TARTSATSI 92

Advertisement

*Page 92*

 

**********************

 

Bayan sun tabbatar tasha maganin ne, Sadiya tace da kwarton ta, yayi sauri ya bar gidan, kada asirin su ya tonu, aiko ad’ari ya cikawa rigar shi iska ya fito gidan saboda sauri idanunshi sun rufe, bai hango Auwal dake k’ok’arin shiga gidanshi ba akan mashin d’in shi, aiko ba shiri Auwal yayi ciki dashi ya fad’i, yana k’ok’arin bashi hak’uri ne yaga ya tashi da gudu yana d’igishi ya nufi bakin titi, Auwal ya bishi da kallo da namaki akan fuskarshi, saboda yaga daga gidan Aliyu ya fito, zuciyarshi ta bashi cewa k’ilan b’arawo ne ya shigar masu gida basu nan sun fita, aiko ya shigar da mashin d’inshi acikin get d’in gidanshi, ya juya zai shiga gidan Aliyu, azuciyar shi yace:

 

“Ko ba komi akwai hak’k’in mak’otaka”

 

Asma’u ta fito tarar sa don taji k’arar mashin d’inshi, sai taganshi zaije gidan Aliyu, mamaki ya kamata, ta biyo bayanshi, domin ta ganema idonta abunda zai Kai Auwal gidan Aliyu, don tasan ba zuwan alkhairi ne zaiyi ba, ita kuma batason fad’an da sukeyi da juna, saboda akullum tana fahimtar dashi, Aliyu fa bada son ranshi ya saki Salma ba, amma ina yak’i fahimtar ta, shine dalilin da ta biyoshi, duk da zungureren cikinta, saboda batason su rabawa kansu abun magana.

 

Advertisements

Auwal ganin k’ofar abud’e yasa ya gano matar gidan tana nan, shiyasa yaja burki yana k’ok’arin barin wurin ne yaji kakarin Hajiya, tana shure shuren zuwa barzahu, aguje ya fad’a don atsammanin shi matar gidan ce, b’arawon yayiwa Illah.

 

Aiko Sadiya tana rik’e da waya zatayi kira tana ganin shigowar Auwal,  ta fara ihu, tana fad’in:

 

“Wayyo Allah ya kashe muna hajiya ya tsere”

 

Asukwane Asma’u ta k’araso jin kuwwar Sadiya, Auwal kam ganin ta atsaye, Hajiya akwance magashiyyan, idanu sun ture kunfa ya fara fita abakinta, sai kakarin mutuwa takeyi, yasashi isa wurinta ya tallabota, duk da uban jikinta, baiji nauyin tallabota ba, da hanzarinshi ya kamota ya fito da ita gidan, yana tallabe da rabin jikinta suka kai bakin titi, Asma’u jikinta yana rawa ta rufo gidansu, ta biyo bayansu, acikin tashin hankali, jikinta yana ta kyarmar tsoro, ya kamata.

 

Mai adaitata Auwal ya tare suka shiga, sai babbar asibitin mai zaman kanta, suna zuwa bayan ‘yan cike cike, aka shigar da hajiya emergency room, akace da Auwal tunda case d’in babba ne, dole ne aje azo da d’ansanda, Auwal ya dinga basu hak’uri ya nuna masu cewa mahaifiyar shi ce, suka nuna lalle sai anzo dasu, don atsarinsu ma basu karb’ar irin case din saida su, amma da yake sunganta unconscious shiyasa suka Karb’eta, aiko anan ya bar Asma’u da Sadiya da tabiyo su, bayan tayita tsinewa Auwal yafi cikin kwando, da yazo ya taimaki hajiya, taso ace sai ta mutu sannan tayi kururuwa mutane suzo.

 

Sannan Auwal  yaje yazo da ‘yansanda biyu,  suka tsaya zaman jiran me zai faruwa, sadiya ido suka rena fata, cikinta ya duri ruwa sai faman raba idanuwa takeyi, tana ta rok’on Allah yasa kar ta tashi, addu’a d’ai takeyi Allah yasa hajiya ta mutu kowa ya huta.

 

Advertisements

Asma’u tace da Auwal ya kira Aliyu ya fad’a masa, ya mik’a mata waya yace takirashi, aikuwa ta karb’a zata kira, Sadiya tayi karaf tace:

 

“Ai nakirashi yana kan hanya”

 

Asma’u da Auwal basu ce da ita k’anzil ba, sukayi kamar badasu take ba,  suna nan zaman jugum jugum sai ga Aliyu yazo hankali atashe, yana rabon ido ganin Asma’u da Auwal, kodai Sadiya k’arya takeyi ba hajiyar shi a batada  lafiya ba, ya k’araso ya mik’awa Auwal hannu sukayi musabuha, fuskokinsu ba yabo ba fallasa, Asma’u ta Kalli Aliyu acikin tausayi ta gaidashi, ganin yanda duk ya rame, yasamu wuri ya zauna, ko  kallon inda Sadiya take baiyi ba, suna nan azaune har aka gangaro gadon hajiya aka fito da ita akwance samb’al tamkar matatta, wani likita yace ina  mutanen patient d’in, Auwal da Aliyu suka had’a baki wajan fad’in:

 

“Gamu”

 

likitan ya dube su yace dasu:

 

“Ya kuke da ita ne?, ko duk yaranta ne ku? ”

 

Sukace: ” Eh ”

 

Yace: “to kubiyoni office”

 

suka bi bayanshi, yayinda Asma’u da Sadiya suka rufawa gadon hajiya baya, Sadiya tana Alla Alla akan ta samu dama ta iyar da Kai hajiya kushewa, tunda har bak’in taurin ranta yasa tak’i mutuwa.

 

Auwal Aliyu suna Agaban likitan,yana yimasu bayani fillah fillah, yace dasu:

 

“Asakamakon bincikenmu mun gano tasha guba ne, shine yayi sanadiyyar yin barazana da rayuwarta, munyi nasarar karya dafin gubar, amma duk da haka dole ne sai munyi mata aiki an yanke gefen hanjinta da suka samu matsala, idan kuma ba haka ba ciyon zaiyita ci gaba har ya kama sauran hanjin gabad’aya, wanda ba fata ba kuma kunsan abunda sakamakon hakan zai bada, Wanda ba’a fata, saboda haka kuyi gaggawar biyan kud’i ashiga da ita ayimata Cs gobe, saboda rayuwar ta tana cikin had’ari”

 

Jikinsu duk ya mutu, musamman Aliyu da har jijiyoyin kanshi suka fito, saboda tashin hankali, Auwal yaje har kusa dashi yana bashi hak’uri, ya rik’o hannun shi suka fito waje, Aliyu ya Kalli Auwal yace:

 

“ya akayi kasan hajiya batada lafiya?”

 

Aliyu jiki asanyaye ya bayyana masa abunda ya sani, aikuwa jin taimakon da Auwal yayiwa hajiya yasakashi jin dad’i ba kad’an ba, yayi ta yimasa godiya, har saida Auwal ya nuna ai shima hajiyar Uwa ce awurinshi, sannan yace dashi ya tambayi matar shi itace zata bayyana masa komi don agabanta abun ya faru.

 

Atare suka shiga d’akin da aka kwantar da hajiya, suka duba ta, sannan Aliyu yace da Auwal ya jira shi zaije gida ya fad’owa Daddy, yazo da Karima domin ta kula da hajiya, ya Kalli Sadiya yace da ita tazo suje, aikuwa duk da ba haka taso ba, don taso abarta anan ta samu hanyar ida k’arawa hajiyar gudu, to amma ba yanda ta iya adole tabi bayan shi sukaje.

 

Tun amota ya fara nunawa Sadiya tsantsan bak’in cikin dake zuciyar shi, domin kuwa gudu yakeyi tamkar ba kowa atitin face shi kad’ai, kafin suje gida duk saida ya jigatar da ita, domin kuwa idan kanta ya bugi murfin mota ya dawo ya bugi kujera tayi luu zata fad’a ta dawo haka yayi tayi da ita har sukakai, tun akofar gida ya damk’o ta yana fisgarta har suka shiga cikin gidan, ya shak’e ta har sai da idanunta suka firfito yace da ita:

 

“Uban wa ne kika kawo acikin gidana, har kuka had’a Kai kuka so kashe man Uwa?”

 

Sadiya saboda tsoro saiga fitsari yana kwaranya ak’afafunta, taji shak’a iya shak’a sannan ya falla mata wani gigitaccen mari yayi Ball da ita saida kanta ya bugu da bango, tana dafe da wuyanta yayi durk’uso dai dai inda take acikin k’araji yace:

 

“Wanene?”

 

Sadiya acikin razana tace:

 

“Barawo ne, sata yazo yi”

 

Aliyu ya ciro belt d’inshi yayi ta laftar ta da k’ututun, saida ya lallasata dakyau sannan ya sake tambayarta, anan ma tace:

 

“Wallahi nima bansan shi ba” b’arawo ne yazo yi muna sata”

 

Aliyu da jajayen idonshi ya kallota yace :

 

“Me ya kawo hajiyata agidannan?”

 

Sadiya ta zaro ido tace:

 

“Nima bansan me tazo yiba wallahi”

 

Aliyu ya sake jifarta da tambaya yace:

 

“To wa ya bata guba tasha?”

 

Sadiya ta k’ara sautin kukan ta tace:

 

“Shine wallahi bani bace”

 

Aliyu ya Kalleta dakyau alamun rashin gaskiya suka bayyana akan fuskar ta, acikin fushi ya jawo gashinta k’iiii ya jefa ta wani store na ajiyar abinci ya rufe ta da key , sannan ya tada motarshi ya nufi gidan su wurin Abba.

 

 

 

 

Yau ake tartsatsi😝

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 54

Advertisement *Page 54* ******************* Azaba iya azaba Raliya tasha ta amma ta kafe k’am da cewa ita ba…
INAYAH
Read More

INAYAH 39

Advertisement _39_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Koda garin ya waye daga ita har ‘yarta  gabaki daya jikinsu kurajen cizan sauro sun…
INAYAH
Read More

INAYAH 1

Advertisement amuhgee_ Document queen meenali 1 _*please masu daukamun Sunayen books da Labarai suna sauyawa suyi nasu lamarin…