TARTSATSI 93

Advertisement

Page 83*

 

**********************

 

Aliyu durk’ushe agaban Daddy sai kuka yakeyi, acikin tashin hankali, saida Daddy ya barshi ya rage rad’d’in bak’in cikin dake damun zuciyar shi, sannan ya fara lallashin sa akan yayi shiru, Daddy ya sauke ajiyar Zuciya, acikin damuwa ya dafa kafad’ar Aliyu yace:

 

“Allah ya bata lafiya, tashi muje asibitin”

 

Daddy ya mik’e tsaye, Aliyu yayi saurin zuwa ya dafa k’afar shi yace:

 

Advertisements

“Daddy zan nemi wata alfarma awurinka, Don Allah ka yafewa hajiya duk abunda tayi maka, saboda wallahi hadda hak’k’in kane ke bibiyarta, ka yafe mata   Don Allah Daddy”

 

Daddy ya bubbuga kafad’ar shi ya tada shi tsaye yace dashi:

 

“Daman cen Zulai albarkacin ku ne take ci, musamman Kai idanunka ne suke hanani, d’aukar mummunan mataki akanta, saboda haka kada kaji komi Allah yasa gudurinka na alkhairi yayi aiki akanta, ta gano d’an hakin da ka rena shi ke tsone ma ido, sannan ta gano tsintacciyar mage bata mage, zo mu tafi Allah dai ya bata lafiya”

 

Daddy yana k’are maganar yayi gaba, Aliyu yace Ameen azuciyarshi, sannan ya biyo bayanshi, koda suka fito karima tana jingine ajikin mota tana jiransu idanunta sunyi jawur saboda kuka, saboda Aliyu bai b’oye mata komi ba, ya fad’a mata abunda ke faruwa.

 

Aliyu ya jasu suka rankaya sai asibiti, ya gwadawa Karima d’akin sannan

suka je suka biya kud’in komi da ake buk’ata, sannan suka zo d’akin da aka kwantar da Hajiyar, inda Asma’u da Auwal suke zaune zaman jiran dawowar Aliyu su tafi gida.

 

Koda karima ta shigo taga su auwal akan hajiya, ba k’aramin mamaki tayi ba, wanda ya fito fili k’arara akan fuskarta ya kasa b’oyuwa, bakinta yana rawa ta gaidasu, sannan tayi kan hajiya tana kuka.

Advertisements

 

Auwal da Asma’u suka gaida Daddy, ya amsa masu acikin jin dad’in ganinsu, musamman Asma’u da yagani ciki har ya turo, bayan sun gaisa ne yace da Auwal yaje yakai Asma’u gida ta huta, yayi masu godiya akan namijin k’ok’arin da sukayi wajen ceton rayuwar Hajiya, da sadiya tayi mata barazana domin ta bar duniyar.

 

Auwal da Asma’u sukayi sallama dasu suka fito, Aliyu ya rakosu har suka bar wajen yana k’ara jaddada godiyar shi agaresu.

 

***

 

Auwal baije gidansu ba, sai da yaje ya sanar da su Abba halin da ake ciki, sunyi mamaki sosai da jin wannan badak’alar, inda anan ne Asma’u ta bayyana masu irin abunda take gani da idanunta wanda Sadiya take aikatawa, duk da bata shiga gidan, amma duk ranar da tafito harabar get d’insu tana shan iska in auwal baya gida, to idanunta zasuyi ta bata abinci, saboda safa da marwar da ‘yan iskan mata sukeyi agidan Aliyu, domin kuwa Watarana ma su sadiya arabar gidan suke cashewarsu, suyita rawarsu suna kuwace kuwacen su.

 

Umma ta sauke tagumin tareda sauke ajiyar zuciya tace:

 

“Duk wanda ya d’ebo da zafi dai bakinsa, mudai babu ruwanmu aciki, iya kacinmu ido, ba abunda zamu ce sai dai Allah ya sauwak’a kuma ya bata lafiya, fad’an da ba ruwanka dad’in kallo gareshi, ku kuma Allah ya saka maku da alkhairi, akan ceton rai da kukayi”

 

Dukansu sukace: “Ameen”

 

Abba ya kallesu yace:

 

“Gobe ku shirya dukanmu muje mu dubo ta”

 

Umma tace:

 

“Amma bada Salma ba ko?”

 

“Abba yayi murmushi yace hadda ita, ko ita ba ‘yar gidan back? ”

 

Umma tayi tayi shiru, tareda b’ata fuska, Abba ya kalleta yayi murmushi, ya maida duban shi akan Salma yace:

 

“Ummusalma, gobe ki shirya muje agano hajiya zulai dake”

 

Salma da tunda aka fara firar bata ce k’anzil ba sai lokacin, asanyaye tace:

 

“To Abba, Allah ya kaimu”

 

Duk sukace “Ameen”

 

Abba ya kalli Umma yace”

 

“Itama Hafsa akira ta af’ad’a mata”

Auwal da Asma’u sukayi sallama da su, suka nufi gidansu.

 

Salma jiki asanyaye ta shige d’akin su, ta fad’a akan katifarsu tace:

 

“Alhmdllh Alhmdllh Alhmdllh Allah nagode maka da kaman wannan sakayyar”

 

***

 

Aliyu yana akan hanyar shi ta dawowa asibiti bayan yakai Abba gida ne, yaji ringing d’in waya acikin motor shi, amma baiga inda wayar take ba, ya lek’a ko ina baiganta ba sai kukanta kawai yakeji, har ta gaji ta tsinke, da sauri ya samu wuri yayi parking, sannan ya fito yana ta lek’en inda zai ganta, sai kawai ta sake k’ara alamar wani kira ne ya shigo, aiko lek’a anan Kurd’a anan ya hango ta AK’ark’ashin kujera, ya saka hannu ya jawo ta, zuciyar shi ta bashi tabbas wayar sadiya ce,  da sauri ya d’auka tareda danna recording, aiko saiga muryar kulsum tana cewa:

 

Wai ke lafiyarki ayita kiran ki baki d’auka, duk kinbi kin tada man da hankali, bansan halin da ake ciki ba, yanzu Zulan ta shura ko da kingin ranta, don Wlh kibi duk hanyar da zakibi ki Iyar da ita, inba haka ba Kwab’ar mu zatayi ruwa, yanzu ya ake ciki ne?, kina asibitin ko kin koma gida? ”

 

Kitt Aliyu ya kashe wayar, tareda dafe kanshi yace:

 

“Kulsum! Sadiya!”

 

Sannan yayi k’yafci ya jefa wayar Alhjihu ya shige motar shi zai tada ita saiga wani kira ya shigo awayar ta sadiya, har ya share don yasan Kulsum ce, amma sai wata zuciyar tace dashi ya d’aga yaji me zata kara cewa, aiko yana dubawa yaga wata number ce, yaga an rubuta sunan *azanto* da sauri ya kashe motor, ya d’auka, ya saka recording sai yaji muryar namiji yana magana, acikin tashin hankali yace:

 

“Haba Sady baby ina ta kiranki kink’i d’agawa, ya ake ciki ne, don nasan dai yanzu an binneta, ai gara da kika bata gubar, shegiyar  mata zata tona muna asiri abanza, bancin ta katse muna jin dad’in mu, ta tara muna jama’a, Allah ya tsare mu ai da batayi man ihu kwarto ba, da wallahi nasan yanzu ina gidan kaso, bayan naci na jaki, tunda ina fitowa aguje naci Karo da mak’ocin ku,  wai Allah ya soni nasha dak’yar,”

 

Ya k’are maganar yana wata dariya ta shak’iyanci,acikin fushi da zafin zuciya Aliyu yace:

 

“Azanto ko?”

 

Ba shiri aka kashe wayar, acikin k’unar Zuciya Aliyu yace:

 

“Sai kaci Ubanka wallahi, acikin daren nan za’a binciko man Kai d’an iska”

 

Ya fad’a mota ya fisgeta da k’arfi.

 

***

 

Da safe misalin k’arfe tara aka shiga da Hajiya d’akin tiyata, su abbasu fito ba har k’arfe biyu, sannan akayi nasarar magance matsalar ta, aka gungurota akan d’an gadon d’aukar marasa lafiya, aka shigar da ita wani d’aki sai sambatun kiran sunan Sadiya takeyi da kulsum,tana cewa”

 

“Yanzu kulsum  ni zaku ciwa amana?” na amince dake shine ku kuma kuka yaudareni?”

 

D’aki yayi tsit ana sauraron ta, zuciyoyi sai sak’e sak’e sukeyi, shidai Aliyu da ya riga da yasan komi, baiyi mamakin jin kalamanta ba, dak’yar aka samu tayi shiru bacci ya d’auketa.

 

Sannan Aliyu yayi gida saboda yana son yayi wanka, tun akan hanya ya tsaya ya siyo ledar biredi, da ruwan pure Water guda, koda yaje direct inda ya kulle sadiya yaje, ya bud’e, sannan ya wurga mata ledar biredin da pure water d’in, sannan ya k’ara rufe d’akin ya tafi d’akin shi yayo wanka, ya fito, koda ya koma wajen sadiya har ta cinye ledar biredin tass, ya shak’o wuyanta ya fito da ita Waje, fuska ad’aure yace:

 

“Kije kiyi wanka ki fito Muje asibiti, minti biyar na baki da ya kin bari ya wuce wallahi sai na sauya maki kamannu”

 

Arazane Sadiya ta kalleshi, ba shiri taji saukar wani bahagon mari, aguje ta fad’a d’akinta ta shige toilet ta dantse, tana wanka tana kuka, agurguje ta shirya ta fito, ya rufe gidan sannan suka kama hanya, sun fara tafiya atsorace tace dashi:

 

“Don Allah bakaga waya ta ba da na mance da ita anan cikin mot…?”

 

Kafin ta rufe bakinta, taji saukar wani azababben mari abakin, sai da ya fashe da jini, da sauri ta dafe bakinta, tana wani kuka marar sauti, har suka Kai asibiti bata koma yin magana ba.

 

**

Koda su Abba suka zo  sun iske ta ta farfad’o acikin hankalin ta, suna shiga ta bisu da kallo d’aya bayan d’aya, har idanunta suka tsaya akan Salma, aiko nan take wasu hawaye suka sirnano mata agefen fuska, da sauri Karima ta isa wurinta tana bata hak’uri,tana share mata hawayen, dukansu sukayi mata ya jiki har salma,ta k’ure kallon ta ga Salma ko k’iftawa batayi, hawayenta basu daina sauka ba, tayi nuni da hannu alamar Salma tazo wurinta, Salma ta Kai dubanta ga Umma, Umma ta b’ata fuska tareda kawar da kanta agefe, bayan tayiwa salma gargad’i da ido, Salma ta maida kallonta ga Abba, Abba ya d’aga mata Kai alamar taje, aiko asanyaye ta fara jan k’afafunta da sukayi mata nauyi, zuwa jikin gadon Hajiya.

 

Hajiya ta rik’o hannunta hawaye suna zuba tana shirin yin magana, Aliyu da Sadiya suka turo k’ofar suka shigo, Hajiya ta Kai dubanta abaakin  k’ofar, da sauri ta saki hannun Salma ta k’walla k’arar kiran sunan Sadiya, tana k’ok’arin tashi zaune, da sauri Aliyu yaje ya hanata, ta Kalli Sadiyar tace:

 

“Munafuka me ya kawoki wurina algunguma, shegiya tsinanniya, ‘yar haihuwar bayan mahaifa, Allah ya tsinewa Kulsum albarka da tayi sanadin zuwanki duniya, shaggu zuri’ar tsiya, babbak’un karuwai, Allah ya isar Man akan ku, tunda har kukayi sanadin raba d’ana da nayi da matar kirki, na had’a shi dake la’ananniya,Allah ya walak’antaku daga ke har Uwarki”

 

Sadiya ta fara kuka tana bata hak’uri, Hajiya ta Kalli Aliyu tace:

 

“Fitar man da ita indaina ganinta a idona, tun kafin zuciyata ta tarwatse”

 

Aliyu yace:

 

“Kiyi hak’uri hajiya ganinki fa tazo yi”

 

Hajiya ta runtse idonta da sauri tace:

 

“Aliyu wa ya haifeka?”

 

Aliyu yace: “ke hajiya”

 

afusace tace:

 

“Na baka Umurni ka sake ta yanzu yanzunnan”

 

Aliyu ya zaro ido atsorace kamar gaske yace:

 

“Don Allah hajiya Kiyi hak’uri nidai wallahi inason matata”

 

 

 

😹😹😹😹Tartsatsi😂

 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 71

Advertisement *Page 71*   **********************   Aliyu bai tsaya iya marin ba, cikin fushi ya cire belt d’inshi…
Read More

TARTSATSI 7

Advertisement *Page 7* ************** Mustapha ya doshi hanyar cikin gidan yana ta sake sake a zuciyarshi. Koda yashiga…
Read More

TARTSATSI 1

Advertisement *Page 1* Yanmatane su biyu gefen titi suna tafe suna hira tsakaninsu kasa kasa wanda idan ba…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 34

Advertisement Kallanta yakeyi bako kiftawa tunanin da yake ya tasheya ko a’a yama Rasa me zaiyi,sai yayi kamar…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 17

Advertisement €pisode 17…………….. Garin Zawatu ya cika dam da mutane . Kowa ka gani yayi kyau sosai cikin…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 15

Advertisement pisode 15……………… Ruwan magarya ya ɗauka cikin wata kwalba ya buɗe , sannan ya yaye lulluɓin da…