TARTSATSI 91

Advertisement

*Page 91*

 

**********************

 

Sum sum maryam ta tashi ta shige d’aki, jiri yana kwasar ta, ta fad’a kujera tana maida numfashi.

 

Asace Abbakar ya shigo mata da abincin da ya siyo mata, saboda tsaro aleda ma aka sako abincin, yace ta shige k’uryar d’aki ta cinye, aikuwa jikinta yana rawa ta fad’a, tun atsaye ta fara aika abincin, ci takeyi wani baka wani ahannu, tass ta canye, ya kawo mata ruwa tasha sannan taji ta dawo mutum.

 

Ranar dai ba yanda Abbakar baiyi da ita ba akan, Tana bashi hak’k’in sa, amma tayi k’ememe ta hanashi sai da taga ranta ya b’ace sannan ta amince, bayan ya k’arasa ta fara kukan tausayin kanta, da ya tambayeta lafiya, shine take sanar dashi abunda Inna tace, aiko Abbakar wata dubara ta fad’o masa, ya tashi tsam ya d’auko wata k’atuwar roba, sannan ya kawo mata ruwa yace tayi wankan aciki, zaije ya zubar da ruwan, aiko jikinta yana rawa tayi wankan, ya d’auki robar yaje yana zubar da ruwan amakwarara, yaji inna abayanshi da sauri ya juya, aiko ta kafe shi da ido tace:

 

Advertisements

Abbakar ruwan mine kake zubarwa acikin dare, aikuwa dubara ta fad’o masa yace:

 

“Amai tayi inna shine na goge, nazo in zubar da ruwan”

 

Inna ta fara salati, aikuwa saigata da fashewa da kuka tana sharar hayaye da gefen zanenta, da sauri Abbakar ya ajiye robar yazo wurinta yana lallashinta tayi shiru, Inna ta fara tafiya Abbakar ya biyota yana bata hak’uri,  ta kalkeshi dakyau tace:

 

“Shikenan ni Abu d’ana k’wallin k’wal Mace zata maida man dashi sallamamme, yanzu don tayi amai shine bazata iya hidimar abunta ba, sai kai ko,?”

 

Abbakar ya karye wuya alamun tausayi yace:

 

“Inna yunwa taci k’arfinta ko motsi bata iya yi, shiyasa na tashi na gyara, Amman kiyi hkr Don Allah bazan Sake ba”

 

Advertisements

Sannan Inna tayi shiru amma da sharad’in bazai sake yiwa maryam bauta ba, yace yaji ya d’auka, sannan sukayi sai da safe ya shige, ya barta anan tana tunani.

 

***

 

Aliyu da Sadiya dai har azuwa wannan lokacin, suna nan zamansu na doya da manja, domin kuwa tun tana neman shi yabata hak’k’inta har ta hak’ura, don yanzu ko zaman gidan ma bayayi, ballantana taga damar shi, in ya fita sai dare yake dawowa ya shige abunshi, tana kwana uku bata sakashi a idonta ba, saboda lokacin da yake fita tana cen tana baccin asara, wanda ko sallah sai rana ta fito take yinta, baya dawowa agida kuma, har sai ya tabbatar da tayi bacci sannan ya shigo.

 

Rashin zaman gidan shi da bayayi ne, yasakata gayyato abokanta, sunata holewar su agidan, suci su sha suyi k’at, su baje falo suna ta tik’ar rawa abunsu duniya sabuwa.

 

Ana cikin wannan halin ne kulsum ta kaiwa  Sadiya ziyara, suka k’ule ad’aka, suna ta k’ulle k’ullen Mugun abunsu, ta fad’a mata duk cin zarafin da Hajiya zulai tayi mata, da alwashin da taci a kan sai Sadiya ta koma bazawara, Sadiya hankalinta ya tashi ta fara kuka tace:

 

“Nidai wallahi  ina son Aliyu ahakan ma, duk da baya kulani, idan na tuno ni matar shi ce inajin dad’i, don Allah hajiya kiyi wani abu don gudun faruwar hakan”

 

Kulsum ta ciro wani magani aleda ta baiwa Sadiya acikin mamaki tace da ita:

 

“Maganin miye ne?”

 

Kulsum ta gyara zama tareda sauke ajiyar zuciya tace:

 

“Wannan da kike gani Magani ne, wanda yake kawo k’arshen duk wata ‘yar tsama atsakanin ki da abokin gaba”

 

Sadiya takai dubanta ga maganin, sannan ta d’ago ta Kalli hajiyar tace:

 

“Wannan wane irin magani ne shikam?”

 

Kulsum ta b’ata fuska ta maida ta, fuskar marasa imani sannan tace:

 

“Ba wani magani bane guba ce, nikeson kiyi k’ok’ari kiyi duk yanda zakiyi  Hajiya Zulai ta cita”

 

Sadiya ta zaro ido awaje tace:

 

“Gu me?”

 

Kulsum tace:

 

Tabbas Guba ce, idan har kinason ta barki kiyi zaman lafiya agidannan, don nasanta kar tunda har ta furta wannan magana to zata bi duk hanyar tasan zai wargaza wannan auren, tun kafin mu samu gurin mu ya cika, tunda har yanzu shi kafaffen d’an nata aikin mu yak’i kamasa, ke kinfi kowa sanin gurinmu bai wuce muyi amfani da Aliyu, mu yashe dukiyar Alhaji Hamza ba, to nadai samu ita hajiyar na tatsi kaso mafi rinjaye na dukiyarta, sauran mu samu kan Aliyun mu dafe, muyita hark’allar mu hankali akwance ba wanda zai tuhume mu, amman muddin Zulai tana raye, wannan damar sam bazamu sameta ba”

 

Jiki asanyaye Sadiya tace:

 

“Toni hajiya taya zan saka mata ita nikam, tunda nazo gidannan ban fita ba har yanzu”

 

Kulsum tace:

 

“Dabara zakiyi masa kice, kina so kije ki gano ta, idan kinje sai kiyi k’ok’arin saka mata abinci ko abinsha”

 

Sadiya jiki amace tace:

 

“To idan anyi nasara taci atunaninki ba za’a gano nice ba?, nifa wallahi inajin tsoro”

 

Kulsum taja gyalenta,  tareda rataya Jakarta, sannan tace da ita:

 

“To ki jira idan auren ya mutu, ai sai ki dawo gida, muci d’ora daga inda muka tsaya”

 

Tana k’are maganar tayi fuuu ta fice, Sadiya tana biyarta tana bata hak’uri amma ina, ko kallonta bata sake yi ba, ta tafiyarta, Sadiya ta dawo ta d’auki maganin ta b’oye sannan ta shiga tunanin abunda zaije ya dawo, don taji tsoron abun sosai.

 

****

 

Cikin Hafsa yana wata takwas ta fara jin motsin shi, aikuwa kwance take falo tayi rigingine, tana latsar waya taji shi yana ta halbawa, da sauri ta tashi zaune,ta dafe inda taji motsin, wani tsoro ya ziyarceta, aikuwa aza hannunta keda wuya ya k’ara motsawa, da sauri ta fad’a toilet ta tub’e kayanta, ta tsurawa cikin kallo, aikuwa sai gashi ya k’ara motsawa har tana hango fatar tana motsi, ba shiri ta k’wallah k’ara, saiga Sadauki aguje ya banko k’ofar ya shigo, ganinta ahaka ya sakashi jin tsoro, jikinshi yana rawa ya rik’ota d’aga murya yace:

 

“Lafiya?”

 

Aikuwa da sauri ta ruk’unk’umeshi tace:

 

“Maciji”

 

Sadauki ya zaro ido yace:

 

“A’inah? ”

 

Ta nuna masa cikinta, Yabi hannunta da kallo, inda take nuna masa, akid’ime yace:

 

“Anan ya cijeki?”

 

Ta d’ago fuskar ta tana kallonshi hawaye sharkaf a fuskarta tace:

 

“Ba cizo na yayi ba, amma najishi acikin cikin na,  ya shige  yanata motsi”

 

Sadauki yayi shiru na minti biyu sannan yace:

 

“Baki dai ganshi ba ko?”

 

Ta d’aga masa Kai, sannan ta k’ara da cewa:

 

“Motsi naji yanaman acikin ciki”

 

Sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya maida mata da kayanta, sannan ya jawota, suka koma falo, ya zaunar da ita, sannan ne wata dariya tazo masa, ya kalleta yace:

 

“Wai meyasa har yanzu kika kasa zama Sadaukanya ab’angaren tsoro da wauta?, ke akullum da sabuwar diramar da kike zuwa da ita”

 

Hafsa ta harareshi tace:

 

“Yanzu miye abun dariya anan kuma? Ka ko san…”

 

Kafin ta k’arasa maganar ya koma motsawa, da sauri tace:

 

“Gashinan ya k’ara motsawa, zai cenye abun cikin yayi muna bak’in ciki, Shikenan zai cenye man hanji in mutu, Wayyo ni Allah na”

 

Sadauki kam me zaiyi inba dariya ba, itako idonta kamar su fad’o saboda harararshi, yana dariya yace:

 

“Kinyi abun dariya ai dolene abarni inyi abuta ko malama, yanzu ke don Allah baki san ciki idan yakai wata hud’u yana motsi ba?”

 

Sai alokacin Hafsa ta tuno da karatun da aka yimasu a islamiyar su, akan ciki halittar mutum, sannan ta fara dariya tace:

 

“Na tuno ance kwana Arba’in yakeyi, a maniyyi, sannan ya koma gudan jini, yayi wasu Arba’in  ya koma tsoka, sannan yayi wasu Arba’in ahura masa rai, kenan yanzu da ranshi kenan shiyasa ya fara motsi?”

 

Sadauki ya d’aga mata kai, aikuwa wata kunya ta lullub’eta, tayi kwance ta rufe fuskar ta da tafukan hannyenta, sadauki yazo yayi durk’uso ya d’aga rigarta ya kaiwa cikin sumba, da sauri ta tashi zaune tace:

 

“Kaifa bakada kunya yasin”

 

Ya d’ago ya zauna, Sannan ya jawo ta jikinshi yace:

 

“Zo in gaisa da farinciki na”

 

Hafsa ta turo baki tace:

 

“Sana’ar kenan”

 

Yace :

 

“Eh naji ki fad’i duk abunda kikeso, amma bazaki hanani gaisawa da abun cikin k’wai na ba”

 

Da dabara yakaita d’aki, daganan suka lula acikin aduniyar ma’aurata.

 

****

 

Bayan Watanni biyu, abubuwa da yawa sun faru aciki har da, k’are iddar Salma,dr asukwane ya kawo kanshi awurin Abba ,tareda baza k’ok’on baranshi yana rok’on abashi dama ya fara neman Salma, Abba ya nuna masa rashin dacewar Hakan, tareda bashi hak’uri, sannan lular dashi idan har da gaske yana son Salma to ya rik’e basma amana tareda d’an k’aramin cikin da take dashi, Abba ya nuna masa da Salma da Basma duk d’aya suke awurinshi, Dr dole badon yaso ba ya hak’ura ya rungumi matarshi.

 

Agefe d’aya Masu bid’ar auren Salma suka yo caa, ba manyan alhazawa ba ba, matasa masu aure ba, har samarin ma ba’a barsu abaya ba.

 

Abba ya bata dama ta zab’i wanda takeso, amma ina ita zuciyarta rufe ruf take bata hango kowa face yaya Aliyunta.

 

***

Ab’angaren Karima ma aure ya mutu ta dawo gida, asanadiyyar zuwan da Hajiya tayi gidanta, taga halin da take aciki, tabi duk ta rame tayi bak’i, domin koda taje ta iske ta atsugunne tana ta wanke wanken tsibin kayan da aka jibgo mata, wasu kwanonin ma dagangan ake b’ata su, don kawai asakata wankewa, izuwa lokacin duk wani lungu da sak’o na gidan ita ke sharewa, wanke wanken ma haka safe da marece, ga wankin yaran duk ita ke wankesu ta goge tass, saboda ubansu ya d’aure masu gindi, aikin komi basuyi agidan itakeyi, aiko hajiya tana zuwa taganta hankalinta ya k’ara tashi, ta fara masifa, jimmai ta fito ta wanketa tass da soso da sabulu, Hajiya ta fara kuka tana had’awa karima kayanta, zata fito da ita ne Saiga Mukhtar ya dawo, jimmai ta kira said ta sanar dashi k’arya da gaskiya, aiko yana zuwa yace da hajiya ta maida karima, don har lokacin bata k’are aikin kud’in shi da tasa ya salwantar wajen auren ta ba, Hajiya ta fad’a ya fad’i suka dinga yi, har Karima taji haushi ganin Hajiyar ta, yasaka ta cire tsoron shi, fara maida masa da martani, aiko ba kunya mukhtar yasa bulala ya zane Karima tass agaban Hajiyar,har saida yaga bata motsi, sannan ya bita da saki Uku, acikin tashin hankali hajiya tabar gidan takai Karimar Asibiti, sannan taje ta d’auko masa y’an sanda suka zo suka tafi dashi.

 

***

 

Maryam dai kam Sun d’aura aure da hak’uri, don kam hajiya ta tare gaba ta tare baya, ana cikin haka kuma saiga ciki ya b’ulla, dole tayi hak’uri ta sabawa kanta da tsiwar Hajiya, saboda mijinta yana sonta.

 

***

 

Sadiya kam da tunanin hanyar da zata kashe hajiya take kwana take tashi, saboda Kulsum tayi fushi da ita sosai, dole ta cire tsoro ta dawo neman hanyar da zata kashe hajiya acikin ruwan sanyi ba Wanda ya sani.

 

Aliyun ma ta daina kulashi, domin ta fahimci in ta biyeshi bak’in cikinshi zai kaita kushewa, shiyasa ta yanke hukuncin komawa sana’arta, ta bin maza, aiko da ya fita zata d’aga waya ta kira saurayinta, yazo suci karen su ba babbaka.

 

Aliyu ya daina d’aukar wayar hajiya ma, ko ta kira baya d’agawa, waya ta k’araci kukanta har ta katse bai d’agawa, amma Daddy kam asace yana zuwa har sashen Aunty ya gaidashi, suyi firar su ya k’ara fita asace, saboda b’adda kamar da yakeyi, ba wanda zai gano shine acikin ma’aikatan gidan balle akai mata tsegumi.

 

Hajiya ta shiga tashin hankali ba kad’an ba rayuwa ta juya mata baya, abunda tafi k’arfi gashi yau duk sunfi k’arfinta, kad’aicin Aliyu ya dameta, aikowa ta kasa hak’uri arana tsaka ta dira gidan Aliyu, tashin hankalin da idanunta suka gano mata ya Saka suman tsaye, wato Sadiya ce tagani afalo turmi da tab’arya suna aikata fasadi itada kwarton ta, sun manta Sam basu saka key suka Rufe k’ofar ba, Ashe da rabon hajiya tayi Mugun gani, acikin kid’imewa Sadiya ta shiga d’aki ta d’auko gubar da kulsum ta bata, ta jik’a ta fito ta iske hajiyar tana ta dukan kwarton da standing pan dake ajiye tana basu iska.

 

Sadiya tana fitowa tayiwa kwarton ta signal, ya rik’a mata hajiya suka danneta suka yimata d’uren ruwan guba, dakyar suka samu ruwan suka shiga bakinta.

 

 

 

 

 

😳😳😳😳😳🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀mun boni

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 63

Advertisement *Page 63*   **********************   Anfara yimasu lallen ne saiga text ya shigo Wayar Hafsa tana dubawa…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 17

Advertisement €pisode 17…………….. Garin Zawatu ya cika dam da mutane . Kowa ka gani yayi kyau sosai cikin…
INAYAH
Read More

INAYAH 36

Advertisement _36_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Ahankali ya waiwayo ya kalleta Ganin irin kukan datakeyi yasashi Dan sauke ajiyar zuciya Yana…
KALLABI
Read More

KALLABI 58

Advertisement BABI NA HAMSIN DA TAKWAS Kurawa juna ido suka yi, kafin Lamido ya janye yana me shafa…
INAYAH
Read More

INAYAH 14

Advertisement 14_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Farko Inayah tayi mamaki sosai da maganganun Zaid din sbd Bata dauka Yana fada da…