TARTSATSI 87

Advertisement

Page 87*

 

******************

 

Sadiya taci gaba da kwalliyarta, da feshe feshen turarenta, dangwala anan murza anan har ta k’are tazo ta zauna agefen gado tana chatt har sha biyun dare, sannan ta duba agogo kirjinta ya buga dam!  dam!, tace:

 

“Kutumelesi shi wannan angon, wai me yake nufi ne?, da bai dawo gida ba har yanzu?”

 

Ta ajiye wayar ta tsam ta fito, tana dube dube abun mamaki koda ta taje bakin k’ofar shigowa agidan taga anrufe da makulli, saboda ta jawo ta jawo taji k’ofar gam ta tabbatar wa kanta Aliyu ne ya rufe ta, ta d’aga labulen window ta lek’a ta hango motarshi ajiye, ai kuwa nan take wani b’acin rai ya ziyarceta aranta tana mamakin faruwar hakan, sannan da tambayar kanta, wannan abun da yayi me hakan ke nufi?, wata zuciyarta tace:

 

Advertisements

“Watak’il kacaniyar biki ce tasaka shi gajiya shiyasa bai nemeki ba” , wata zuciyar tace:.”idan ko har ya barni da wannan abun da ke damuna bansan ya zanyi ba”.

 

Da saurinta ta nufi d’akinshi ta fara bubbugawa, tana kiran sunanshi, yana kwance wani bacci Mai k’arfi ya sace shi, acikin baccin ne yajiyo k’wank’wasar, firgigit ya tashi yana jiyo sautin muryar ta tana kiran sunanshi ya yaje ya bud’e k’ofar, yayi tsaye abakin k’ofar ya kalleta sama da k’asa yace:

 

“Lafiya ina bacci na zaki tada ni?”

 

Sadiya ta fara inda inda tace:

 

“Naji shiru ne shiyasa nazo nagani ko lafiya, sai naga Ashe ma har ka dawo”

 

Aliyu ya tsura mata ido sosai, yana kallon ta yace:

 

Advertisements

 

“To ya ai yanzu kinga na dawo ko?, kuma lafiya to kije ki kwanta kiyi bacci, sai da safenmu”

 

Yana k’ok’arin rufe k’ofar tayi saurin cewa:

 

“Ni bana jin bacci ai”

 

Aliyu ya d’age gira alamun renin wayo yace:

 

“To me kikeso ayi ne yanzu”

 

Sadiya ta harereshi tace:

 

“Idan har baka sani ba Shikenan”

 

Ta fara tafiya zata shige d’akinta, sai juya mazaunai takeyi, har ta shige d’akinta, ya bita da kallo, aranshi taso ta rufta shi, amma ya waske ya shigewar shi ya banko k’ofar, Ya fad’a kan gado ya shiga nazari.

 

Itakam tana shiga ta fashe da kuka tace:

 

“Yau nashiga Uku ni Sady, idan har wannan mutumen yayi man haka, to tabbas ba makawa wallahi ya zalunceni”

 

Aikuwa sai gata da yin safa da marwa, saboda tayi ta d’irkawa kanta kayan mata na gargajiyar dana asibitin, har da na bokaye duk tayi amfani dasu, domin tanadi ga wannan r rana sai gashi yana so ya kwafsa mata.

 

Da abun yayi tsamari sai gata da dafe marar ta tana murk’ususu, da taga zata cuci kanta idan har ta zauna, ta tashi ta koma tana ta bubbuga k’ofar shi da k’arfi tana kuka kashirb’an, zuwa lokacin shikam idonshi biyu ya k’are sallah yana jero addu’o’i ne yaji bugun k’ofar amma yayi banza da ita, da yaga zata dameshi ma ya tashi ya d’auko wayar shi yasaka earpiece yana sauraron karatun ALQUR’ANI, Sadiya kam bata hak’ura ba haka ta canye rabin dare da dukan k’ofa har sai da tagaji sannan ta jingina  anan jikin k’ofar, tana ajiyar zuciya har bacci ya sace ta.

 

***

 

Asma’u da Aunty Umaima koda suka koma gida, sukayita baiwa Salma labarin tartsatsin da suka gano yau,  sai jimamin abun sukeyi Salma dai tana sauraronsu bata ce dasu k’anzil ba, Aunty Umaima tace:

 

“Wallahi Salma ki godewa Allah, domin ya fara saka maki tun kafin aje ko’ina, don uk’ubar da su Karima zasu fuskanta, ke sai kince ba’a yimaki komi ba,don wannan gogaggiyar ‘yar duniya kishiyar Karima idonta atsaye suke, koshi mijin nasu bata ganin girma shi,kin koga komi zata iya yi kanta atsaye,bata shayin komi”

 

Asma’u ta sauke ajiyar zuciya tace:

 

“Nifa Aunty nafi jin wannan tsukakkiyar tsohuwar mai tab’in jinnu, don wallahi Maryam sai tasha wuya ba kad’an ba, saboda wannan masifaffiyar tsohuwar ko idonta kika kalla zaki hango ruwan masifar dake tattare da ita, Kai ina ai nikam wannan tsohuwa tsoro ma take bani”

 

Salma da Aunty Umaima suka kwashe da dariya, Salma tana dariya tace:

 

“Matsoraciya”

 

Asma’u tana dariya tace:

 

“Tsoro kam ai dole ne ke don baki ganta bane shiyasa”

 

Daga nan suka ci gaba da firarsu suna ta dariya ,Salma tayi ta kasa kunne taji antab’o labarin Matar Aliyu amma taji shiru, kamar ta tambayesu, sai kuma ta share amman dai kam azuciyarta taso taji d’an wani abu dangane da matar.

 

Suna gidan har dare sannan Mustapha yazo ya d’auki Umaima, Asma’u ma Auwal yazo da sabon mashin d’in shi da ya saye roba roba ya d’auke ta, suka tafi.

 

***

 

Hajiya zulai ma labari ya isa wurinta irin abunda akayi agidan auren d’iyanta, aikuwa ta fara zuba ruwan masifa, har zanen yana k’ok’arin fad’uwa tana taroshi, taja gyale wai zataje gidajen ayi wadda za’ayi, k’awayenta suka rirrik’eta suna bata hak’uri.

 

Jikinta har rawa yakeyi ta shige toilet, ta kira bokanta cikin tashin hankali, ta sanar dashi abunda yake faruwa, yace da ita tasha kuruminta ankawo masa labarin komi, me takeso bakinta yana kumfa tace:

 

“Ita wannan tsotsatsiyar tsohuwar ak’ara mata gudu kawai kowa ya huta, itako wannan ‘yar iskar Don ubanta, ayimata kurciya tabar gidan tabi duniya kowa ya manta da labarinta”

 

Tsidudu yace ta kwantar da habkalinta yanzu zai fara aiki akansu, duk abunda akayi zai kirata, amma ta turo masa kud’i account d’inshi yanzu, Hajiya jikin ta yana rawa tace:

 

“Indai kud’i ne bakada matsalarsu Kai kanka kasani ka fara aiki kawai yanzu zakaji alert, nidai gurina abar man yarana suji dad’in zaman auren su, duk wanda yace zai kawo masu cikas niko bazanyi sanya wajen ganin Bayan mutum ba”

 

Bokan ya tabbatar mata da yanzu, zai fara aika masu da makaman nuclear, hajiya taji dad’i acikin farin ciki tace:

 

“Ai nasanka bakada sanya mutumina rauhanai su taimakeka”

 

Sannan sukayi sallama hankali akwance ta fito, tana ci gaba da hada hadar ta, kamar ba itace tayi haukar da tayi ba, mutane sai mamaki sukeyi, ganin yanda ta canza lokaci d’aya.

 

Itakam dalilin ta shine ta riga da tayi imani da cewa boka aikinsa zaiyi kyau, saboda kasancewar shi mai aiki da cikawa, (Hmmm).

 

***

 

Tsuntsayen soyayya, Hafsa da Sadauki, sun sauka gida Lafiya, mummy farin ciki har kunne ga ‘yarta ta dawo ganin yanda tsukayi kyau dukansu su biyun suka yi ‘yar k’iba ta samun hutu da kwanciyar hankali, Zakiyya sai tsokanar su takeyi tana cewa:

“daman sun jira an aiko masu da kayansu kawai suyi zamansu acen, tunda basu so dawowa ba”.

 

Mummy tayi mata dak’uwa tace:

 

“Bacin nan kike damun mutane da su dawo, har da d’an kukan ki sannan yanzu kice, to ai taimakon ki ma sukayi, da har suka dawo”

 

Duka falon akayi dariya, bayan sunci sunsha, sunyi k’at Hafsa ta kwanta tana son tayi baccin da ya zamo mata ibada, Mummy tace da ita:

 

“Taje gidanta tayi wanka, ta kwanta ta huta acen, don kada adameta anan”

 

Zakiyya ta zunb’uro baki tace:

 

“Aiko dani zataje don nima fa banison adameni tunda ‘yar haka ce”

 

Sadauki yana dariya yace:

 

“Ai Mummy idan har wannan yarinyar tana awuri idanunta rufewa sukeyi da ganin kowa sai ita, nima fa agaskiya na fara gajiya, Shikenan daga zuwanta ta k’wace mani power”

 

Mummy ta kallesu tayi murmushi tace:

 

“kwaji da tsugudidinku nidai ‘yata kawai na sani”

 

Hafsa dai sai gyangyd’i takeyi suna mata dariya, mummy ta rik’a ta takaita har sama d’akinta, ta kwanta, ta jawo mata k’ofa ta dawo suka ci gaba da firar su, suna tsokanar Hafsar mummy tana tarewa.

 

****

Karima kam duk d’okin miji akanta ranar kwanan bak’in ciki yayi domin ya risketa sab’anin yanda yayi tsammani, tun adaren ya dinga bata kashi sai da ya tabbatar ta lallasu dakyau sannan ya shak’e ta yace:

 

“Ubanwa kika bari yayi maki, wannan wawakakken rame har haka?”

 

Karima tana kuka tana bashi hak’uri, duk yanda yayi ta gana mata azaba akan ta fad’i amma ina, saboda taurin Kai irin nata, acikin fushi yace da ita:

 

“Wallahi bazan sake ki ayanzu ba, Amman ki sani sai kin gwammace zaman gidanku akan zama wannan gidan nawa, don daga yau duk wani aikin gidan kece zakiyi shi, da girkin ki da ba girkin ki ba, sannan lefe na wallahi ko tsinke bazan bar maki ba, kwashe abuna zanyi in darzo sabuwar Amaryata, mai rufaffen wurin hutawa, ba irinki ba, wadda ko wutsiyar maza biyaraka had’e awurin sai anbar sauran fili, cab wallahi da sake da nasan haka kike Allah na tuba mezanyi dake, Uwar gidana ma Mai haifuwa shidda, tafiki muhallin k’warai”

 

Karima taso zata yimasa rashin kunya, ya k’ara jibgar abun banza, sannan ya sakata agaba suka fita ya kaita har wurin tsibin kayan wanke wanke da akayi hidimar biki dasu,yace ta duk’a ta fara wankesu, idan ta k’are zai kaita wurin sauran ayukkan da zatayi, da yaga zata kawo masa taurin Kai yaje d’akinshi ya d’auko bulalar shi Mai halshe biyu, ya fara watsa mata d’aya, tanajin zafin dukan ta fara wanke wanke jikinta yana kyarma.

 

Agefe d’aya kuma ‘ya’yan shi da matar shi ta biyu sai dariya suke yimata, matar Mai suna jimmai ta k’araso har inda take wanke wanken tace:

 

“Sannu da zuwa gidan ‘yanci, domon a dukkan alamu sun nuna abud’e aka iskeki, shiyasa tun da safe kika fara da karb’ar tukwicinki, Kai gaskiya kinyi jarumta, koda yake dai ma akwai irinki da yawa masu baje hajar su atiti ana siye, su koma gida suna yiwa iyaye kallon hadarin kaji, tunda anriga an san komi, oni jimmai wannan amarya Kinzo da goshi”

 

Ta k’are maganar tareda b’allewa da wata mahaukaciyar dariya, acikin dariyar ta dubi yaran dake tsaye suna dariyar suma tace:

 

“Ku taimaketa ku tattaro mata sauran kayan kada Amarya tasha jibgar banza”

 

Aikuwa lungu da sak’o duk inda kwanoni suke sai da suka kwaso suka jibge mata, Karima kam tana kuka tana wanke wanke, saboda jin zafin maganganun da jimmai take yimata, da abun ya isheta tayi tsam tayi ciki da jimmai suka fara kokuwa, da yake k’arfi ba d’aya ba, aiko jimmai ta d’auki abur banza ta kada ta acikin kwanonin wanke wanken, saiga Karima tsamo tsamo da cakalin kingi kingin abincin da aka raga, aiko yaran me zasuyi ba dariya ba, wasu harda Kai kwance awurin dariya, wani daga cikin yaran yace:

 

“Ke amaryar babanmu ashe bakida k’arfi”

 

Aiko dukansu har da jimmai suka dinga tik’ar dariya, sai da Uwargidan shi ta fito ta kora yaran, amma itama ganin Karima atsakiyar kayan wanke wanke jikinta duk guntu guntun abinci, sai da ta dara, amman bata tsaya ba ta shigewarta d’aki, ana haka saiga Mukhtar ya fito da zungureriyar bulalarshi, tana hangoshi  tayi saurin tashi ta ci gaba da wanke wankenta, tana sharar hawaye.

 

🤣🤣🤣🤣🤣jar Uba

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 17

Advertisement €pisode 17…………….. Garin Zawatu ya cika dam da mutane . Kowa ka gani yayi kyau sosai cikin…
Read More

TARTSATSI 90

Advertisement   *Page 90*   **********************   Hajiya zulai tana k’are sambatun nata, dannawa kulsum kira awaya, jiki…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 7

Advertisement €pisode 7……………………. Da ƙarfin tsiya NAHEELA ta cira sama ta saki fuka-fukanta, sai da tayi sama sosai,…