TARTSATSI 88

Advertisement

*Page 88*

 

********************

 

Ab’angaren maryam kuwa, su Gwaggo suna fita tsohuwar tayi mata wani kallon renin wayo tace:

 

“Ai da kin bisu kunyi gida, yafi wannan kukan da kikeyi, tunda har zaman gidan naku bai isheki ba, in bancin Abbbakar da naci irin nashi me ma zaiyi dake, aike ba sa’ar auren shi bace, ga mata agari birjik, duk ya rasa matar da zai aura sai ke, to wallahi idona akanku zai k’are don bazan yarda ki tsofar man da yaro ba, shikad’ai ne gareni wallahi haka kawai bazan zura ido ina kallo ba, ki kassara man shi”

 

Tana k’are maganar ta d’auki buta tayi makewayi, har ta shige maryam tana binta da kallo baki asake,  don mamakin maganganun tsohuwar, tana nan atsaye dafe da kumatun ta tana fassara maganganun tsohuwar, har taji bud’ewar k’ofar bayin zata fitowa, da sauri ta shige d’akinta tayi zaune tana ta karanta wasik’ar jaki, har aka kira sallah’r Mag’rib, ta fita ta d’oro arwallah don batada toilet ad’aki sai na wajen Shikenan kuma d’aya agidan, akayi dace tsohuwar ta k’are arwallar ta shige d’akinta, duba da talkamin ta dake ajiye ak’ofar d’akin, da suke d’auke da danshin ruwa.

 

Advertisements

Abbakar bai dawo ba har k’arfe tara, abokan shi suka rako shi har d’akin ta, sukayi masu addu’o’in zaman lafiya, sannan d’aya daga cikin abokan ya ajiye ledar da ya shigo da ita, sannan sukayi masu sallama suka fita.

 

Suna fita Abbakar ya jawo ledar ya bud’e yana k’ok’arin ware d’aya ledar dake ciki saiga tsohuwa ta d’age labule tana k’are masu kallo ahankali har idanunta suka sauka akan ledar dake hannun Abbakar, aiko acikin Hanzari ta  k’araso cikin d’akin, ta rik’e k’ugu tana yi masu wani kallo tace:

 

“Lalle Abu yanzu daga yin aurenka yau yau,  zaka fara cin amanata”

 

Abbakar ya daburce, jikinshi yana rawa yace:

 

“A’a Inna daman cen yanzu nike shirin Kai maki naki kaso kin ma ganshi”

 

Ya k’are maganar tareda fiddo d’ayar ledar ya nuna mata, Inna kam ta zuro hannu ta kwashe ledodin, ta fara tafiya tana cewa:

 

Advertisements

“Kazo ina nemanka”

 

Abbakar tsam yayi yabiyo bayanta, suka bar maryam da tagumi, domin izuwa lokacin har ta fara sarewa da auren shi, nan take wasu hawaye suka zubo mata sharr sharr akan fuskarta, ta saka hannu ta share, sannan ta d’an gincira tana tunanin itakam karima tana cen hankalinta akwance, ita kad’ai aka bari da tashin hankali.

 

Inna tana gaba Abbakar yana bayanta har d’akinta, ta bashi umurnin ya zauna, ba musu ya samu wuri ya zauna, taje ta dauko tire ta juye kazar dake cikin d’ayar ledar wadda tafi girma, sannan ta saka hannu ta d’auko wata tsoka ta guma abakinta, yana abakinta tana taunawa tace dashi:

 

“Saka hannun ka muci”

 

Abbakar ya kalleta yayi murmushi yace:

 

“Inna kar fa ki sark’e, kici ahankali”

 

Inna ta d’aga Kai, saboda dad’in naman yasa ko magana bata iya yi, sai aunawa bakinta takeyi tana kad’a kai, shima ya saka hannu suka fara ci, suna fira basu tantance ba, har suka tada tiren, sannan Inna taje ta kawo masa ruwa yasha, sannan ta tsiro masa da fira kala kala, har saida dare yaja sosai, sannan Abbakar ya duba agogon hannun shi yace da ita:

 

“Inna bari in shige ashe dare yaja”

 

Inna ta b’ata fuska tace:

 

“To kadaiyi ahankali kar taje ta tsetse ka, ka kasa mamora, don na hango idanunta atsaye suke da jaraba”

 

Abbakar ya Sosa k’eya yana yimata sai da safe, har ya fara tafiya ya dawo baya yace da ita:

 

“Inna ki kawo nata in kaimata”

 

Inna ta d’auke ledar ta tashi, taje ta bud’a wata kula ta jefa tace dashi:

 

“Sai da safenka Allah ya tashemu lafiya, idan har ran mu yakai zan d’umama shi sai kaci kafin ka fita”

 

Abbakar yayi shiru, sannan ya juya ya fara tafiya, Inna ta bishi da harara tace:

 

“So kakeyi in bari ka zama sallamamme ne, to wallahi da sake bazata tab’a sab’uwa ba”

 

Koda ya shiga bai ganta afalo ba, Kai tsaye ya wuce k’uryar d’aki ya sameta tana ta sharar bacci, ya durk’uso yayi mata kiss, sannan ya tada ita, ta tashi zaune acikin magagin baccin tace:

 

“Ina naman?”

 

Abbakar yayi tsuru tsuru, yasha jinin jikin shi, sannan ya basar yace:

 

Tashi kiyo arwallah muyi sallah, Maryam tana gunguni ta sauko ta fito tayi arwallah sannan ta koma d’aki, Inna tana kallonta acikin duhu tayi k’wafa.

 

Bayan sun k’are sallah’r ne, labari ya fara shan bam bam, domin kuwa har yayi nisa da son ya raya sunnah saiga k’wank’wasar k’ofar d’akin su anayi, acikin tsoro dukansu suka razana, Abbakar ya kimtsa jikinshi ya k’araso ajikin k’ofar yana tambayar wanene, acen bakin k’ofar Inna tace:

 

“Nice Abu nakasa kwana cikina sai ciyo yakeyi”

 

Da sauri Abbakar ya bud’e d’akin saiga inna tana dafe da ciki tana murk’ususu, acikin tashin hankali ya rik’ata suka yi d’akinta, yaje acikin tsohuwar ajiyar komatsan shi ya samo palajin ya b’allo biyu ya bata da ruwa tasha, sannan ya lallab’ata ta kwanta, har bacci ya fara d’aukarta, sannan ya lallab’a ya fito ya fad’a d’akinsu ya rufe ya koma bakin aikin shi, Maryam dai saboda takaici kasa tab’uka komi tayi yana gaf da samun cikar burinshi, Inna ta sake k’wank’wasa k’ofar tana kuka tana kiran sunan shi, ba shiri ya mik’e ya ya saka doguwar riga ya fita, koda yaje Inna tana k’ofar d’akin kwance tana malalowa dafe da cikinta, Abbakar ya k’arasa da sauri yace:

 

Har yanzu cikin bai daina ba Inna sannu kinji sannu tashi Muje d’akin ki, ki kwanta, Inna acikin muryar tausayi tace:

 

“Kaini d’akin ku in kwanta acen,kada ta Allah ta cika dani ba kowa akusa dani”

 

Abbakar ya zaro ido awaje yana shirin yin magana Inna ta k’walla wata k’ara da hanzari ya rik’ota ya kaita falon su, ya kwantar da ita akan doguwar kujera, shima ya zauna yana yimata sannu, aiko Inna tana jin laushin kujera ta fara nasari, Abbakar dai azaune ya kwana yana gadin Inna, yayin da Maryam dake k’uryar d’aki take acikin bak’in ciki, zuciyar ta kamar tayi bindige, saboda tsananin takaicin Inna.

 

 

 

 

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
INAYAH
Read More

INAYAH 1

Advertisement amuhgee_ Document queen meenali 1 _*please masu daukamun Sunayen books da Labarai suna sauyawa suyi nasu lamarin…
Read More

TARTSATSI 52

Advertisement *Page 52* ********************** Da gudu usman yazo kan Umma, yana girgizata tareda kiran sunanta, amma ina Umma…
KALLABI
Read More

KALLABI 54

Advertisement BABI NA HAMSIN DA HUƊU *Ina matan Alfarmar ga maman ZEEY me kayan mata tazo muku da…
INAYAH
Read More

INAYAH 19

Advertisement 19_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Breakfast sukayi na Lafiyayyan abincin da rabon umma yaganah dataci sa harta manta, Soyayyar doya…