TARTSATSI 89

Advertisement

*Page 89*

 

*******************

 

Amarya sadiya ma sanyin asuba ne yasakata dunk’ulewa wuri d’aya, tana rawar sanyi, Aliyu ya bud’e kofa zai fito yaje masallaci yaci Karo da ita abakin k’ofa, da sauri ya furta:

 

“Subhanallah”

 

Saboda ta bashi tausayi, ahankali ya fara tadda ta, har ta bud’e idonta akanshi, zumbur ta mik’e ta cakumoshi da k’arfi tace:

 

Advertisements

“Wallahi bazan sakeka ba har sai kabani hak’k’i na”

 

Ta k’are maganar tareda murgud’a baki, ta bashi dariya sosai amma ya danne yace da ita:

 

“Sakarni masallaci zanje inyi sallah”

 

Sadiya ta k’ara k’arfin rik’on nashi tace:

 

“Ba inda zakaje sai ka bani hak’k’i, duk wulak’ancin da kayiman jiya baka gani ba”

 

Aliyu ya fisge rik’on da tayi masa ya fara tafiya, zai je ya bud’e k’ofa da sauri tasha gaban shi tace:

 

Advertisements

“Bafa inda zakaje, sai dai ayi wadda za’ayi”

 

Aliyu ya kalleta sama da k’asa nan take wani b’acin rai ya ziyarceshi da hanzarinshi ya bangaje ta ta fad’i ya bud’e gidan ya fitawarshi.

 

Sadiya ta bishi da kallo tareda dafe kunkurunta tace:

 

“Mugun banza”

 

Sannan ta lallab’a ta shige d’aki tana k’ananun maganganu marar sauti.

 

Sai da haske yayi shaa sannan ya dawo, yana shigowa k’amshin break fast d’in da take had’awa yana bugun hancin shi, tana fitowa kitchen ta hango shi, ta k’araso acikin ladabi tana yimasa ina kwana, shima acikin sakin fuska ya amsa kamar ba abunda ke tsakaninsu, ta rik’o hannun shi ta zaunar dashi kan kujera tace:

 

“Zauna anan nakusa k’arasawa sai muyi breakfast”

 

Aliyu yayi murmushi baice da ita komi ba, yana nan zaune har ta k’are sai rawar jiki takeyi da shi, tun daga yanayinta da ya gani yasan akwai wani shiri da take k’ullawa, bayan ta had’a masa komi tace dashi:

 

“Bisimillah”

 

Amamakance ya kalleta yace:

 

“Ba atare zamu yi karin dake ba?”

 

Tayi saurin girgiza kanta tace:

 

“Kaci kawai ni ba ayanzu zan karya ba”

 

Tana maganar tana karya harshe, tareda jifar sa da wani shu’umin kallo, Aliyu yayi shiru na minti biyu, sannan yayi tsam ya mik’e tsaye, da sauri ta kalleshi tace:

 

“Lafiya ina zakaje kuma?”

 

Ya fara tafiya yace:

 

“Ki kawo man d’aki acen zanci”

 

“Aiko jikinta yana rawa ta biyoshi da abun Karin, farin ciki fal ranta, tana ajiyewa yace:

 

“To taje ta dawo, toilet zai shiga idan ya k’are zai kirata”

 

Aiko acikin farinciki ta fita tana rausaya, tana fita yasaka makullli ya dantse d’akin, ya bubbud’a komi, sannan ya d’auko leda ya zuba abincin, ya raga saura, sannan tea d’inma da ta had’a agabanshi zuciyarshi bata kwanta dashi ba, shiga yayi toilet ya zube amasai yayi ploshing sannan ya fito da kofin ya ajiye, sannan ya bud’e d’akin, yayi zaune dirsham alamar yaci ya k’oshi, koda ta dawo ta iskeshi ya goge baki da tissue, wani farinciki ya lullub’eta, data sauri ta haye cinyar shi tana aika masa da manyan sak’una, acikin dakewa yace:

 

“Je ki Kai kayan ki ajiye,sannan ki dawo”

 

Aiko jikinta yana rawa ta ridi kwanoni tayi kitchen akayi dai dai saiga kira ya shigo wayarta dake kan kujera tana ta ringing, da sauri ta ajiye kayan tazo ta d’auki wayar, tana ganin mai kiran ta shige d’akinta da sauri, Aliyu kam shigewarshi wanka yayi agurguje ya fito yasaka kaya ya dauko ledar da yasaka abincin, ya fita sai k’arar tashin motar shi ta jiyo, da sauri ta fito har k’ofar gidan, amma ko k’urar shi bata gani ba.

 

Yana cikin tafiya ya gangara wata bola yayi cilli da ledar, sannan ya tafiyar shi sha’anin gaban shi.

 

Wasa wasa dai sai da suka kai sati ahaka, yana wasar ‘yar b’uya da ita, abincinta ma, da ta kawo masa ya saka aleda ya fita ya zubar, saboda zuciyarshi bata amince da ba wani surkulle aciki ba, yana tsoron ya baiwa wani almajiri, acutar da rayuwarshi, shiyasa yake zubarwa.

 

Matakin farko da ya d’auka na horar da hajiya Zulai shine, rashin zuwa gaidata, ko kiranta a waya duk ya soke, itace kawai take kiranshi in ta matsu tajishi, tace yazo tana nemanshi yace to, kamar gaske amma kuma yayi luf yak’i zuwa, tun abun bai damunta har ta fara shiga damuwa akan hakan, saboda abubuwa ne sukayi mata yawa, damuwa goma da ashirin, boka tsidudu aikinshi kamar yankan wuk’a, amma wannan karon ya kasa biyamata  da buk’atar ta, saboda yayi ta tura aljanu akan tsohuwa amma sai su dawo suce bazasu iya sauka kanta ba, saboda tun tana da k’urciya itama gwana ce wajen shige shige, akwai tsari sosai ajikinta, saboda duk da tsufanta ta rik’e ibadarta sosai.

 

Haka itama jimmai asirin ya k’i kamata, don itama atsaye take da neman tsarin jikinta, duk ta inda suka b’ullo mata sai ta tsallake, gashi bokan ya sanar da ita yaranta basu cikin kwanciyar hankali, domin duk ya shiga bincike sai ya hangosu suna ta kuka, shiyasa ta damu da Aliyu yazo suyi shawarar abunyi, domin Alhaji taje masa da maganar amma kanzil baice da ita ba, yanzu haka ya kwashe komi nashi ya koma sashen aunty Amarya da zama.

 

Ab’angare d’aya kuma kulsum sai iza mai kan tururuwa take yimata, tana saida k’addarorinta tana yimata jagora wajen bokaye ta had’a Kai da  su sunata cin kud’in su, suna sharara mata k’arya, shiyasa duk da sadiya tana fad’a mata irin wilak’ancin da Aliyu yake mata, bata wani damu ba, don wata hanya ta bud’u ta cin kud’in ab’agas, kullum sai bata hak’uri takeyi, akan ta k’ara hak’uri akwai wani plan da take shiryawa na tatse hajiyar tass sannan suyi plan d’in su na biyu Akanta.

 

 

Sati biyu yau cif da auren Aliyu da k’annenshi, amma idan ka Kalli hajiya kallo d’aya zaka gano ramar da tayi, saboda tashin hankali, ayau dai tagaji da rashin ganin Aliyu ta kirashi tace yazo tana neman shi, yace to gashinan zuwa.

 

Aiko minti sha biyar atsakani sai ga Kirashi awayar ta yana sanar da ita gashinan ak’ofar gida yakasa shiga cikin gidan ta fito su gaisa, acikin mamaki hajiyar ta fito, suka rab’e ajikin d’akin mai gadi, Hajiya tana kallonshi taga duk ya rame, acikin d’aga murya tace dashi:

 

“Me ke damunka haka Aliyu kaga yanda duk ka rame lokaci d’aya, ko baka cin abinci ne, Sannan ka daina zuwa gaidani, ni in nakiraka bazaka zo ba shin me kake nufi daga yin aurenka sati biyu duk ka sauya halayenka na kirki”

 

Aliyu yazama kalar tausayi yace:

 

“Wallahi hajiya nima bansan abunda ke damuna ba, haka kawai naganni ina wannan ramar, sannan inason inzo in gaidaki, amma sai inji nakasa, ban iya zuwa gidan, haka idan kin kirani, nasha zuwa nan k’ofar gidan sai inji bazan iya shiga ba sai in koma”

 

Ya k’are maganar tareda fashewa da kuka, acikin tashin hankali Hajiya tace:

 

“Hajiya kulsum ni zakiyiwa cin amana, akan yaro na?, na amince dake na had’a auren d’ana da ‘yarki shine kikeso ku rabani dashi?”

 

Aliyu ya fara rawar murya yace:

 

“Hajiya fa bxa ruwansu, Don Allah kar ki ga laifinsu, ai Sadiya da mahaifiyarta kowa yasan mutanen kirki ne san…. ”

 

Hajiya ta katse shi da cewa :

 

“Kai rufeman bakinka har yanzu Kai yaro ne bakasan komi ba, ana nuna maka gabas kana runtse ido”

 

Aliyu ya fara rantse rantsen ba ruwan su kulsum, hajiyar tayi mashi kallon uku saura kwata tace:

 

“Inafa zasuyi ruwa tunda anwanke anbaka ka shanye, wallahi dani take zance, ni kaga tafiyata, amma idan har na kiraka kazo ko anan k’ofar gidan ne zamu rik’a gaisawa”

 

Sannan sukayi sallama, ya tada motarshi farinciki fal zuciyarshi, ya bar wajen, Hajiya ta bishi da kallon tausayi tace:

 

 

“Oni Zulaihatu anaso amaida man da yaro lusari, haka kawai na d’ebo ruwan dafa kaina, to wallahi Ni ko ke kalsum da munafukar d’iyar taki”

 

 

 

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

 

 

Akafta🤸🏻‍♀

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 54

Advertisement *Page 54* ******************* Azaba iya azaba Raliya tasha ta amma ta kafe k’am da cewa ita ba…
KALLABI
Read More

KALLABI 32

Advertisement BABI NA TALATIN DA BIYU Duk yadda Aminatu taso kin shiga cikin gidan haka Innayoh ta tisa…
Read More

TARTSATSI 42

Advertisement *Page 42* **************** Hafsa tana zaune sai faman sak’awa da kwancewa takeyi, in ta kamo hanya nan…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 22

Advertisement 22   Yana Jan Jan Dan ya taje, ta rike hannunsa,sabida wata irin masiffan zafine daya ratsata,…
Read More

TARTSATSI 85

Advertisement   *Page 85*   **********************   Aikam Hajiya tayita sababi, bakinta yana kunfa, saboda tsabar masifa, dak’yar…