INAYAH 50

INAYAH
INAYAH

Advertisement

50_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ringing biyu wayar tayi anty Hafsat ta dauka tana cewa”

Dr Inayah majeed Yar gatan Abbinta Kuma amaryar Abbinta..”” ta qarasa zancen da Yar dariya.

Sanyi jikin Inayah yayi tana Jin dadin kirarin Amma Kuma duk wannan yanason kauduwa.

A sanyaye tace”

Anty Hafsat Yaya gida?
Ina my sweet Siyama?

Lfy kalau Inayah,
Ya kike?
Yasu umma yaganah da hajiya?
Ya abbin naki Kuma?

Bata tsaya amsa gaisuwar yasu umma ba tace”

Anty Hafsat Abbina ya canja sosai zuwan Haj umma
Kuma umma yaganah ta Hana nayi magana
Ni gaba daya Abbina yafara Zama kaman na nawaba.

Umman Dr Abdul tace na sauya bangaren Mata
Ni banganeba Anty Hafsat kizo gidan kigan yanda muke yanzu duk ba Dadi,

Ga Haj umma komai nayi saitace shiriritata da shirme kawai na iya.

Advertisements

Yanzu itace Mai kulawa da Abbi fa,
Umma yaganah ma yanzu Takoma Yar kallo abinci kawai take Masa.

Nidai anty Hafsat wlh bazan iyaba
Ina kallo Abbina ya Dena ji Dani kaman da
Bayan umman Abdul tace kamata yayi matsayina ya ninku tunda matsayina biyu agurinsa.

Numfashi anty Hafsat ta sauke tana jinjina zantukan Dan duk da kusan a shagwabe da damuwa Inayah ke fadan zancen idan ta fahimta Haj umma batai na’am ba haryanzu da Inayah a rayuwar AA MAJEED barema ta dauki auren da mahimmanci.

Wani numfashi takuma sakewa tana ajiye ruwan data kawowa CM ta juya ta fice daga palonsu zuwa dakinta Dan bazataso yaji zancen nasuba.

Tana Shiga daki ta zauna bakin gado tana cewa”

To kodai kina Mata abinda baimata bane Inayah?

A sanyaye tace”

Wlh anty Hafsat bana Mata komai
Kuma Ni bandamu data kaunaceniba
Nidai Abbina nakeson ya koma yanda yake kada ya rage ji dani.

Inayah duk wannan abin na tabbata Koda qwayar zarra kaunarki da matsayinki a zuciyar Abbinki Bata raguba
Bama Zata taba raguwaba qaruwa zatayi sbd har Koda yaushe kece kaman strength dinsa.

Kawai dai inaga aurenku ne Bata aminta dashiba sbd ganin kaman bazaki iya kalawa da AA MAJEED dinba kinyi qanqanta….

Aikuwa wlh Ni inason auren yanzu bazaa rabani da Abbi ba,
Ko shima Ni Zan fada Masa inason aurena bazan rabu dashiba.

Da mamaki anty Hafsat tace”

Advertisements

Yanzu Kuma kinason auren kenan?
To kinason auren yanzu harzaki tsaya kina kallo auren na Neman fara rawan tun baigama tsayuwa ba,

Wannan rashin amintar da Haj umma tayi kome zai iya faruwa
Dan kuwa ko auren be rabuba MAJEED Kam zai iya samun matar dazata kular Mata dashi….

Wani mummunan faduwa gaban Inayah yayi ta tashi zaune ahankali dakyau tana cewa”

Sai tasashi yayi wani auren anty Hafsat?
Shima abbin sai yayi wani auren?

Wani mugun sanyi taji Yana shiga qafafunta tayi shiru tana jiran amsar anty Hafsat wadda taji rashin kamatan yin zancen da Inayah Dan haka ta Dan gyara murya cikin nutsuwa da kulawa da rarrashi tace”

Idan kika tsaya shirme nake fada Miki hakan kila zai iya faruwa,
Dan haka yanzu ki nutsu kema ki ringa kulawa da Abbin kaman matarsa sbd wannan right dinki ne dake Zaki bawa kanki.

Kasa cewa komai tayi sbd jikinta daya Gama mutuwa da wani irin tsoro dan kuwa tana fama da zuciyarta akan Haj umma idan Abbi ya auro wata Batasan ya Zata iya dauka.

Ganin ta Dena gane abinda take fada yasa Anty Hafsat yimata sallama da cewan Zata shigo gobe Inshallah.

Aje wayar tayi hannuwanta na Dan rawar data kasa gane Kota menene.

Kasa qarasa cin abincinta tayi ta miqe tareda daukan tray din ta fita zuwa kitchen.

Tana ajiye kayan data kawo kitchen kasa juyawa tayi ta tsaya agurin tana shiga tunani
Ita gabaki daya kanta ma ya toshe takasa gane komai,

Ita Abbinta kawai takeso ita kadai.

Juyawa tayi ta fito tana kokarin Isa hanyar bedroom dinta taji Qamshin Boadicea ta dakata sbd tasan Abbinta ne yadawo.

Juyowa tayi tadawo palon daidai Yana shigowa sanyeda kaftan
Navy blue best kalar dayafi amfani da ita.

Ganinsa yasa idanuwanta cikowa da hawaye tanajin wani irin nauyi a zuciyarta da abinda anty Hafsat ta fada dazu.

Kallonta ya qaraso yanayi zuciyarsa na tabuwa da kallonda take Masa idanuwanta da Hawaye Wanda yasan na kewansa ne.

Ahankali ya bude Baki zaiyi magana ta fada jikinsa ta qanqamesa tana sako hawayenta.

Shiru yayi Yana kokarin daidaita kansa sbd ba zatan datai Masa.

Qamshin Turarenta na black opium ya shiga hancinsa da kyau
Take yaji kansa ya Sara ya bude idanuwansa akanta tareda daga hannuwansa zai zareta daga jikinsa Amma ta ture hannunsa tana sake shigewa jikinsa hawayenta na sake gudu zuciyarta na bugawa da zancen anty Hafsat har lokacin.

Maqoshinsa yaji Yana Neman bushewa sbd yanayin yayi Masa nauyi Musamman Haj umma ko umma yaganah wani zai iya samunsu ahakan.

Numfashi ya sauke ahankali tareda Dan nutsuwa cikin kulawa yace”

Me kikeyi Inayah?
Lafiya?
Akwai abinda ke damunkine?
Taso naji matsalar…

Girgiza Kai tayi tana qin sakinsa tace”

Abbi Dan Allah karka rabu Dani Ni inason auren….

Wani irin duka zancenta yayiwa zuciyarsa har baisan lokacinda ya rintse Ido ahankali ba tareda budewa zuciyarsa na Neman yin sanyi sbd a bazata yaji zancen.

Ahankali ya daga hannuwansa Yakai kan hannuwanta Yana kokarin janyeta kenan saiga Haj umma da umma yaganah kusan atare sun shigo palon kaman aike….

Da sauri Haj umma ta dakata tana kallon ikon Allah lokaci daya tana dauke idonta Kuma.

Umma yaganah kuwa juyawa tayi abinta batareda ta tsayaba tana jinjina sangantar Inayah sbd tasan itace me wannan aikin ba Abbin ba.

Ganin Haj umma yasa duk yaji yana sake shiga wani yanayi na sanyin jiki ya janye Inayah din zaiyi magana ta sake komawa ta maqalesa tana cewa”

Abbi Dan Allah kabarni da aurena zanyi biyayya akan da….

Salati haj umma ta sake tana maido da kallonta kan Inayah dataqi Kota kan idonta tabi.

Ba Shiri Haj umma ta kamo hannunta tana janyota gefenta tace”

Yaushe zakiyi nutsuwa nikam ‘yar nan?
Yanzu uban naki kike damuqa haka gaban mutane kina maganar aure.

Tashi cikin turawa haukane akace Miki?

Maza wuce daki kisan abinda kikeyi
Mace da kunya da kamun Kai aka santa.

Haj umma idan na Kama kaina to Abbi zai iya auren wata yabarni da wannan auren..

Daga Haj umma har abbin kasa magana sukai sbd zancenta ya mugun Basu mamaki
Ya dago ya zuba Mata indanuwansa dasuka sake kashe Mata jiki tanajin kaman zuciyarta Zata fashe akan kishin hada sunansa da wata takuma rabarsa.

Haj umma kuwa sake sallamawa Inayah tayi sai takasa cewa komai ta qwalawa umma yagana Kira.

Umma yaganah najin Kiran tasan zaa Rina Indai akan MAJEED ne Inayah Bataji hakama Haj umma da alama itama tanada aiki tunda tana cikin uwaye masu kishin yayansu.

Umma yaganah na fitowa Abbin na wucewa batareda ya tsayaba Dan baisan mezai iya tsayawa saurara ba kuma.

Yaganah meyasa Inayah bakinta baya tauna zance ne?
Kunga illar rashin kwabarta
Gashinan sai zantuka takeyi marasa kan gado.

Cikin nutsuwa da umma yaganah tace”

Ya aka iya sai hakuri da addua Haj
Inayah din ce akwai kuruciya sosai atareda ita.

Fada Haj umma tafara Yi umma yaganah na Bata hakuri aka dai kashe maganar taja Inayah zuwa daki.

Bataiwa Inayah fadaba sbd itama zuwa yanzu tafara ganin rashin kyautawar Haj umma saidai Kuma bazata nuna hakan gaban Inayah ba sbd kada taci da ganin rashin kyautawar Haj umma din.

Batace komaiba Dan batada abin cewar Dan haka ta juya ta fice Takoma aikin datakeyi kitchen.

AA MAJEED na Isa bedroom dinsa zaunawa yayi kan sofa ahankali tareda Dan rintse Ido Yana dafe goshinsa sbd Dan juyawar da kansa keyi.

motsawan da zaiyi Qamshin black opium ya Shiga hancinsa daga kayansa na Inayah Dan haka ya miqe ahankali ya zare ya janyo towel maroon ya daura a qugunsa ya nufi toilet Yana Dan sake dafe goshinsa.

Wanka yayo yafito ya shirya cikin Kelvin Klein sweatset yana qamshi Mai sanyi ya fito ya nufi masallaci sallar magriba.

Tunda tadawo daki haka kawai takasa samun nutsuwa da sukuni tayita hawayenta tagama ta tashi itama tayi alwawala tayi sallar magrib tana idarwa ta dauki wayar Neesah daketa faman kiranta.

Sun jima suna waya tana Bata hakuri da qarfafa Mata gwiwa akan aurenta kafin suka kashe.

Wanka ta tashi tayi sbd batai niyar fita cin abinci ba tana fitowa ta saka Riga da wandon Balenciaga masu kauri tana kokarin hayewa kujera chatting ta tuna gargadin Abbinta na rashin fitowa cin abinci Dan haka ta miqe da wayarta a hannu tareda zira slippers ta fito tana qamshin black opium Mai sanyi.

Tana fitowa ta nufi dakin Haj umma ta Bata hakuri suka fito kusan tare zuwa dining din haj umma na sake nanata Mata ta Dena sakawa ranta banzayen tunani akan MAJEED sbd ubane agunta.

Batace komaiba har suka Isa suna Zama saiga Abbin ya shigo cikin nutsuwarsa da kwarjini sai qamshinsa yakeyi komai nasa a kame da nutsuwa.

Zama yayi Yan gaidasu umma kafin ya kalli Inayah dake kallonsa cikin sanyi da alaman ban hakuri.

Shikenan ya Isa”
kawai yace Mata ahankali cikin kulawa.

Murmushi tasake tana maida kanta ga abincin da aka dafa tuwon shinkafa da miyar ganye masu lafiya da Naman kaza da kifi.

Bata fuska ta danyi sbd Bata cikason tuwoba Dan Haka kadan ta zuba tuwon tanaci da spoon ahankali..

Shima abbin da spoon yakecin tuwon a natse.

Wayar Inayah din ce tayi ringing sunan Dr farhat ya bayyana akai ta saki siririn numfashi tareda daukan wayar a gundure tace”

Dr farhat I will call you muna cin abinci.

Kashe wayar tayi Bata jira amsartaba ta ajiye.

Jin Dr farhat ce yasa Bayan ajiye wayar haj umma Dan kallon MAJEED fuska asake tace”

Dr farhat nada kokari jiya ta hadani da mahaifiyarta mun gaisa sunada karamci sosai….

Shiru kowa yayi harshi abbin.

Jin yanda Haj umma ke yabon Dr farhat yasa Inayah kasa shiru tace”

Haj umma Ni kullum fada kikemun Amma kinata yabon Dr farhat,
Bayan nice jikarki Kuma….

Da idon umma yaganah tai Mata tsawa tana hanata qarasawa.

Murmushi Haj umman tayi tace”

Ke dince su yagana sun sangartaki da yawa kin kasa sanin kin girma,
Bakisan abinda kikesoba da Wanda bakyaso komai fada kike…

Ni yanzu Abbi kawai nakeso bayanshi banason koma….

Qwarewa abbin yayi da abincin dake bakinsa yafara tari ahankali.

Da sauri ta dauki ruwan ta taso ta kawo Masa tana cewa”

Sorry Abbi,sannu…

Matsesa tayi gurin basa ruwan
Turarenta yaringa Shiga hancinsa take ruwan suma suka fara kokarin qwaresa ya ajiye cup din Yana daidaita nutsuwarsa yace”

Thank you.

Kasa magana Haj umma tayi bakinta take ya mutu har aka Gama Babu Wanda yakuma magana acikinsu.
##MAMUH#
#HOTLOVE/ROMANCE

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 31

Advertisement BABI NA TALATIN DA DAYA *Kun yi min alkawarin Ba zaku nime kari ba🙄🤫* “Kana kara kuskuren…