TARTSATSI 94

Advertisement

*Page 94*

 

**********************

 

Aiko saboda jin lafazin bakin Aliyu da sauri hajiya numfashinta ya fara sama da k’asa da sauri aka kira Dr’s suka rufu kanta, dak’yar aka shawo kan matsalar, sannan akayi mata allurar bacci.

 

Akace kowa ya fita abarta itakad’ai ta sami hutu, haka ko akayi, suka ajiye abunda suka zo mata dashi sannan dukansu suka fito waje, Aliyu sai satar kallon Salma yakeyi, da sun had’a ido ta galla masa harara ta kawar da kanta agefe, shidai iyakacinshi murmushi, sadiya kam tana rab’e agefe, tana tunanin ta wace hanya zata bi ta sub’uce ta bar asibitin, amma duk wani motsi nata yana kan idon Aliyu, suna nan zaune saiga Hafsa da Sadauki sun zo, da sauri Hafsa ta ajiye kulolin dake hannuta,ta isa wurin Umma da gudu ta ruk’unk’umeta tace:

 

“Oyoyo Ummata”

 

Advertisements

Umma tayi saurin fad’in:

 

“Nifa dad’i na dake baki girma Hafsa, duk da wannan abun dake jikinki, baki tausayin kanki”

 

Hafsa ta zunb’uro baki,  ta janye jikinta tace:

 

“To Umma ni Shikenan sai infasa murnar ganinki?”

 

Umma tana dariya tace :

 

“Eh ki fasa d’in”

 

Advertisements

Abba yana murmushi yace:

 

“Naganku arana Uwa da ‘yarta”

 

Umma tayi dariya tace:

 

“Jikana ko jikanyata nike tattali, tunda ita bata jin jikinta”

 

Hafsa taje wurin Abba  da Aliyu ta gaidasu, Sadauki ma ya k’araso ya kwashi gaisuwa awurin su Abba, sannan ya je wurin Aliyu sukayi musabuha, yana tambayar shi Auwal, Aliyu yace dashi yana kan hanya, sannan suka fara maida magana akan zancen ciyon na hajiya.

 

Hafsa ta rik’o hannun Salma tana murmushi tace:

 

“Kefa b’ata fuskar na minene?”

 

Salma ta galla mata harara, Hafsa tazo saitin kunnenta tace:

 

“Ko na murnar ganin yaya Aliyu ne?”

 

Hafsa tana ganin yanayin Salmar tagano akwai abunda yake damunta, afakaice ta jawo hannunta suka bar wajen, suka zauna akan wasu kujeru, Hafsa ta rik’o hannunta tace:

 

“Me ke faruwa ne naga ranki ab’ace?, wani abu aka yimaki ne?”

 

Salma kam sai ji tayi hawayen da take mak’alewa suna gangaro mata akan fuska, da sauri Hafsa tace:

 

“Subhanallah Aunty Salma meye abin kuka kuma?”

 

Salma ta kwashe abunda akayi ta fad’awa Hafsa, acikin jimami Hafsa tace:

 

“Ki iya takun ki hajiyata, kada ki kuskura ki bada k’ofar da zai gano kina kishin shi, ki yi kamar ma baki ji me yace ba, jikina yana bani ya kusa zuwa hannunki, ke kuma alokacin ki wujijjigashi dakyau har sai ya galabaita, sannan ki tausaya masa koshi azuwan bada son ranki ba”

 

Salma ta share hawayenta tace:

 

“Nagode mangatah,  amman wallahi bakiji yanda nikejin zuciyata ba”

 

Hafsa tace:

 

“Cool Dawn aunty nah kema fa zakiyi time d’inki, matso kiji”

 

Aikuwa ta rad’a mata wata magana akunne, da sauri Salma ta zaro ido awaje tace:

 

“Kin kawo shawara mangata”

 

Daga nan sukaci gaba da tattaunawa har su Abba suka kirasu akan salma tazo zasu wuce gida.

 

Koda sukaje sukaga Asma’u da Auwal sun zo, akayi ta gaishe gaishen juna, Abba yace zasu wuce akayi masu rakiya har jikin motar shi da sukazo da ita, bayan sunyiwa Hajiya zulai fatar samun lafiya, Aliyu dai sai kallon gefen ido yake yiwa Salma yayinda tayi biris dashi tamkar ma batasan ma yana wajen ba.

 

Sadiya dai sai raba idanu takeyi, saboda gaba d’aya afirgice take, don tagano su wane Abba, wacece Salma, itakanta ganin Salma ya rud’a ta ba kad’an ba,  saboda duk iya kushen mai kushe bai isa ya kushe halittar Salma ba, ayanzu ta gano Ashe ba banza ba Aliyu ya manne mata, don itakanta ta yarda da cewa Salma mace ce, idan Aliyu yana ganin ta to ita ba abunda zai yi da ita, saboda ta burgeta ba kad’an ba, atake tayi datasani bata aikata abunda tayi ba, kodon ta rayu da gwarzon miji irin Aliyu.

 

Saboda tasha wassafa ma kanta ba k’aramar jarumta zaiyi ba awajen raya sunnah, shiyasa ma ta nace da sonshi, nan take wani kuka yazo mata ta dafe bakinta.

 

Su Abba suka tafi akabar Asma’u da Hafsa, Sadauki da Aliyu da Auwal, sannan Sadiya.

 

Aliyu ya fakaici idanun jama’a yasa k’afarshi ya take Sadiya da takalmin shi, har sai da tayi k’ara, da sauri yace:

 

“Lafiya?”

 

Tayi saurin girgiza Kai tace”

“Ba komi”

 

Sannan suka rankaya suka koma, Aliyu ya yi masu jagora suka shiga har sadiya suka dubo hajiya da take ta bacci sharkaf abinta.

 

Sannan Suka ajiye mata kulolin abincin suka fito waje, Asma’u ta Kalli Hafsa tace:

 

“Mai ciki, yaushe zaki haufo muna babyn mu?”

 

Hafsa ta harareta tace:

 

“Renin wayo, ai kema kinsan sai kin rigani haihuwa”

 

Asma’u tace:

 

“To Ubangiji Allah ya sauke mu lafiya”

 

Hafsa tace:

 

“Ameen, itama basma ance ciki ne da ita kowa? ”

 

Asma’u tayi dariya tace:

 

“wato ance Mane baki tabbatar ba?, cab alamu sun nuna baki da zumunci Hafsa, saboda inajin baki tab’a ma zuwa gidanta ba fa”

 

Hafsa tana dariya tace:

 

“Sa’idinawa ai zanje ne ko?”

 

Daganan suka ci gaba da firar su, har Sadauki yayi sallama dasu Auwal suka tafi,Auwal ma basu jima ba suka bar asibitin.

 

****

 

Bayan sati d’aya hajiya taji sark’i sosai har ta fara tafiya, akullum sai su Abba yaje dubota, kunya kamar ta nurse akasa, idan ta tuno irin abunda tayi masu abaya, duk yaje sai ta rok’eshi akan ya yafe mata abunda tayi mashi, don ko Alhaji Hamza da yake mujinta bai zuwa ganinta kullum irin yanda Abba yake zuwa, yau ma dayaje tana ta kuka tana rok’onshi akan akawo mata Salma ta rok’i gafararta, Abba yace ba komi ta yafe mata, ta daina tada zancen.

 

***

Izuwa lokacin Aliyu yasa angano masa azanto ya mik’awa hukumar ‘yan sanda shi ahannu, yace suyita azabtar dashi har sai ranar da ya nemesu, aiko suka dinga horashi horo mai tsanani.

 

Itako Kulsum, shirun da taji na Sadiya yayi yawa yasa taje gidan don taji ko lafiya akayi rashin dace Aliyu yana nan, tayi ta rafka sallama taji shiru, aiko sai gata har d’akin Sadiya ta tura tajishi abud’e ta fad’a.

 

Sadiya dake rufe a store tana jin muryarta, ta fara kiran sunanta amma ina ba maiji saboda uk’ubar da Aliyu yake gana mata yasa, saboda kuka muryar ta ta shak’e.

 

Aliyu kam yana jin muryarta ya gano itace, ya fito koda yazo sai yaga takalminta ak’ofar d’akin Sadiya, da sauri ya koma ya d’auko belt d’inshi mai shegen k’wari, ya shiga d’akin sadiyar ya Kalle da makulli, Kulsum ta waigo tana shirin yin magana taji saukar duka ta ko’ina aika mata yakeyi, tun tana dauriya har ta dinga kwarara ihun neman ceto.

 

Sadiya dake store sai jin k’arar kulsum takeyi, aikuwa sabon tashin hankalinta ya k’aru, sai buge buge takeyi tana ta gwara kanta ak’ofa.

 

Saida Aliyu yayiwa Hajiya kulsum tib’is, sannan ne yajiyo bugun k’ofar da sadiya takeyi da kanta, da sauri ya fita ya rufe k’ofar don kar kulsum ta tsere, ya bud’e Sadiya ya jawota k’iiii ya kaita d’akinta inda kulsum ya jefar, Sadiya da gudu ta fad’a jikin Kulsum tana kiran sunanta, ganin irin dukan da Aliyu yayi mata, amma ina hajiya kulsum kam ta jibgu iya jibga, baki da hancinta sun fashe sai zubar da jini sukeyi, ahakan ya kira ‘yan sanda, da suka zo yace suje da ita su tsare masa ita, sannan suyita gana mata azaba har sai ya nemesu, aikuwa sadiya ta haukace tana tana ta kuwwa, wai baza’aje da kulsum ba, amma ina wata ‘yar sanda ta ciyo k’ugun kulsum, tana tafe tana layi suka jefata motarsu suka tafi.

 

Sadiya tana tsugunne tana kuka na fitar hankali, Aliyu ya k’ara jawota k’iii ya kaita ma’ajiyarta store ya rufe sannan ya fad’a a kujera yace:

 

“Kema shegiya da nagama aikin da zanyi dake zan had’aki da ita in maka ku kotu, da hujjata mai k’arfi da take hannuna, Don ubanku duk sai kun d’and’ani zama gidan yari wallahi”

 

 

Aifa😹😹😹😹

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 18

Advertisement €pisode 18…………….. Bayan wata ɗaya . Tun daga Ranar da Naheela ta karɓi mulkin Garin Zawatu wani…
INAYAH
Read More

INAYAH 31

Advertisement _31_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Sake Shan jinin jikinsu dukkaninsu sukayi Jin cm yace sufito atafi gida Nan suka sake…
INAYAH
Read More

INAYAH 6

Advertisement Mamuhgee 6_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Yagana aiki takeyi a qaramar private school din dake kusa da anguwar tasu amatsayin nanny…
KALLABI
Read More

KALLABI 26

Advertisement BABI NA ASHIRIN DA SHIDA Muryan shi na rawa ya rike hannun ta. “Zai fi kyau ki…