INAYAH 48

INAYAH
INAYAH

Advertisement

[11/7, 11:34 AM] +234 805 800 0496: *_48_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Washe gari da wuri ta fita aiki ko Abbi dataje gaidasa bai fitoba wucewa tayi bayan ta kirasa awaya kashe da alama Bai tashiba.

Ko yau ta hadu da umma Hadiza asibiti sbd umman hankalinta Bai kwanta da barin Abdul da Inayah dinba batareda ta rakosa tana sake tunatar dashi illar da shedan ke masaba na maqalar Masa da tunanin Inayah.

Duk da ya tabbatarwa umma Hadizan zai nesanta kansa da duk wani tunanin daban Amma takasa yarda dari bisa dari dashi,

Tasan bazai aikata abinda yafita musulunciba Amma Kuma batason ya shigewa Inayah din sosai sbd ko kadan bazata so a shiga haqqin AA MAJEED ba bayan datasan girmansa da sadaukarwarsa akan Inayah,

Ayanzu ko ita data Haifa Inayah din tayi alqawarin dakatar da kanta daga zuwa gunta matuqar ba MAJEED din ya Basu Daman hakanba.

Yauma kaman baqi haka suka gaisa da juna saidai har umma Hadizan ta fice Inayah na zaune cikin mota tana kallonta.

Fitowa tayi ta nufi ciki tana saka wayarta silent tareda sakawa cikin jaka.

Kaman yanda suka Saba kusan tareda Dr Abdul tayi aikin wunin ranar na duba patients Dan haka tafara Jin sakewa dashi kaman yanda suke can farko.

Sai yamma sosai yau tadawo Dan haka Bata tsaya koinaba sai bedroom dinta tafada wanka.

Tana fitowa sallar magriba tayi tareda saka kayan bacci tayi kwanciyarta a  daki tana Jin ciwon Kai na Dan damunta na gajiya.

Advertisements

Ta Bangare Daya jinta takeyi wani sukuku sbd gabaki daya wunin batai magana da Abbinta ba abinda baitaba Kuma baya faruwa a rayuwarta,

Abbinta shine abokin firarta akoda yaushe kusan da safe da Rana kusanma dai time to time suke waya idan har baya gari
Idan Yana gari kuwa tunda safe saitaga Abbinta take fita hakama kafin tadawo Zata kirasa da darema tare sukecin abinci a dining Kuma tabisa palonsa kafin taje ta kwanta Amma yanzu komai Yana neman canjawa duk sbd auren Nan dakuma zuwan Haj umma.

Da zaaci abincin dare Bayan kowa ya zauna zasu fara baiga tafito Kuma yau duk baijitaba shima.

A natse ya dago ya ‘dan kalli umma yaganah yace”

Inayah Bata dawo daga asibiti bane?

Tadawo,
Batajin dadine kanta na ciwo tun dazu.

Baice komaiba ya ajiye tissue din hannunsa tareda miqewa tsaye zai wuce Haj umma ta riqe hannunsa ahankali cikin kulawa tace”

Ka zauna,
Ina zaka bakaci abincinba?
Bari a kuma kiranta.

Dan shiru yayi tareda Dan juyowa gefen zubbi dake kokarin ajiye juice data kawo yace”

Ki kirata ta fito taci abinci.
Idan jikin yana damunta sosai Dr farhat zatazo yanzu ta dubata.

Yes Sir” zubbi tace tareda juyawa ta nufi dakin Inayah din.

Tana zuwa ta taddata kwance idanuwanta a rufe saidai ba bacci takeyiba waya takeyi da Neesah ahankali sbd batako son doguwar magana yau.

Advertisements

Magana sukeyi da Neesah akan damuwarta na abinda yake sauyawa daga rayuwanta da Abbi.

Cikin kulawa zubbi tace”

Abbinki yace a kiraki kifito kuci abinci.

Ajiyar zuciya Inayah sauke ahankali zatai magana Neesha tace”

Babes kice bakida lafiya sosai bazaki iya fitaba kodan abbin yanuna Miki kulawansa dakika rasa kwana biyun.

Shiru Inayah tayi tana nazarin maganar,
Bata yiwa Abbinta Karya sbd Bai koyar da itaba Amma Kuma tanason kulawansa datake neman rasa sbd zuwan Haj umma Dan haka ta amsa shawarar Kai tsaye tace”

Babes saimunyi mgn.
Kashe wayar tayi tareda ajiyewa gefe ta kalli zubbi a kasalance tace”

Zubbi bazan iya fitowaba kaina na ciwo sosai na koshi da abincin.

Juyawa zubbi tayi abinta ta isarda sakon ta juya ta koma kitchen.

Shiru kowa yayi
Haj umma na jiran ganin idan tashi zaiyi.

Umma yaganah ma jiran take taga abinda zaiyi.

Ajiye spoon din hannunsa yayi yanason miqewa Amma Kuma Haj umma da kanta tayi serving dinsa cikin tsananin kulawa da kauna da maimaicin yaci abincin.

Katse shirun Haj umma tayi da cewa”

Yaganah Akira likitan dazata dubata Mana tun kafin dare yayi Amma nafisa ran stress ne na aiki kawai may be idan tayi bacci zuwa safe Zata wartsake.
Dan yakamata ta saba da duka irin wannan stress din tunda likitace,

Kun sangartata shiyasa komai qanqantan Abu take maidasa Babba,

Saiga kuna rufe Ido kuna koyar da ita wani bangare na rayuwar
Ba’a sangarta da shiririta rayuwar Zata qareba
Aure zatayi Batasan kalan rayuwar dazata tadda b……

Tissue din daya goge Baki ya ajiye tareda miqewa Yana musu Saida safe gabaki daya.

Umma yaganah ma kasa shiru tayi cikin ‘yar Wasa tace”

Aure Kam ai tariga tayi saidai ta muyita fama ta nutsu tasake sanin abinda takeyi,
Inayah kam dama ai akwai shiririta taqi girma indai tana gaban MAJEED.

Aikuwa Dole tasan ta girma tunda majeed din ba zauna zaiyiba zaman jiran tayi hankali,

Aure yakamata yasan yayi Dan shekarunsa yanzu yakamata ace yafara Tara Yara Amma gashinan aurenma baisan yayiba Dan shirmen Inayah,
Idanma batai hankaliba ai shikam bazai zauna jiran ranarda Zata hankaltuba aure zaiyi manyanta yakeyi ba saurayi yake sake zamaba.

Tsit umma yaganah tayi tana sauraron abinda Haj umman ke fada cikeda mamaki da shakka,

Me kuma yakawo maganar MAJEED da wani auren yanzu ana zaune kalau,

Auren dake kansa yanzuma baigama samun mazauniba a rayuwarsa ake maganar wani auren yanzu?
Kenan Haj umma Bata dauki auren Inayah din da majeed aureba sai hanyar dakatar da Hadiza kawai.

Jin tayi jikinta yayi sanyi bakuma gurin sauran gurin shigan abinci acikinta sbd maganar Haj umma Dan haka ta Dan saki yaqen murmushi tana yiwa Haj umma din Saida safe ta tashi.

Itama Haj umma tagama Dan haka ta miqe ta nufi dakinta Kai tsaye tana sanarda Salimat ta hado ruwan zafin gasa Mata qafafunta.

Inayah dake daki tana jiran zuwan Abbinta dubata taji shiru Babu Wanda yazo tsawon mintuna.

Sanyi jikinta da zuciyarta ke kokarin Yi matuqar Abbinta baizo dubataba to tabbas yanzu ba kaman dah bane kenan,

A sanyaye ta zame ta qarasa kwanciya tana Jan bargo ta rufa.

Shigowar umma yaganah ce ta sanyata dagowa a sanyaye ta kalleta.

Itama umman jikinta a mace yake Amma Bata Bari Inayah din taganeba ta qaraso tareda Zama gefenta tana cewa”

Yaya kan?
Ya rage ciwo?

Dago kanta tayi daga kan pillow ta kwantar kan cinyar umma yaganah tana lumshe idanuwanta.

Ahankali tace”

Umma yaganah Ina Abbi?
Yana gurin Haj umma ne?

Numfashi umma yaganah ta sauke tareda dafa kan Inayahn cikin nutsuwa da kulawa tace”

Inayah kina buqatan cire duka wani tunanin MAJEED kada ya kusantu da kowa bayan ke,
Haj umma mahaifiyarsa ce wadda duk duniya Babu Wanda yakaita matsayi agunsa,

Duk yanda yake tsananin kaunarki idan kina nuna Jin zafi ko kishin kusancinsa da Haj umma Zaki iya jawa kanki matsala,

Ki cire tunanin komai ki maida hankali kan aurensa dake kanki Dan yanzu duk wani shashanci ki ajiyesa ki fara sanin aurene akanki.

Kuma ki koyi hadiye Abu Dan Allah Inayah sbd banson afara samun damuwa tunda wuri tsakaninki da mahaifiyarsa tunda dai ba zaunawa zatai har abada ananba dole wataran Zata tafi,
Nima zuwa gaba kuna fara taramun ‘yan jikoki Zan barku ayita kaimun renonsu..koba haka ba?

Ko har shirin auren da kukai keda Neesah ya wargaje sbd Abbi ne mijin ba’a aura masu rawar Kai ba..

Da ‘yar tsokana ta qarasa zancen tana shafa kan Inayah sbd ta sake Dan tasan Zata iya kwana da damuwa aranta.

Murmushi kawai Inayah tayi tana safe lafewa tace”

Umma yaganah ai Abbi ma kila ya manta da cewa nifa yanzu matarsace..

Nidai umma yaganah kiyi Masa tuni nifa yanzu ba ‘yarsaceba kawai Ni matarsace Dan Allah ya……

Buge bakin umma yaganah tayi tana cewa”

Zaki fara ko?
Ba nace ki ringa Kama bakinkiba idan bakisan me Zaki fadaba.

Umma yaganah fa kinaga ko Dan kallon mace bayamun saina ‘yar baby Inayah wadda ta…….

Bazakiyi shirunba kenan?

Shiru tayi tana hadiye sauran zancen Dan ita idan matsayin Mata zaisa kulawan Abbinta yadawo Mata Zata zabi hakan da sauri.

Zubbi ce tayi knocking kofar dakin tashigo tareda Dr farhat wadda taketa zuba qamshi Mai Dadi da adonta na doguwar Kuwait Abaya red fes da ita kaman ba dareneba.

Abbi ne yakirata ta taho duba Inayah,

Qarasowa tayi fuskarta daukeda murmushi da kulawa tana gaida umma yaganah kafin ta zauna gefen Inayah tana cewa”

Oh my baby meke damunki?

Abbinki yakira hankalina ya tashi na dauka sosai ne jikin naki,

Meye matsalar?

Tashi zaune Inayah tayi daga kwancen ta zauna tana cewa”

Ciwon Kai ne kawai due to stress na aiki I think,
So Inaga dana samu nayi isashen bacci I will be ok by morning.

Duk da hakan Bari nai checking pulse naki,
Duka wannnan Zaki Saba ahankali ok?
Ki ringa samun bacci da hutu sosai.

Tea da cake Mai laushi akasa zubbi ta kawo Mata Tasha suna Dan fira sama sama kafin sukai sallama Dr farhat ta fito.

Umma yaganah ce takaita har dakin Haj umma ta gaidata.

Da mamaki sosai Dr farhat ke sake gaida Haj umma dakyau tana mamakin ba umma yaganah ceba Ashe ta Haifa AA MAJEED.

Haj umma itama sosai ta saki fuska suka gaisa da Dr farhat din Dan yanda Dr farhat ta ringa gaidata cikin Jin kunya da girmamawa sosai yasa taga mutuncin Dr farhat din sosai.

Bayan tafiyar Dr umma yaganah itama wucewa tayi dakinta ta kwanta.

Har Inayah tayi bacci cikin sanyi tana Jin damuwar rashin ganin Abbi.

Da safe haka taqi fita aiki da wuri Saida tayi breakfast da kowa.

A dining tana zuwa da Abbi tafara hada Ido Yana zaune cikin Navy blue Ralph Lauren suit dasukai masifar yimasa kyau tareda fidda hasken lafiyayyar fatarsa dake cikin hutu.

Gabaki daya Qamshinsa ya hadu Dana English breakfast din dake jere a dining ya sauya gurin.

Cikin nutsuwa da kulawa da sanyin murya tace”

Good morning Abbi.

Idanuwanta ya kalla kafin ya dauke idonsa akai anatse Yana cewa”

Morning,
Yaya jikinki?

Complain zatayi umma yaganah ta katseta da cewa”

Yaya jikin Inayah?

Naji sauki umma,
Haj umma Ina kwana?
Umma yaganah good morning.

Zaunawa tayi tana kokarin fara cin abinci Haj umma tace”

Yaya kan?
Yayi sauki ko?

Eh naji sauki alhmdllh.

Fara cin toasted bread tayi tana daukan tea tafarasha.

Itace tafara gamawa ta miqe ta Zata fice Abbinta yace tajira zai ajeta asibitin.
##MAMUH#

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 37

Advertisement BABI NA TALATIN DA BAKWAI Kallon juna suka yi da Innayoh, kowacce fuskar ta dauke da murmushi.…
Read More

TARTSATSI 68

Advertisement *Page 68*   **********************   Sadauki kam saida ya tabbatar ya karkare, duk wata tsatsa da ta…
Read More

TARTSATSI 93

Advertisement Page 83*   **********************   Aliyu durk’ushe agaban Daddy sai kuka yakeyi, acikin tashin hankali, saida Daddy…
Read More

TARTSATSI 97

Advertisement *Page 97* ********************** A siyasance Abba ya dinga yiwa hajiya nasiha, tareda lurar da ita akan hak’uri…