TARTSATSI 35

Advertisement

*page 35*

********************

Umma da gwaggo haja da aunty amarya, sun k’ule falon na umma, sai hirar su ta manya suke yi.

Hafsa kuwa, da salma, da basma, da zainab, D’iyan aunty amarya da sukazo, suma suna cikin d’akin nasu salma sai baje hajar su, sukeyi tayi, tareda ture turen film film, da wak’ok’i da sukewa turawa junansu a waya, saiga sallamar yaya Auwal da yaya Aliyu, tareda Asma’u da raliya k’awar da salma tayi, a lokacin bikin su Asma’u, saboda tunda akayi bikin bata je gidan Asma’u ba, akayi dace zata zo, itama raliyar tace tana zuwa,taga k’awarta salma.

Gida ya k’ara cika, tubarkallah inda Allah ya agaza duk wad’anda suka zo tareda kulolin abincinsu nik’i nik’i suke zuwa, don kuwa ita gwaggo haja k’atta k’attan kuloli ta lodo abincin a cikinsu, don ita bata aza ansallamo su daga asibiti ba, sai da taje ne akecewa ansallamesu, kasancewar tasan daga umma har hafsar suna asibitin, shiyasa tasa aka dafa shi da yawa, don suci su k’oshi har dare.

Aunty amarya ma da kularta tazo, saiga Asma’u da nata girkin amare itama, gida ya hautsine sai kace gidan biki.

Shigowar Asma’u da raliya a d’akin na su salma, yasa d’akin ya k’ara runtumewa, sai murnar ganin juna suke tayi, muryoyin su a sama, sun cika gidan da hayaniya.

Yaya Aliyu ya lek’o da kanshi cikin d’akin yace

“waiku lafiyarku? kuke ta cika muna gida da kuwwa?”

Asma’u tayi murmushi tareda dafe bakinta tace

Advertisements

“Kodai kodai”

Yaya Aliyu yayi sauri ya shigewarshi d’akin umma,domin ya gaisa da su gwaggo, don Auwal har ya shige ya barshi, yana lek’en ta ina zaiga idon salma.

Suna shiga saiga Asma’u ta shigo Don itama ta gaida umma, saboda bata ma san gwaggo tazo ba, aiko tana ganin gwaggo da gudu taje ta rungumeta gwaggo ma da yake tayi kewar ‘yar tata itama sai farin cikin ganinta takeyi, Asma’u ta d’an zamo k’asa ta gaida umma tareda aunty amarya, sannan ta koma ta mak’ale gwaggo Aliyu ya kalleta yace

“Ke mage uwar son jiki tashi, ko bakisan yanzu kin girma ba?”

Asma’u tayi mashi gwalo tace

“Anji jeki waje dai, kayi zaman jira, zan kira maka ita ku gaisa, don naga kana buk’atar hakan.

Aliyu da sauri ya zaro ido yace

“Laa laa laa kuji yarinya”

Fuskarshi d’auke da mamakin, ya akayi ta ganoshi.

Asma’u tace “tun lokacin biki na ganoka ai”

Aliyu yana dariya yace “bukin wa halan”

Aiko kamar ansawa bakin ta kwad’d’o an dantse, tayi gum da bakinta,bata sake biyeshi shi ba, don tana gudun tayi abun da zai sa taji kunya, a gaban iyayenta,shi ko Aliyu ya samu hanya sai tsokanar ta yakeyi, su umma ko sai b dariyarsu suke tayi (Zumunci dadi) shidai Auwal baice k’ala ba, sai dariya yakeyi shima.

Advertisements

Ad’akin su salma kuwa hira ta kacame a tsakaninsu, idan hira tayi dadi sai dai kawai kaji sautin dariyar su, tareda shewa, (hmm taron mata).

lokacin sallah yayi, kowa yana ta k’ok’arin yaga ya sauke nauyi, ya huta, salma dai akayi dace tana fashin sallah, itama raliya haka nan suka b’uge da hira a tsakaninsu,raliya ta Kalli salma tace

“yade mutunniya ta, ciyon me ne kikeyi haka? har ya kaiki gadon asibiti, ya kwantar? Miye sirrin hajiyata?”

Salma tayi shiru na minti biyu, ta waiga taga duk abunda zasu fad’a dole ne su basma sai sunjisu ita kanta hafsar tana d’akin, da sauri ta tashi ta rik’o hannu Raliya tace

“Zo muje kijiya”

Sai da sukaje harabar get bakin k’ofar yaya Auwal sannan taja tunga suka tsaya salma tace

“Kinsan komi yana da sirri”

Raliya tace “Tabbas mutunniyata, kin kawo wuta”

Salma tayi ‘yar k’aramar dariya tace

“Ba dole ba, ai yanzu ingaya maki, jira kawai ake aji sirrin ka, a bazaka ga tire ayi ta tallar ka, lungu da sak’o, inda ma bakaje ba, ina tabbatar maki sai labarinka yakai, acikin duniya”

Raliya ta gyad’a Kai kawai, don ta matsu taji wannan sirrin, cikin zumud’i tace

“Haka ne mutunniya bani insha”

Salma ta sauke wata nannauyar, ajiyar zuciya tace,

“Ina wannan Gay d’in da muka gani, a wurin dinner?”

Raliya tayi saurin d’aga kai tace “Eh D’an gidan Bashir Dala”

Salma ta k’ara sauke ajiyar zuciya tace

“shifa, to tun daga ranar zuciyata, bata koma natsuwa ba, har zuwa yau, ke k’arshen zancen dai ingaya maki, akan shi ne nayi wannan jinyar, da taso kaini barzahu ba tareda na shirya ba”

Raliya ta zaro ido tace “Garin yaya haka ta faru”

“Salma tace Bari kawai Kedai, ina ta dakon son shi, bansan ya akayi ba, wai ashe shi kuma, Hafsa yake so”

Raliya ta aza hannu Akai tace

“See na wee come”

Salma tayi dariya tace

“yanzu dai in tak’aice maki labari,munyi da Hafsa akan, ta bani dama inhar na sato zuciyarshi,to tabbas zata hak’ura, ta barman shi”

Raliya tace yi wani zullo tace “ta kwana gidan sauk’i, Don kuwa wallahi kika samu Gay d’in nan ko, hmm gaba ki d’aya familyn ku, kakar ku ta yanke sak’a, don Kuwa kuda talauci kunyi hannun riga, har abada baku ba talauci, Don kuwa Sadauki ya mallaki, mahaukaciyar dukiya, wadda in a titsiye shi shi kanshi bazai kawo adadinta ba”

Salma tayi wani tsalle tace

“wow biri yayi kama, da mutum, to yanzu miye Mafita k’awata, ga dama fa ta samu a hannu”

Raliya ta shiga zurfin tunani tace

“mafita guda d’aya ce, ina da wani malami da yake yiman aiki sha yanzu magani yanzu, in har zaki amince Muje wurinshi, to keko ina tabbatar maki da cewa, kamar anyi aurenki da sadauki angama”

Salma ta zaro ido waje tace

“Boka ko malami”

Raliya tace “duka biyu”

Salma ta dafe k’irji tace

“Na shiga uku anfasa aurena”

Raliya tace “ba fa wani abu bane ba, zakiyi maganin matsalarki ne, in kuma kinga bazaki iya ba, to kawai ki hak’ura, kibar hafsa da masoyinta, suyi aure, ke kuma ki zamo ‘yar lasar miya gidan masu kud’i”

Salma ta Kai mata duka tace “To muguwa banji bakinki ba”

“Raliya tace “Ahtoh bake bace, ana azaki akan hanya kina kaucewa?”

Salma tace

“ki zama serious Don Allah, yanzu kina nufin dole ne sai naje,? nifa wallahi tsoron zuwa irin wajajen nan nikeyi, indai zakiyi man alfarmar kije kawai, ni basai naje ba Shikenan, don saboda umma baza barni infita nikad’ai ba,ba tareda Hafsa ba gaskiya, kinkoga shirin mu ne zai wargaje”

Raliya tace “bakomi ki tanadi kud’i kawai”

Salma ta zaro ido waje tace

“An yanka ta tashi Raliya, don kuwa ni ba wata sana’a nikeyi ba, bale in samu k’udin kaiwa”

Raliya tace “yanzu ke ko ‘yan k’ananun samarin nan, da suke d’an bada ‘yan kud’i, ke ba Mai baki?”

Salma tayi dariya tace

“Ba sai in na kulasu ne zasu bani ba, ke nifa wallahi kallon banza ma basu isheni ba”

Raliya tace “cab da sauranki, amma dai kam Kiri k’ok’ari, ki samo wani Abun gaskiya, don aiki ba yayi sai da kud’i”

Salma tace “OK zan duba ingani”

Raliya tayi dariya tace

“yayi Mrs sadauki, don nifa tun yanzu, zan Fara girmamaki, don in har abun ya tabbata kinsha kwana hajiyata”

Salma sai jinta takeyi wata shegiya, kanta ya k’ara yin sama, sai faman murmushi takeyi, tana hangota kanta a matsayin, wata Big madam d’in nan, Raliya ta lak’amo Salma ta saita bakinta a kunne ta tace

“Daman irinku kyawawa, su sadauki ne dai daiku, da kun saka su a kwana Shikenan, ko sunan uwarsu mantawa zasuyi, ballantana na wani”

salma tayi ta kwashe da dariya tace

“K’awata bakida dama”

Hafsa dake fitowa cikin gida ta kallesu sau d’aya ta d’auke Kai tana kallon wani gefe tace da salma

“In kun k’are shawarar, to kije umma tana nemanki, in kuma baku gama ba to ku k’arasa, nasan ta yanda zanyi, in kareki wajen ta, don na fahimci maganar taku mai muhimmanci ce”

Hafsa tana k’are fad’in maganar ta, ta yiwa Raliya wani Mugun kallo, ta juya abinta ta koma cikin gida.

Raliya nan take tasha jinin jikinta, alamun rashin gaskiya duk suka bayyana a kan fuskarta, jikinta yana rawa tace da salma,

“Anya wannan hafsar, bata Ji hirar mu ba kuwa?”

Don ta kwantar mata da hankali tace

“Bata ji ba gaskiya, kinsan daman cen jininku, bai had’u ba shiyasa kika ga tayi maki haka”

Raliya ta ciro Wayar ta a cikin jaka tace

“Bani number ki zamuyi waya”

Salma ta fad’a mata tayi saving,bakinta yana rawa tace da salma

“In Asm’au ta tambaye ni kice mata na wuce”

A cikin sauri ta nufi k’ofar get tana tafiya tana k’ok’arin saka wayarta jaka wajen rawar jikin ta fita ma saida wayar ta fad’i ta duk’a ta d’auka da ta fita kamar wadda zata tashi sama saboda sauri, (Marar gaskiya ko acikin ruwa yayi jib’i).

Salma ta bita da kallo har ta fita, sannan Itama ta fara tafiya zata shiga cikin gidan, a cikin ranta tace,

“kwab’a ta tayi ruwa, don kuwa tabbas, Hafsa ta ji hirar mu”

A b’angaren umma kuwa tun da ta dawo bata shiga kuryar d’akin nata ba,kasancewar hirar da ta d’auke mata hankali, ko su gwaggo duk toilet d’in waje sukayi amfani dashi, sukayi arwallah, sallah ma anan falo sukayita, umma ta shiga k’uryar d’akin don ta ajiye wasu kaya, ai kuwa sai taci karo da tsibin tulin kayan da sadauki ya kawo, da sauri umma tayo falo, jikinta yana ta rawa, bata ce da kowa komi ba Tayi waje da saurin ta, taja tunga a abakin k’ofar Abba ta tsaya, ta reda dafe k’irjin ta, da yake ta bugawa, da sauri da sauri, akayi dai dai Hafsa ta fito da kulolin, da Asm’au ta kawo na abinci, zata Kai su cen d’akin na umma, karaf idonta suka Kai kan umma, dake dafe da kirji, cikin sauri ta ajiye kulolin, ta yi wurin umma, ta rik’o hannunta tace,

“Umma lafiya? Meke damunki?”

Umma ta Kalli Hafsa, fuskarta d’auke da tsoro tace,

“kaya na gani, acikin d’akina, kinsan dasu?”

Hafsa nan take, wata dariya ta sub’uce mata, da sauri ta dafe bakinta tace ,

“Ummata wallahi ke na biyo, nifa har zazzab’in wahala niyyi fa, da niggansu”

Umma kalleta dakyau tace

“Daga wace nahiya suka fito ne? Allah yasa ba aljanu, suka kawo muna su, suka ajiye muna ba”

Hafsa ta k’ara kyalkyalewa da dariya tace

“Umma kwantar da hankalinki, mutane ne suka kawo su, asalima su usman ne suka shigar dasu har cikin d’akin”

Umma ta k’ara zaro ido waje kafin tayi magana Hafsa tarigata da cewa

“Bak’on da yazo wurina ne jiya, bayan mun tafi asibiti ya dawo, ya kawo kayan”

Umma ta sauke ajiyar zuciya tace

“Hafsa wannan yaro yayi b’arna da yawa gaskiya, kinga yanda naga kayan sun cika d’akina fa, har saman gado sune”

Hafsa ta kara fashewa da dariya tace

“Wallahi umma, idanun ki ne, suka bude, amma basu Kai saman gado ba kam”

Hafsa ta k’ara fashewa da dariya tace

“Allah ya rabamu da ganin abun tsoro umma, don kuwa ni da ke bansan Mai tada wani ba wallahi”

Hafsa dariya harda su hawaye, gwaggo taji dariyar tayi yawa ta fito tace

“Yaya lafiya keda ‘yar taki”

Umma Tana dariyar tace da gwaggo

“Zo muje, kema muga taki jarumta”

Hafsa tana dariya taje ta d’auki kulolin ta Kai d’akin na umma ta ajiye ta fito, umma tace da aunty amarya, itama ta zo ta gani, gwaggo da ita suka wuce k’uryar d’akin, Aunty ma ta bisu a baya.

 

Lol😝

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 8

Advertisement Babi Na Bakwai>* *Godiya da fatan alkhairi son so daga Mai Daraja😍🔥* Barka da Juma’a# Masarautar Gobir.…
Read More

Lu’u Lu’u 45

Advertisement _Bismillahir rahamanir rahim_ *45*   Tattausan kayan bacci ya d’auko mata dogon wando da rigarshi mai k’ananan…
Read More

TARTSATSI 75

Advertisement *Page 75*   *********************   Alhaji acikin b’acin ran da ya bayyana, akan fuskarshi k’arara yace:  …
Read More

TARTSATSI 49

Advertisement *Page 49* ******************** Atare Abba da Aliyu suka shiga cikin gidan suna shiga Umma ta tarbe su…
Read More

TARTSATSI 71

Advertisement *Page 71*   **********************   Aliyu bai tsaya iya marin ba, cikin fushi ya cire belt d’inshi…
KALLABI
Read More

KALLABI 16

Advertisement BABI NA SHA SHIDA D’ago fararen idanun ta, tayi tana kallon shi cikin sanyin jiki, a hankali…