INAYAH 49

INAYAH
INAYAH

Advertisement

Daga ita data fada har su duka dake gurin tsit sukai cikin jujjuya zancen.

Batareda ya kalletaba cikin nutsuwa ya amsa a taqaice da cewa”

Muntashi lfy¿

A natse Inayah ta gaidata tareda kallon Abbin tace”

Abbi to waye zaizo daukana idan natashi tunda banzo da motaba?

Tada motarsa yayi ya dago ya kalleta cikin kulawarsa da kaunarsa yace”

Dr Abdul nasan zai Zama busy
May be mamansa idan Bata komai Zata iya maidaki gida,

Amma karki biya koina daga asibiti gida direct Zaki koma.

Jan motar yayi yabarsu tsaye Inayah nabin motarsa da kallo
Umma Hadiza kuwa wanin zallar farin ciki da mamakin MAJEED ne yacikata kenan majeed din ya yarda takai Inayah gida sbd kawai ta zanta da ‘yarta….

Tasan bazai iya yafe Mata ko kulata lokaci dayaba Amma ko ahakan ta gode da karamcin.

Advertisements

Inayah rasa abin cewa tayi ta kalli umma Hadiza da farin cikinta Bai boyuba tace”

Zan dauki drop kokuma na Kira Charles idan natashi sbd Zaki wahala zuwa daukana Kuma ki kaini har gida.

No Ayshatouh please kibari nazo na daukeki da kaina
Muna buqatan sanin juna
Damace Abbinki yabani please.

Dan murmushin yaqe tayi tana cewa”

Ok Zan tashi 2 yau Inshallah.

Zanzo kafin 2 Inshallah.

Juyawa tayi ta wuce dama Dr Abdul Bai tsayaba ya wucewarsa.

Bayansu umma Hadizan tabi da kallo tana jin farin ciki Mai tsanani ganin yayanta dukasu biyun likitoci ne.

Duk da Inayah Bata Gama Zama qwararriyaba Amma zuwa gaba itama tasan Zata Zama abin alfahari gurin marasa lfy dasu iyayenta.

Data tuna mahaifiyarta zatazo daukanta saitaji wani iri Amma Kuma ita kanta tanason sanin umman Abdul din.

Qarfe daya da arbain kuwa saiga Hadiza ta iso asibitin Dan haka Inayah ta tattara ta fito suka wuce gida.

A hanya umma Hadizan keta Jan Inayah din da fira da tambayoyi akan rayuwarta Wanda komai ta tambaya sunan abbine amsar,

Advertisements

Anan tasake saddaqarwa MAJEED sbd yariga yayi ginuwar da Babu abinda zai girgizasa Aran Inayah,

Shine ciki da Bai din rayuwarta Dan kuwa da ace wani mijin ta aura bashiba zaiyi wuya mijinta baiyi kishinsaba duk da Yana matsayin ubanta sbd kaunar tayi karfi.

Kaman daga sama ta jeho Mata tambayar

“Ya maganar aurenki da Abbin naki?…

Shiru Inayah tayi cikin rausayar dakai tace”

Bansaniba,
Amma dai Ni aguna tanan bazan taba rabuwa da Abbi ba ko bayason auren nidai inaso yanzu….

Kallon mamaki Hadiza tayiwa Inayar tana tauna zancen,

Lallai majeed yagama shagwaba Inayah ta yanda Babu ruwanta duk maganar datazo Mata fada takeyi.

Tayaya zakiso auren idan shi baisoba ai Babu au……

Karki min Baki a auren please,
Ni inaso Kuma tunda inaso Abbi ma zaiso.

Murmushi Hadiza tayi aranta tana cewa”

Hmm wanna abbin naki Mai taurin Rai bazai taba kallonki mace ba bare matarda zai iya kwanciyar aure da ita.

Suna Isa gida a gate ta ajiyeta batareda tashiga gidanba ta juya ta komawarta.

Inayah na shigowa gida a Palo ta tadda Dr farhat tazo sunata fira da Haj umma
Umma yaganah Kuma tana kitchen yau da ita ake aikin abincin sbd kwana biyu bataiwa MAJEED abinci da kantaba.

Da mamaki Inayah ke kallon yanda har suka Saba a wuni daya daga zuwan Dr farhat din.

Gaisawa sukai tana tambayar Dr farhat dalilin zuwanta tace Haj umma tasake zuwa gaidawa da Rana sbd jiya darene Basu gaisa da kyauba.

Dakinta ta wuce tayi tube tayi wanka da sallah ta fito sanyeda doguwar chiffon gown Mara nauyi kanta daure da silk scarf.

Tunda ta fito itama kitchen ta nufa gurin umma yaganah acan Tasha cornflakes sbd bata iya cin birabisco ba shi sukai da Rana.

Da ita aka qarasa aikin tasaka hannu duk da bawani aikin ta iyaba bayan wanke plates da cups sai dafa tea shima Dan Abbinta Nasha sosai yasa ta iya Dole.

Daki Takoma ta sauya kayanta sbd batason kamshin girkin dasukeyi.

Har dare Dr farhat na gidan da ita sukai dinner tareda Abbi dashima ya danyi mamakin sabonta da ummansa daga zuwa.

Gurin cin abincinma haka dai umma yaganah da Inayah suka Zama Yan kallo har aka gama kowa ya tashi.

Da Dr farhat Zata tafi har mota ta rakata ta wuce sai yabon Haj umma takeyi itadai Inayah batace Mata komaiba akan aurenta da Kuma Dr farhat din Bata saniba hakama Haj umma Bata Sanar mataba.

Kasa bacci tayi Saida ta fadawa Neesah zuwan Dr farhat sukaita maganar kafin ta kwanta.

Washe gari Abbi Bai tashi da wuriba Dan haka ta wuce
Kuma acan ta tadda umma Hadiza Saida suka gaisa kafin ta wuce.

Yauma tana dawowa Dr farhat na gidan yau Kuma wai BP din Haj umma dinne yahau tazo dubowa.

Haka takuma wuni dasu sai dare ta wuce.

Ahankali ahankali Dr farhat ta maida gidan nasu gurin zuwa fiyeda yanda take zuwa adah,

Tayi sabo da Haj umma sosai ba laifi Dan kuwa Haj umma najin dadin yanda take zuwa duba BP dinta akai akai Wanda Kuma a Yan kwanakin tagano irin son da Dr farhat kewa MAJEED sbd hatta kulawar datakewa Inayah Mai girmace duk sbd MAJEED
Shikuma baimasan tanayiba.

Ta bangare Daya Inayah kwata kwata yanzu Bata wani gane kan Abbinta sbd dukkanin kulawansa Takoma kan Haj umma sbd kwana biyun batajin dadin BP dinta sai hawa yake Yana sauka.

Tun suna mamaki itada umma yaganah harsun koma Yan kallo Danma umma yaganah tana kokari sosai gurin dannarta da hanata magana,.

Duk tabi Takoma sukuku batada walwala koyaushe a sanyaye take Dan yanzu koyaushe idan dai Abbi na gida to Yana tareda Haj umma wadda yanzune tasan tana tareda kaunar danta tunda ya maida hankali sosai akanta.

Ganin hakan yasa Inayah ke dadewa gurin aiki sosai sbd gidan ba Dadi tunda Abbinta baida lokaci sosai.

Hadiza kuwa ganin tana samun ganin Inayah a asibiti yasa kusan duk bayan kwana daya saitaje gurin Inayah asibitin su jima suna magana
Da hakan tafara sabuwa da ‘yarta tunda dama Inayah bamai hayaniya ko riqe Abu bace
Ba jimawa tayi sabo da mutum sbd sanyin halinta.

Ahankali umma Hadiza ta fahimci abinda ke damun inayah na kishin Abbinta da kowa karya fita kusanci dashi
Hakama Sam wannan auren nasu tasan idan akabi ta MAJEED kila ahaka zasu qare amatsayin uba da ‘ya.

Cikin dubara ta bawa Inayah shawaran ta fadawa antynta Hafsat abinda yake faruwa.

Dayake anty Hafsat tayi tafiya jiya tadawo aikuwa da farin ciki ta karbi shawarar.

Tana dawowa gida wanka kawai tayi tayi sallar la’asar tayi zamanta adaki zubbi takawo Mata noodles data saka ta dafa Mata da sausage.

Wayarta ta fidda ta Nemo numbern anty Hafsat ta saka Mata Kira.
##MAMUH#

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 46

Advertisement page 46* ******************* Hafsa hankalinta ya dawo ajikinta, koda ta waiga bataga Salma da khadija ba, nan…
KALLABI
Read More

KALLABI 44

Advertisement BABI NA ARBA’IN DA HUƊU Cikin wani irin yanayi ya ke kallon ta, a hankali take kallon…
Read More

TARTSATSI 27

Advertisement Paga 27* ****************** Daga hafsa har salma ba Wanda yace da wani kanzil, har suka shiga cikin…