wallahi zan bar maki shi na d’auki wannan alkawali,saboda haka dubara ta ragewa mai shiga rijiya”

Da sauri Hafsa ta nufi k’ofa zata fita, salma ta kira sunanta tace,

“Hafsa! Kar ki mance girman alk’awali fa”

Hafsa ta waigo tace

“Nasan da haka kuma a shirye nike, da in cika maki shi, matuk’ar yace yana sonki”

Salma tayi murmushi ta zare k’arin ruwan ta diro kan gadon ta rungume Hafsar akayi dai dai da shigowar umma tareda Dr yana ganinsu a haka yace

“A’a lalle maralafiya taji sauki, sallama kawai take jira”

Dukansu sukayi dariya, ana cikin haka saiga Aliyu da auwal suma Sun shigo, bayan angaisa ne, aka taru ana ta hira, Dr yaje ya kawo mata takardar sallamarta, amma da sharad’in ko a gida ne sai an k’arasa saka mata leda biyu, na ruwanta da suka rage ba’a sa ba, dukansu sai faman godiya suke yimashi, daman Abba kafin ya fita sun gaisa dashi, tareda yimashi godiya akan d’awainiyar da yayi tayi dasu, don umma ta fad’a masa komi da suka fito.

Umma ta sa salma dole ta karya, Aliyu ma ya sauko hannunshi hannun salmar, suna karin, acewarshi shima baiyi Karya ba, don azahirin gaskiya rabonshi da abincin tun jiya da dare, da aka fad’a masa batada lafiya, ya matsu safiya ta waye yazo yaga salmarsa, saiko gashi yayi farin gani tunda ya isketa taji sauk’i, harda sallama.
Bayan sunk’are ne
aka shiga tattara masu kayansu, ana ta lodawa a cikin motar Aliyu da sukazo da ita shida auwal.

Umma, Hafsa, da salma suka shiga baya suka zauna, autar umma tana rungume a jikin Hafsa, auwal ya shiga gaba Aliyu yaja motar.

Dr yana d’aga masu hannu har suka k’ule,aranshi yace

” Inda bansan komi ba salma, da tabbas dani za’a Yi wannan tafiyar, sai na kaiki har gida in dawo, amma yanzu kam Allah ya had’a kowa da rabonsa, zan koyawa kaina dangana”

ya juyawarshi, ya shige office d’inshi, yana tausayin kanshi.

*********

Su salma ko suna tafe ana ta hirar zumunci har suka Kai gida, bayan sunk’are kwasar kayan sun shige dasu cikin gida ne, umma ta Kalli su Aliyu tace

“waiku yau bazaku je, wajen aikin bane?”

Auwal yace “wallahi umma ba yanda banyi dashi ba, akan ya bari sai muntaso daga aiki, muzo muganta, yace ala dole sai munfara zuwa wurin salma”

kasancewar yanzu Aliyu ya koma a cikin gidanshi, da aka gina mashi, tareda auwal kusa da kusa, don yace bazai bari auwal ya shanye dad’in gidan badashi ba,

Umma tace “to kunzo ai kuje ku wuce wurin aikinku, mungode Allah ya bada lada”

Sukace “Ameen”

Aliyu yana Sosa Kai yace

“Umma da dai ya tafi Ni ya barni a nan”

Umma ta rike baki tace

“Anki a barka d’in ku wuce nace”

Suka fita sunata dariya auwal ya juyo yace

“Da na taso aiki umma, zan kawo Asma’u insha Allah”

Umma tace “Allah ya nufa”

Bada jimawa da fitarsu Auwal ba, aikuwa saiga gwaggo haja, nik’i nik’i da guzurin kulolin abincinta, tareda wata ‘yar aikinta, aiko umma da gwaggo sai faman murnar ganin juna sukeyi, gwaggo ta shiga har d’akin su salma ta dubata, tana murmushi ta Kalli Hafsa tace

“Yan biyun yaya, lalle wagga tagwaitaka taku tayi, wato don salma tana ciyo, shine
sai kema kika rame”

Dukansu sukayi murmushi, amma ita umma saida taji gabanta ya fad’i, don batason kowa yasan wannan abin kunyar da salma take so, ta tafka masu.

Ana cikin hira ne, sai ga sallamar aunty Amarya, tareda ‘yammatanta guda biyu, gida ya runtume sai murna ake tayi da firar yaushe gamo.

D’ai d’aikun ‘yan unguwar ma, sai shigowa sukeyi dubiya, gida dai kam masha Allah, sai hada hada ake tayi, da fatar samun sauki a wurin salma.

Salma ma hankalinta ya Fara kwantawa, saboda tana hangen nasara,a cikin yak’in neman zuciyar sadauki, da take shirin fafatawa.

 

Ba girin girin ba dai tayi mai🤒

 

Akafta🤸🏻♀

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 31

Advertisement *Page 31* ********************** Fad’uwar salma, yayi daidai da fitowar Hafsa daga gida, da gudu ta k’araso wurinta,…
KALLABI
Read More

KALLABI 1

Advertisement   (Yau Laraba/11/ ga watan Rabi’ul Auwal 1809. Karni na goma sha takwas) Da gudu Mahayi ya…
Read More

TARTSATSI 50

Advertisement *Page 50* ********************* Hafsa rik’e da hannun Salma har suka shiga d’akinsu, kowacensu kuka takeyi, bayan sun…
Read More

TARTSATSI 65

Advertisement   *Page 65*   **********************   Wani carpet ne ja aka shinfid’a mai d’auke sunan WELCOME TO…